KATATUN FIQHU ASAUKAKE

KARATUN FIQHU ASAUKAKE DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (DARASI NA GOMA SHA DAYA)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salatin Allah da amincinsa da albarkarsa su tabbata ga wanda aka aikoshi domin Rahama ga dukkan Halittu.

Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan bayin Allah managarta.

Idan ba'a manta ba, acikin darasi na goma mun tsaya ne akan Sunnoni da mustahabban alwala, kuma muna magana ne akan Sunnah ta goma sha bakwai. Yanzu kuma zamu dora in sha Allahu.

18. SUNNAH TA SHA TAKWAS : TSANTSAME JIKI BAYAN KAMMALA ALWALA KO WANKAN JANABA : Shi wannan mustahabbi ne awajen mafiya yawan Maluman Fiqhu. Musamman idan larura ta sanya yin hakan.

Wasu ma suka ce yin hakan yana daga cikin ladubba masu kyau da kuma abubuwan kiwon lafiya.

Wasu kuma daga cikin Maluman fiqhu sunce yin hakan yana daga cikin halastattun abubuwa wadanda shari'a bata hana ba, kuma bata ce ayisu ba. (Wato mutum zai iya yi ko kuma barinsu).

Wasu kuma Maluman sun Qirga yin hakan acikin Makruhai (wato abubuwan da aka hana).

Sai dai magana mafi inganci ita ce yin hakan yana daga cikin Mustahabbai. Saboda abinda muka riga muka fada cewar yin hakan yana daga cikin ladubba da kuma kiwon lafiya.

Kuma an ruwaito hadisai masu yawa da suke nuna cewa Manzon Allah (saww) ya kasance yana yon hakan. Duk da cewa hadisan Dha'eefai ne, to amma Malamai sunce Idan Dha'ifan hadisai sukayi yawa akan Wata Mas'ala guda, to lallai suna Qarfafar Junansu. Wato za'a iya dunkulesu waje guda ayi aiki dasu.

Kuma ma akwai Sahihai daga cikinsu kamar hadisin da Imamul Baihaqiy da Nisa'iy suka ruwaito tare da isnadi SAHIHI daga Iyaas bn Ja'afar daga wani Sahabi yana cewa :

"Hakika Manzon Allah (saww) ya kasance yana da wani Mayani ko kuma Kyalle wanda yake goge fuskarsa dashi idan yayi alwala".

Maluman da suka karhanta yin haka, su kuma suna kafa Hujjah ne da hadisin da Sayyiduna Abdullahi 'dan Abbas (ra) ya ruwaito daga 'Yar uwar Mahaifiyarsa, kuma Matar Manzon Allah (saww) wato Sayyidah Maimunatu Bintul Harith (rta) tace :

"Na ajiye ma Manzon Allah (saww) ruwan da zai yi wankan Janabah dashi, sai na Mika masa Kyalle amma bai karba ba. Sai ya rika gogewa da hannunsa".

(Bukhariy ne ya ruwaito).

Amma Maluman da suka ce Mustahabbi ne ayi haka, sun dauki wannan hadisin amatsayin cewa yana fa'idantar da cewa ya halatta abar kyallen, wadancan hadisan na farko kuma suna nuna halascin yi da kyallen. Wato ya zama yinsa da kuma barinsa duk ya halatta.

Amma idan larura kamar sanyi, ko Mura ko kuma wata jinyar tana tare da mutum, to kaga yin hakan ya zama Mustahabbi kenan domin maganin larurar.

Anan muka kawo karshen Sunnoni da Mustahabban Alwala. Kuma zamu shiga cikin Makruhai (wato abubuwan da aka Hana yinsu acikin alwala) in sha Allah.

MAKRUHAN ALWALA
************************
Alwala tana da Makruhai wato abubuwan da yinsu bai 'bata alwalar ba, amma zai iya kaiwa ga rashin samun cikakkiyar ladan ibadar.

Zamu iya tattarosu gaba daya acikin abinda ke tafe kamar haka:

1. BARIN WATA SUNNAH: An karhanta mutum ya bar wata sunnah daga sunnonin nan da muka lissafa. Domin kuwa barin sunnah daga cikin ibada, zai kai mutum zuwa ga samun tauyewar aikinsa. Kuma duk wanda ya bar wata sunnah, to ba zai samu ladanta ba.

Kuma bai kamata Musulmin da yake kaunar Allah da Manzonsa (saww) ya rika barin Sunnah da gangan ba. Domin yin haka zai sa ya rika wulakanta ita kanta ibadar, harma watarana ya bar farilla ma.

Gashi kuma Manzon Allah (saww) yayi Wasiyyah ga al'ummarsa cewa lallai mu kiyaye sunnarsa muyi riko da ita gam-gam.

Inda yake cewa "KUYI RIKO DA SUNNAH-TA DA SUNNAR HALIFOFI SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA WADANDA ZASU ZO ABAYANA. KU RIKETA DA HAKORANKU NA CIZO".

(Tirmidhiy da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi).

Sai dai wanda ya bar wata Sunnah bisa kuskure ko mantuwa, to babu Zunubi akansa domin kuwa Allah ya riga ya yafe ma wannan al'ummar duk abinda sukayi cikin kuskure ko mantuwa. Ko kuma abinda aka tilastasu akansa. Kamar yadda hadisai Sahihai masu yawa suka tabbatar.

Bisa wannan ya kamata duk Musulmi idan zai yi alwala yayita Cikakkiya sosai tare da Farillanta da Sunnoninta. Domin samun cikakken ladanta.

Imamun Nisa'iy ya ruwaito hadisi daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

"DUK WANDA YAYI ALWALA IRIN YADDA AKA UMURCESHI, KUMA YAYI SALLAH KAMAR YADDA AKA UMURCESHI, TO AN GAFARTA MASA ABINDA YA GABATA NA ZUNUBANSA".

Allah Madaukakin Sarki yana so idan bawansa zai yi wani aiki, to ya kyautatashi, kuma ya cikashi.

2. YIN ALWALA AWAJE MAI NAJASA : Malamai sunce Makruhi ne yin alwala awaje mai najasa, sai dai in da larura.

Kuma sai dai in mutum ya tabbatar cewa ruwan da ya sauka akan najasar ba zai fantsalu ajikinsa ba.

Acikin wannan akwai sauki ga mutumin da bashi da wajen yin alwala ko wanka agidansa sai dai bandaki. Domin shi addinin Musulunci sauki ne dashi acikin Umurninsa da haninsa.

3. YIN MAGANA YAYIN ALWALA : Shi ma wannan Makruhi ne. Sai dai in da larura. Amma babu laifi ka amsa Sallama, ko kuma yin addu'a ga masu atishawa.

4. MARIN FUSKA YAYI ALWALA : Shima wannan Makruhi ne mai alwala ya rika zuba ruwa da karfi aoan fuskarsa. Domin babu ladabi cikin yin hakan. kuma zai sa yayi kama da mutanen da suke marin fuskarsu din nan yayin musiba.

Kuma lallai wasu Makruhan sunfi wasu Qarfi wajen karhanci. Misali kamar barin Sunnah karhacinsa yafi Qarfi fiye da marin fuska yayin alwala.

Kayi sani cewa Shi dai Makruhi akwai lada cikin barinsa. Amma babu Ukuba akan wanda yayishi. Sai dai barin nasa yafi.

Anan zamu dakata. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka ji. Allah shi Qara mana ilimi mai albarka.

An gabatar da wannan darasin ne a Zauren Fiqhu Whatsapp (1) aranar Asabar 20-02-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI