MU SAN ANNABINMU (28)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa mafi daukaka Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka, da dukkan salihan bayin Allah.

Wannan shine darasi na ashirin da takwas acikin tarihin  rayuwar Manzonmu avin koyinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kuma har yanzu dai muna bayanin yakokinsa ne, zamu dora in sha Allahu daga inda muka tsaya.

YAQIN AHZAB :

Wannan yaqin shi ake kira Yaqin gwalalo kuma ya faru ne acikin watan shawwal a shekara ta biyar bayan hijirah. Kuma yana daga cikin manyan yakokin da suka fi tada hankulan jama'ar Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) amma daga karshe Allah ya basu rinjaye da nasarori. Ga yadda abun ya faru kamar haka :

Yahudawa sunyi nufin makirci da tayar da fitina ga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) don haka sai suka rika kwadaitar da mushrikan Quraishawa akan su fito su ha'da kai dasu tare da sauran Qabilun larabawan kauye domin su yaqi Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Sun zugasu kuma sun samu ha'din kansu ba tare da sanin al'ummar Musulmai ba.

Yayin da Manzon Allah (saww) ya samu labarin gabatowar wadannan rundunoni guda uku, wato rundunar Quraishawa karkashin jagorancin Abu Sufyan bn Harbin, da rundunar Banu Gatfan karkashin jagorancin mutane uku kamar haka : Uyainatu bn Hisnin daga Banu Fizarah, Da Al Harith bn Auf daga Banu Murrah, da Mus'ar bn Rukhailah daga Ashja'a. Gaba daya dai sun haura mutum dubu goma.

Wadannan rundunonin na kafirai sun ninka yawan sahabban Annabi (saww) alokacin har sau uku kuma gashi sun kawo yaqin ne har gida. Don haka sai Annabi (saww) ya nemi shawarci sahabbansa game da lamarin yaqin. Salmanul Farisiy (Allah ya yarda dashi) Mutumin Qasae Farisa ne ya musulunta. Kuma shine ya bada shawara mafi Qarfi, yace su agarinsu idan yaqi irin wannan ya samesu ga yadda sukeyi. Sukan tona rami su kewaye garinsu dashi yadda dawakan abokan gaba ba zasu iya tsallakewa ba.

Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya karbi wannan shawarar ta Sayyiduna Salmanul Farisiy, aka rarraba jama'a aka fara tono. Kowanne mutum goma aka tsaga musu inda zasu tona, wato tsawon zira'i arba'in. Shi kuwa Salmanul Farisiy ta wannan dalilin  samu Qaruwar daraja acikin sauran Sahabbai har suka rika jayayya da juna akansa. Muhajirun suka ce shi nasu ne tunda ba haifaffen madeenah bane. Su kuma Al Ansar suka ce shi nasu ne tunda a Madeenah aka zo aka sameshi. Ba'a dena jayayya akan haka ba har sai da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "AI SALMANU ACIKINMU YAKE, MU AHLUL BAITI".

Ana cikin wannan tonon ne sai su Salmanul Farisiy da Nu'uman bn Muqarrin da Huzaifah bn Yaman, da Amru bn Auf da wasu mutum shida suka tarar da wani Qaton dutse wanda ya kasa fasuwa agunsu. Dasuka je suka sanar da Manzo (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai ya taso da kansa yazo ya karbi abun tonon ya rike da hannayensa masu albarka ya doki dutsen sau uku, yana dukansa dutsen yana walkiya har ya rududduge, shi kuwa yana kabbara (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Yayin da ya fito daga ramin sai Salmanul Farisiy ya tambayeshi game da wannan hasken da suka gani. Sai yace masa a yayin bugu na farko, hasken ya haskaka hairah da katangun kisra ne (wato sarkin farisa) kuma Jibreelu yayi mun albishir cewa lallai al'ummata zasu ci garin da yaqi.

Acikin bugu na biyu kuma hasken ya haskaka jajayen katangun nan na kasar Sham da Rum ne. Kuma (Jibreelu) ya bani labarin cewa lallai al'ummata zasu cinyesu da Yaqi. A karo na uku kuma ya haskaka mun katangun birnin San'a'u ne (wato Yemen) kuma ya bani labarin cewa lallai al'ummata zasu cinyesu da Yaqi don haka kuyi bushara".

Musulmai baki daya sai sukayi bushara. Su kuwa kafirai sai suka fara guna-guni suna cewa "Kuji wani abun mamaki, yana gaya muku abinda bai faru ba, yana yi muku albishir cewa wai zaku ci Qasashe da yaqi alhali yanzu koda fito na fito da kafiran nan ba zaku iya yi ba!".

Allahu Akbar!!! Allah ya gaskata Annabinsa (saww) ya cika ma al'ummarsa wannan alqawarin. Domin kuwa Manzon Allah (saww) bai cika shekaru hamsin da barin duniya ba sai da rundunonin Musulmai suka ci dukkan garuruwan nan da yaqi har ma gaba da nan.. Allahu Akbar!!.

Kamar yadda na gaya muku tun farko,  adadin Sahabban da suka tsaya awannan yaqin su dubu uku ne (3,000) su kuma kafirai sun kai dubu goma (10,000) ko sama da haka. Kuma sun zagaye garin Madeenah amma sun kasa shigowa saboda tsoron wannan lambatun (rami) wanda ya zagaye garin. Kuma sun zauna ahaka sama da kwanaki ashirin basu samu shigowa ba, sai dai sukan harba kibiyoyi cikin gari, su ma Sahabbai su mayar musu da harbin.

Sannan a gefe guda kuma ga Qabilun yahudawan Banu Quraizah suna ba wa mushrikan goyon baya. To yayin da wannan hali ya tsawaita sai yahudawan suka ji tsoron kada Quraishawa su gaji da tsawon zaman nan su shigo garin Madeenah su kashe kowa da kowa. Don haka sai shugaban yahudawan mai suna Huyayyu bn Ahtab ya tafi wajen banu Quraizah ya nemesu da cewa su janye alkawarin dake tsakaninsu da Manzon Allah (saww).

Yayin da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya samu labarin wannan ha'incin da yahudawan ke shiryawa sai ya aika da nasiha garesu cewa suji tsoron Allah su kiyaye alkawari, amma basu yarda sun bi maganarsa ba. Wannan kuwa shi ya janyo Qaruwar tashin hankali ga Musulmai domin ana yaqarsu ta waje kenan da ta cikin gida.

Anan zamu tsaya in sha Allahu sai a karatu na gaba zakuji yadda Qarshen wannan yaqin ya kasance.

Salati da aminci wanzazzu, mayalwata, madawwama su tabbata bisa mafi soyuwar halittun farko da na karshe,  Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar Qarshe.

An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 2 ranar 22/07/2019 (19/11/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI