SHIN BA ZAKA JI KUNYAR UBANGIJINKA BA?

YA KAI 'DAN ADAM!! Shin ba zaka ji kunyar Allah ba??  Kullum shi yake baka ci da sha da numfashin da kake shaqa, Amma godiyarka ta tafi zuwa ga waninsa, Sa'bonka kuma ya tafi zuwa ga Allah din.

Kana nuna ma mutane kamar cewa kai mutumin kirki ne, alhali akwai Miyagun ayyukanka da ka boye, da kuma Miyagun tunanin dake Qunshe a zuciyarka.. Ubangiji ya san dasu amma bai ta'ba tona maka asiri ba..

Kullum rufa maka asirinka yakeyi, amma kai kuma kana Qara butulce masa. Kullum Qara turo maka Ni'imominsa yakeyi, amma Maimakon ka gode masa sai kake ganin kamar hikimarka ce ko kuma wayonka ne suke baka.

Yanzu idan kana dauke da Olsa (Ulcer) ko Hawan jini ko Diabetes (Ciwon Sugar) duk abincin da likita ya hanaka ci, Sai kayi shekaru baka cishi ba, saboda mae?? Saboda kana tsoron MUTUWA!!!

Amma Ubangijinka wanda ya hakicceka yace maka :

- QARYA BABU KYAU.
- GULMA BABU KYAU.
- SATA BABU KYAU.
- SHIRKA BABU KYAU.
- GIRMAN KAI BABU KAYU.
- ZINA BABU KYAU.
- TUNANIN AIKATA FASADI KOWANNE IRI MA BABU KYAU..

Yace maka duk wadannan HARAMUN NE, Kuma zasu kai ka Zuwa ga shiga Wuta, Amma duk da haka gashi nan kana yinsu babu dare babu rana... SHIN GASKATASHI NE BAKAYI BA?? KO KUWA LIKITAN ASIBITI YAFI UBANGIJINKA FA'DAR GASKIYA NE???

Ya Allah mun tuba ka yafe mana... Idan mu halinmu ne muyi sa'bo saboda raunin zukatanmu, To kai kuma halinka ne yin Qafara da Rahama da Afuwa ga bayinka ba tare da hisabi ba. Ya Allah ka Tsaftace zukatanmu daga dukkan abinda baka so. Ka sanyamu cikin bayinka Masu shiryuwa da kuma shiryarwa zuwa gareka. Ba Batattu ba, kuma ba masu batarwa ba. Aaameeen.

Wannan Nasihar safe ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (14-02-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI