MU SAN ANNABINMU (29)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, Salati da amincinsa su tabbata bisa zababben zababbunsa Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya.

Har yanzu dai muna cikin bayanin abubuwan da suka faru ne a lokacin yaqin Ahzab (yaqin gwalalo) wanda mushrikan Quraishawa suka ha'da kai da sauran Qabilun larabawa da yahudawa da munafukan madeenah domin su murkushe musulunci amma Allah bai idda nufinsu ba.

Dakarun Mushrikan Makkah sunyi sansani atsakanin tudun nan mai suna Juruf da Zugabah, su kuma Qabilar Gatfan sunyi sansani kusa da dutsen Uhudu, Shi kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya fito tare da Sahabbansa guda dubu uku sun yi nasu sansani kusa da dutsen Sal'u.

Dama a baya na gaya muku cewa Yahudawan Madeena (wato Banu Quraizah) sun warware alkawarin dake tsakaninsu da Musulmai, don haka dole aka kwashe Qananan yara da Mata duk aka boyesu awani waje saboda tsoron sharrin Yahudawa.

Ana cikin wannan tashin hankali ne sai wasu mahaya dawakai daga cikin mushrikan Makkah suka tsallako wannan gwalalon abisa dawakansu. Acikinsu akwai :

- Amru bn Abdi Wuddin daga Banu Aamir bn Lu'ayy.

- Ikrimah bn Abi Jahlin (sannan bai musulunta ba).

- Hubairah bn Abi Wahbin.

- Naufal bn Abdillah.

- Dharrar bn Al Khattab Alfihriy.

Kafun su hauro sai da suka zuga sauran kafiran (kamar banu Kinanah) cewa suma su tsallako su yaqi Manzon Allah (saww) domin a gane jarumtarsu. Musamman shi Amru 'dan Abdu Wuddin wanda dama ya halarci yaqin badar abangaren kafirai kuma yasha wahala ya samu raunuka masu yawa ajikinsa a hannun Sahabbai.

Don haka ya taho wannan yaqin da niyyar daukar fansa. Kuma ya kasance shi Qato ne sosai yana da Qarfi da girman jiki da gwanintar Yaqi. Ya matsa har sai da ya tsallako, don haka sai Sayyiduna Aliyu dan Abu Talib (karramal Lahu wajhahu) ya fito ya tareshi yace masa :

"Ya Amru hakika kai kayi wa Allah alkawarin cewa babu wani mutum daga Quraishawa da zai kiranka zuwa ga wasu abubuwa guda biyu fache sai ka karbi 'daya daga ciki?!".

Sai yace "Eh hakane".

Sai Sayyiduna Aliyu yace masa "To hakika ni ina kiranka zuwa ga Allah da musulunci".

Sai kafirin yace "Bani da bukatar haka".

Sai Sayyiduna Aliyu yace "To ni ina kiranka zuwa ka sauko muyi yaqi".

Sai yace "Wallahi bani so in kasheka".

Sai Sayyiduna Aliyu yace masa "Sai dai kuma ni ina so in kasheka".

Daga jin haka sai kafirin ya fusata ya sauko daga kan dokinsa, ya soke dokin sannan ya yiwo kan Sayyiduna Aliy, suka fara gwabza yaqi atsakaninsu har tsawon wuni guda babu wanda takobinsa ya sari wani. Daga karshe dai Sayyiduna Aliyu ya tsagashi biyu ya kasheshi sannan ya Qara kashe wani kafirin ma bayan shi.

Nan take sauran kafiran suka juya da  gudu akan dawakansu suka koma wajen sansaninsu, muminai suna harbinsu da kibiyoyi. Tun daga nan sai zukatan kafiran da dama suka fara karaya.

Acikin irin kibiyoyin da kafirai ke harbowa har kibiyar wani daga cikinsu mai suna Hibban 'dan Qaisu wanda ake kira da laqabin "Ibnul Ariqah" kibiyarsa ta samu Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (radhiyallahu anhu) ta tsinka masa jijiya. Yayin da zai yi harbin ya fa'di sunansa cewa "Karbeta nine Ibnul Ariqah".

Annabi (saww) yace masa "Allah ya dulmiya fuskarka acikin wuta". Hakan ce kuwa ta faru domin bai musulunta ba har karshen rayuwarsa. Shi kuma Sa'adu bn Mu'az (ra) wannan raunin ne yayi ajalinsa. Amma kafin ya rasu yayi addu'a.

Sai a karatu na gaba zamuji wacce addu'a yayi, kuma muji sauran labarin abubuwan da suka faru awannan yaqin. In sha Allahu anan zamu tsaya.

An gabatar da karatun nan ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP ranar 25/11/1440 28/07/2019).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI