Posts

KATATUN FIQHU ASAUKAKE

KARATUN FIQHU ASAUKAKE DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (DARASI NA GOMA SHA DAYA) BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salatin Allah da amincinsa da albarkarsa su tabbata ga wanda aka aikoshi domin Rahama ga dukkan Halittu. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan bayin Allah managarta. Idan ba'a manta ba, acikin darasi na goma mun tsaya ne akan Sunnoni da mustahabban alwala, kuma muna magana ne akan Sunnah ta goma sha bakwai. Yanzu kuma zamu dora in sha Allahu. 18. SUNNAH TA SHA TAKWAS : TSANTSAME JIKI BAYAN KAMMALA ALWALA KO WANKAN JANABA : Shi wannan mustahabbi ne awajen mafiya yawan Maluman Fiqhu. Musamman idan larura ta sanya yin hakan. Wasu ma suka ce yin hakan yana daga cikin ladubba masu kyau da kuma abubuwan kiwon lafiya. Wasu kuma daga cikin Maluman fiqhu sunce yin hakan yana daga cikin halastattun abubuwa wadanda shari'a bata hana ba, kuma bata ce ayisu ba. (Wato mutum zai iya yi ko kuma barinsu). Wasu kuma Maluman sun Qirga yin h...

ZUNUBI BABBAN CIWO!!!

Ya kai 'Dan uwa, ko kasan cewa Zunubi shine ciwo mafi Muni wanda yake samun 'Dan Adam?? ZUNUBI Wani irin ciwo ne wanda babbar 'barnar da yakeyi shine ya Afkar da mutum acikin wutar Jahannama. ZUNUBI yakan haifar ma 'Dan Adam Matsaloli iri daban-daban tun anan duniya. Kafin kuma aje lahirar. ZUNUBI yakan haifar ma Mutum Chututtuka masu yawa, amma daga ciki akwai: - TOSHEWAR BASIRA. - TOSHEWAR KOFOFIN ARZIKI. - RASHIN ALBARKAR RAYUWA. - RASHIN ALBARKAR ARZIKI. - BAQIN CIKI. - RASHIN WALWALA. - LALACEWAR ZUCIYA - LALACEWAR JIKI. - RASHIN DACEWA. - ZUBEWAR MUTUNCI. - RASHIN QIMA AWAJEN ALLAH. - MUMMUNAN TSUFA. - MUMMUNAR MUTUWA. - CIKAWA BA IMANI. - MUMMUNAR MAKOMA. Lallai Zunubi ba Qaramar matsala bane ga 'Dan Adam!! To shin yana da magani kuwa?? AMSA : Eh yana da magunguna kala kala.. Da farko zaka iya yin RIGA-KAFI (Vaccination) da ALLURAR TSORON ALLAH. (TAQWAH-QUINE). In sha Allahu idan kayi ma Zuciyarka Riga kafin tsoron Allah,  In sha Allahu ...

SHAITANUN ALJANU BASU SON AZKAR DIN SAFE

ALJANU BASU SON AZKAR DIN SAFE ***************************************** Azkar din safe shine abinda Shaitan ba yaso kayi.. Yafi sanya Maka kasala da nauyin jiki da kuma barci mai nauyi adaidai lokacin da kake zaune zakayi Azkar din.. Ko kasan dalili?? Dalili shine gabatar da azkar din safe in sha Allahu zaisa ka samu damar Wuni cikin Walwala da annashuwa tare da samun kariya daga Sharrin Shaitanun fili da na boye. Shi kuma shaitan yafi so ya ganka kullum acikin matsala! Shi yasa ba zaiso ka rika yin Azkar din ba.. Watarana Allah ya taimakeni na Kama wani Shaitanin Aljani Ajikin wani Saurayin Bil Adama. Sai na tambayi shi Aljanin : ZF: Bismillahi wa ke tare damu? ALJANI : Ni bani da suna. ZF : To Musulmi ne kai, ko kafiri?. ALJANI : Ni Musulmi ne. ZF: To Kaji tsoron Allah ka gaya mun gaskiya. Shine menene ya kawoka jikin wannan yaron? ALJANI : Na shiga jikinsa ne kawai don Mugunta. Ni nafi so in ganshi ko yaushe acikin matsala. Shi yasa na hanashi karatun addini ko na boko....

RAKUMI YAYI SUJADAH AGABANSA (SAWW)

Image
Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya bada labari cewa: "Akwai mutanen wani gida daga cikin Ansar (mutanen madeenah) suna da wani Rakumi wanda suke 'daukar ruwa dashi. Watarana sai Rakumin nan yayi musu bore, ya hana su dora masa komai. Sai wasu daga mutanen Madinah din suka garzayo wajen Shugaban Halitta (saww) suka gaya masa halin da suke ciki, kuma suka xe masa rakumin ya Qi daukar ruwan, kuma yanzu haka ga shukokinsu sun fara bushewa, Bishiyoyin dabinonsu duk yayi yaushi saboda rashin ruwa. Sai Ma'aiki (saww) yace ma Sahabbansa "KU TASHI MUJE". Sai suka tafi zuwa ga wani shinge (waro gona wacce aka katangeta) suka iske rakumin ya rakabe aciki, yaja daaga. Yayin da mutanen suka ga Manzon Allah (saww) ya nufi wajen inda rakumin yake, sai suka ce "Ya Rasulallahi Rakumin nan fa ya zamanto kamar Mahaukacin Kare, don haka muna tsorace maka sharrinsa". Sai Annabi (saww) yace "Ai babu abinda zai yi mun". Mai ruwayar (wato Anas bin Malik) yace : ...

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI

Idan kana tsoron cutarwa daga wani mutum, ko kana fuskantar cin mutunci daga gareshi, ko daga Jama'arsa, to ga addu'ar da zaka karanta domin samun kariya daga Allah. Kuma aniyarsu zata koma kansu in sha Allah. Ga addu'ar nan kamar haka: اللَّÙ‡ُÙ…َّ رَبَّ السَّÙ…َاوَاتِ السَّبْعِ، Ùˆَرَبَّ الْعَرْØ´ِ الْعَظِيمِ، ÙƒُÙ†ْ Ù„ِÙŠ جَاراً Ù…ِÙ†ْ (اِسمُÙ‡) ÙˆَØ£َØ­ْزَابِÙ‡ِ Ù…ِÙ†ْ Ø®...

KAR KA BAR DUNIYA TA RUDEKA!!!

Image
Wallahi duniya Mayaudariya ce, Makaryaciya ce, Kuma  Tsohuwa ce Mai Makirci. Babban dillalinta shine Shaitan. Mai Zakin baki, mai chusa Tunane-Tunane da Waswasia Zukatan Mutane!! Yayin da Allah ya baka lafiya da dukiya da Mulki da 'Ya'ya, Sai shaitan La'ananne yazo ya rika Qawat maka zaman duniyar nan. Ba zai barka ka tuna da lahira ba, ballantana kayi tanadin tafiya, ko kuma guzuri domin gyaran lahira.. Kullum idan anyi zancen "LAHIRA" sai shaitan ya chusa ma Zuciyarka damuwa da kuma Baqin ciki.. Kai babu labarin da kafi son ji in banda labarin "DUNIYA" da abin cikinta wanda ba zai amfaneka ba.. Ko kuma labaran da zasu Qara maka sakankancewa acikin sa'bon Allah..!! WALLAHI SHAITAN MAKIYINKA NE! BA ZAI YARDA KA SAMU JIN DADIN LAHIRA BA.. Kullum yana Qars shagaltar dakai yana nuna maka duniya, Zuciyarka tana qara Makancewa da lahira.. Da haka har ranar da Mala'ikan Mutuwa Zai kawo maka Ziyarar Qarshe!! Babu wani mai rai fache kullum sai Mala...

SHIN BA ZAKA JI KUNYAR UBANGIJINKA BA?

YA KAI 'DAN ADAM!! Shin ba zaka ji kunyar Allah ba??  Kullum shi yake baka ci da sha da numfashin da kake shaqa, Amma godiyarka ta tafi zuwa ga waninsa, Sa'bonka kuma ya tafi zuwa ga Allah din. Kana nuna ma mutane kamar cewa kai mutumin kirki ne, alhali akwai Miyagun ayyukanka da ka boye, da kuma Miyagun tunanin dake Qunshe a zuciyarka.. Ubangiji ya san dasu amma bai ta'ba tona maka asiri ba.. Kullum rufa maka asirinka yakeyi, amma kai kuma kana Qara butulce masa. Kullum Qara turo maka Ni'imominsa yakeyi, amma Maimakon ka gode masa sai kake ganin kamar hikimarka ce ko kuma wayonka ne suke baka. Yanzu idan kana dauke da Olsa (Ulcer) ko Hawan jini ko Diabetes (Ciwon Sugar) duk abincin da likita ya hanaka ci, Sai kayi shekaru baka cishi ba, saboda mae?? Saboda kana tsoron MUTUWA!!! Amma Ubangijinka wanda ya hakicceka yace maka : - QARYA BABU KYAU. - GULMA BABU KYAU. - SATA BABU KYAU. - SHIRKA BABU KYAU. - GIRMAN KAI BABU KAYU. - ZINA BABU KYAU. - TUNANIN AIKATA ...