MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari.

'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka :

YAQIN BADAR NA KARSHE :

Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar".

Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wancan yaqin badar din na farko).

Ya isa wajen tare da rundunar Sahabbansa (Allah ya yarda dasu) sai sai su kafiran Quraishawa sunji tsoro basu fito ba. Don haka aka juya zuwa Madeenah.

YAKIN DAUMATUL JANDAL :

Wasu Qabilu ne dake zaune awani gari a kauyukan Qasar Sham, chan kusa da Tabuka. Kuma wannan shine yaqi mafi nisa wanda Manzon Allah (saww) yaje da kansa (kafin tabuka).

Dalilin wannan yaqin shine, wadannan Qabilun sun kasance suna tsoratar da Attajiran musulmai masu wucewa ta garuruwansu. Don haka Manzon Allah (saww) ya fita acikin watan Rabee'ul Awwal a shekara ta biyar bayan hijirah, tare da sahabbai dubu daya domin ladabtar da wadannan Qabilun.

Yayin da suka ji labarinn gabatowar Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai suka tsere. Don haka Manzon Allah (saww) sai ya juya zuwa Madinah bai bibbiyi bayansu ba. Dama an fita ne domin a nuna razanar dasu don su dena ta'addancin da suke yiwa musulmai.

'Yan uwa ku dubi yadda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ryuwarsa take cikin gwagwarmaya ko yaushe. Ku dubi irin Qokarin da yayu wajen tabbatar da isar da sakon Ubangiji zuwa garemu.

Ya Allah ka saka masa da mafi alkhairin sakamakon da kake yiwa Annabawa bisa al'ummominsu. Ameen.

NA GABATAR DA KARATUN NE A ZAUREN FIQHU WHATSAPP RANAR 02/05/2019  26/08/1440.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI