KAR KA BAR DUNIYA TA RUDEKA!!!


Wallahi duniya Mayaudariya ce, Makaryaciya ce, Kuma  Tsohuwa ce Mai Makirci.

Babban dillalinta shine Shaitan. Mai Zakin baki, mai chusa Tunane-Tunane da Waswasia Zukatan Mutane!!

Yayin da Allah ya baka lafiya da dukiya da Mulki da 'Ya'ya, Sai shaitan La'ananne yazo ya rika Qawat maka zaman duniyar nan. Ba zai barka ka tuna da lahira ba, ballantana kayi tanadin tafiya, ko kuma guzuri domin gyaran lahira..

Kullum idan anyi zancen "LAHIRA" sai shaitan ya chusa ma Zuciyarka damuwa da kuma Baqin ciki.. Kai babu labarin da kafi son ji in banda labarin "DUNIYA" da abin cikinta wanda ba zai amfaneka ba.. Ko kuma labaran da zasu Qara maka sakankancewa acikin sa'bon Allah..!!

WALLAHI SHAITAN MAKIYINKA NE! BA ZAI YARDA KA SAMU JIN DADIN LAHIRA BA.. Kullum yana Qars shagaltar dakai yana nuna maka duniya, Zuciyarka tana qara Makancewa da lahira.. Da haka har ranar da Mala'ikan Mutuwa Zai kawo maka Ziyarar Qarshe!!

Babu wani mai rai fache kullum sai Mala'ikan Mutuwa ya kawo masa Ziyara sau Saba'in.. Yana zuwa yana duba agogon Zuciyarka, yana ganin sauran lokacin da ya rage maka!!

Duk ranar da ajalinka ya cika, Mala'ikan zai tarar dakai baka shirya ba, Baka kintsa ba, Baka tanadi Guzuri ba.. Kuma WALLAHI ba za'a jinkirta maka koda SECOND GUDA ba!!

Zai Fizgi ranka ya tafi dashi zuwa wajen Ubangijin nan naka wanda baka son haduwa dashi!!! LA ILAHA ILLLAL LAHU MUHAMMADUR RASULULLAHI!!!

Daga wannan ranar shikenan taka ta Qare.. Kodai ka huta kenan, Ko kuma an huta da sharrinka. WALLAHI KODA KA MALLAKI ZINARE (GOLD) DA LU'U-LU'U (💎) CIKIN DUNIYAR NAN, Ba zasu yi maka amfani ba.. Ba zasu tare maka azabar Allah ba!!! (Sai dai in ka ciyar dasu bisa tafarkin Taimakon Marayu, Miskinai, Masallatai, Makarantu, Zumunci, taimakon al'ummah da sauransu).

Amma idan ba haka ba, DUKIYA SHARRI CE GAREKA YA KAI DAN UWA!! Wallahi ba zaka matsa daga gaban Zatin Ubangiji ba, fache sai ka amsa tambaya akan kowanne KOBO DA SISI DA NAIRA DA DALOLIN DA SUKA SHIGO HANNUNKA :

- Ta yaya ka samu?
- Mai kayi dasu?
- Ta ina ka 'batar?

Kuma sai an tambayeka akan kowacce Ni'imar da ka mora aduniya. Wato kamad irin su LAFIYA, KURUCIYA, IDONKA DA KAKE GANI DASHI, Kunnenka da kake ylji dashi, Fatar Jikinka, Harshenka da kake magana dashi, Qafarka da hannayenka Har al'aurarka duk baki daya..

Allah zai tambayeka :

- Mai kayi da dukkan Ni'imominsa da ya hore maka??
- Cikin neman yardarsa ka tafiyar dasu, ko kuma wajen bin SON ZUCIYARKA??

Aranar nan babu Lawyer, Kuma gabobin Jikinka su zasu bada shaida gareka, ko kuma akanka. Sannan Mala'iku zasu bada shaida gareka ko akanka!!

'Dan uwana, Wannan Tunasarwa ce domin ka san halin da kake ciki.. Amma lokacin tuba bai Qure maka ba.. Don haka yi sauri ka tuba yanzun nan. Don baka san yaushe ne Mala'ikan Mutuwa zai Ziyarceka ba.. Zata yiwu yanzun nan ne, ko sai anjima, ko gobe ne, ko jibi ne, (Wallahu A'ALAM).

Amma dai Ubangiji ya riga ya gargadeka. Lallai Wa'azi yazo maka. Kuma ka karanta a Zauren Fiqhu. Don haka Ubangiji yana da Hujjah akanka.

Kai wacce Hujjar kake da ita da zaka kare kanka??

Hujjah  ita ce Kaji tsoron Allah afili da boye tare da yin biyayya ga dokokinsa.

- Kula da sallolinka na farilla da nafilfili.
- Fitar da Zakkar dukiyarka tare da yawaita sadaqah (domin ita sadaqah Hujjah ce). Koda dukiyarka bata kai zakkah ba.
- Kulawa da hakkin Iyaye, 'yan uwanka na Zumunci da kuma makobta.
- Karatun Alqur'ani, Zikirin Allah da Salatin Manzon Allah (saww).

- Raba zuciyarka daga sharrin girman kai, Dogon buri, Qarya, Hassada, Munafurci, etc.

"KA TUNASAR, DOMIN HAKIKA TUNASARWA TANA AMFANAR DA MUMINAI".

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (14-02-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI