ZUNUBI BABBAN CIWO!!!


Ya kai 'Dan uwa, ko kasan cewa Zunubi shine ciwo mafi Muni wanda yake samun 'Dan Adam??

ZUNUBI Wani irin ciwo ne wanda babbar 'barnar da yakeyi shine ya Afkar da mutum acikin wutar Jahannama.

ZUNUBI yakan haifar ma 'Dan Adam Matsaloli iri daban-daban tun anan duniya. Kafin kuma aje lahirar.

ZUNUBI yakan haifar ma Mutum Chututtuka masu yawa, amma daga ciki akwai:

- TOSHEWAR BASIRA.
- TOSHEWAR KOFOFIN ARZIKI.
- RASHIN ALBARKAR RAYUWA.
- RASHIN ALBARKAR ARZIKI.
- BAQIN CIKI.
- RASHIN WALWALA.
- LALACEWAR ZUCIYA
- LALACEWAR JIKI.
- RASHIN DACEWA.
- ZUBEWAR MUTUNCI.
- RASHIN QIMA AWAJEN ALLAH.
- MUMMUNAN TSUFA.
- MUMMUNAR MUTUWA.
- CIKAWA BA IMANI.
- MUMMUNAR MAKOMA.

Lallai Zunubi ba Qaramar matsala bane ga 'Dan Adam!! To shin yana da magani kuwa??

AMSA : Eh yana da magunguna kala kala.. Da farko zaka iya yin RIGA-KAFI (Vaccination) da ALLURAR TSORON ALLAH. (TAQWAH-QUINE).

In sha Allahu idan kayi ma Zuciyarka Riga kafin tsoron Allah,  In sha Allahu kwayar chutar Zunubi ba zata kusanto wajenka ba.. Kuma koda tazo ba zata iya chutar da kai ba. Domin kuwa wannan tsoron Allah din dake tare dakai shi zai kashe maka  Kwayoyin chutar tun kafin su ratsa Jikinka

TAMBAYA : To yaya zanyi, idan har na riga na kamu da wannan chutar, Domin yanzu awannan Zamanin muna cikin wani Epidemic ne (ANNOBA) irin ta Zunubai kala kala.. Shin yaya zanyi in rika tsarkake kaina??

AMSA : Yadda zakayi shine ka yawaita shan wadannan Kwayoyin :

- TUBA.
- NADAMA.
- ISTIGHFARI.
- TASBEEHI.
- HAILALA.
- SALATUN NABIYYI (SAWW).
- KARATUN ALQUR'ANI.

Kuma ka rika wasa Jikinka da yawan Ibadah, Kula da Sallolinka na farilla da nafilfili, Yawaita Sadaqah, Kulawa da Hakkin iyaye, Marayu, Makobta, etc.

Manzon Allah (saww) yace "DUKKANKU MASU LAIFI NE. AMMA MAFIYA ALKHAIRIN MASU LAIFI SUNE WADANDA SUKE YAWAN TUBA".

Ya Allah ka gafarta mana dukkan laifukanmu, ka Qara mana tsoronka, ka tsarkake mana Zukatanmu. La Qara mana Ikhlasi da Qaunar Annabinka (saww) da tsananin biyayya gareshi. Aaameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU (19-02-2016).

Munyi ma daliban Zauren Fiqhu Izinin Forwarding din wannan tunatarwar zuwa ga al'ummar Musulmai. Amma DON GIRMAN ALLAH kar wani ya kwafa ya chanza mana!

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI