HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (122).

SHAYAR DA MAI RAI
*********************
Hadisi daga Muhammadu 'dan Seerina, daga Sayyiduna Abu Hurairah (Allah ya yarda dashi) yace Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) yace :

"WATARANA WANI KARE YANA ZAGAYE WATA RIJIYA, QISHIRWA TA KUSAN KASHESHI SAI WATA KARUWA DAGA KARUWAN BANU ISRA'EELA TA GANSHI.

SAI TA CIRE TAKALMINTA (TA JANYO RUWA) TA SHAYAR DASHI, SAI AKA GAFARTA MATA SABODA WANNAN".

ADUBA : Sahihul Bukhariy (juzu'i na 3 shafi na 1279).

QARIN BAYANI
***************
Tausayi yana daga cikin siffofin Ubangiji. Don haka Allah yana yin rangwame da afuwa da fifiko ga duk bawansa wanda ya siffantu da wannan siffar.

Ku dubi girman laifin zina, musamman ga wacce ta maidashi sana'arta. Amma Allah ya gafarta mata saboda shayar da kare ruwa da tayi. To yaya kuma wanda ya shayar ko ya ciyar da Dan Adam, wanda darajarsa agun Allah tafi na kare!!.

Yaku 'Yan uwa Musulmai! Mu Qara kokari mu sanya himma sosai wajen taimakon al'ummah wajen ciyar dasu da shayar dasu don neman yardar Allah. Musamman gidajen marayu da asibitoci da makarantun Almajirai ako yaushe, ba sai cikin watan Ramadhana ba.

Idan kana neman waraka daga wata chutar dake damunka, ko neman yayewar wani bakin ciki, ko neman samun daukaka awajen aiki, ko biyan bukatunka awajen Allah, to ga hanya mafi sauki ita ce ka yawaita ciyarwa da shayar da bayin Allah. In sha Allahu Allah zai dubi wannan tausayin naka ga bayinsa, sai shi kuma ya biya ma bukatarka, ya yaye maka chutarka komai girmanta.

Allah yasa mu dace.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (09/07/2019).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI