MADUBIN DUBAWA (75)

QARSHEN MAI CI DA ADDINI
*****************************
Al Imam Ibnul Jauzee ya hakaito daga Uthman bn Abdillah cewa a zamanin Annabi Musa (amincin Allah ya tabbata gareshi da Annabinmu) akwai wani mutum wanda yake hidimta masa, kuma yana neman ilimi awajensa.

Watarana sai wannan mutumin ya nemi izini awajen Annabi Musa (alaihis salam) cewa yana so zai je garinsu ya dawo. Sai Annabi Musa (alaihis salam) yayi masa izini ya tafi. Amma daga zuwansa sai ya mayar da kansa tamkar shine malamin garin.

Yana tashi yana wa'azi atsakanin mutanen garin, motsi ka'dan sai yace musu "Musa kaleemul Lahi (alaihis salam) ya bani labari cewa kaza yayi kaza". Ko kuma "Annabi Musa mai ganawa da Allah ya bani labari cewa kaza yayi kaza... ".

Su kuma mutanen garin suna jin dadi suna tara masa dukiya har dai ya tara kudi da dukiya mai yawan gaske. Kuma daga nan ya zauna agarinsu bai sake komawa wajen Annabi Musan ba.

Shi kuwa Annabi Musa (alaihis salam) ya kasance yana yawan tambayar labarin mutumin amma babu labarinsa.

To watarana Annabi Musa (alaihis salam) yana zaune sai ga wani mutum yazo wucewa yana janye da wani zomo, da igiya a wuyan zomon. Sai ya tambayeshi daga inda yake, sai mutumin yace daga gari kaza (ya ambaci sunan garin Mutumin chan mai ci da addini).

Sai Annabi Musa ya tambayeshi ko kasan wani mai suna kaza? (ya ambaci sunan almajirin nasa). Sai mutumin yace "Ai shine wannan zomon da kake gani a hannuna! ". (Wato saboda laifin ci da addini Allah ya juyar da siffarsa ta koma ta dabba Qarami irin zomo).

Sai tausayi ya kama Annabi Musa (alaihis salam) don haka ya roki Allah cewa "Ya Ubangiji ka dawo dashi zuwa siffarsa domin in tambayeshi shin wanne laifi ya aikata har kayi masa wannan uqubar!"

Sai Allah yayi masa wahayi cewa *"DA ACHE ZAKA ROKENI DUKKAN ABINDA ANNABAWA SUKA ROKENI TUN DAGA KAN ANNABI ADAM (AS) DA WADANDA KE QASANSA DAGA ANNABAWA HAR ZUWA ANNABI MUHAMMAD (SAWW) DA BAZAN KOMAR DASHI ZUWA SIFFARSA TA FARKO BA. HAKIKA NAYI MASA WANNAN NE SABODA KASANCEWARSA YANA NEMAN DUNIYA NE TA HANYAR CI DA ADDINI".*

Don Qarin bayani aduba :

- IHYA'U ULUMID DEEN NA Hujjatul Islam  Al Ghazaliy (juzu'i na 1 shafi na 66).

- QUTUL QULOOB (juzu'i na 1 shafi na 205).

- Mukhtasaru Tareekhi Damashqa (juzu'i na 7 shafi na 464).

- Uyunul Hikayat na Ibnul Jauzee shafi na 370 Hikayah ta 367.

ABIN LURA
***********
Hakika wannan babbar izina ce ga Malamai da Almajiransu da kuma masu yin karambani acikin lamarin addini. Shi musulunci addini ne na ilimi. Idan kana son kayi magana acikin addini dole kaje ka nemi ilimi, kuma ka tabbatar ka nemeshi awajen Malami masu tsoron Allah. Ba masu bin son ransu ba. Kuma ka tabbatar ka gyara zuciyarka ka nufi Allah wajen neman ilimin, ba wai don jayayya da mutane ba.

Shi ilimi siffar Allah ne. Duk wanda ya nufi neman duniya dashi, to hakika sai Allah ya kunyatashi tun daga duniyar har lahira. To yaya kuma wanda bai san abun ba, amma yake nuna tamkar shi masanin ne??.

Ya zama wajibi Malamai su nufi Allah da iliminsu ba don burge wasu jama'a ba, ba don neman tara abin duniya ba, ba don yin jayayya ko zage-zage ko cin zarafin wasu ba. Domin kuwa duk wanda bai nufi Allah da iliminsa ba, to ilimin ne zai zama linzamin jansa zuwa wuta. (Allah shi kiyayemu).

WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (01/08/2019 28/11/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI