Posts

Showing posts from January, 2016

IDAN AKA SANYA BAWA ACIKIN QABARINSA

Image
Y ayin da aka sanya bawa acikin Qabarinsa, sai Qabarin yace masa : "KAICHONKA YA KAI 'DAN ADAM!! WAYE YA RUDEKA DAGA GARENI? "SHIN BAKA SAN CEWA NINE GIDAN FITINA BA? KUMA (NINE) GIDAN DUHU, KUMA (NINE) GIDAN KADAITAKA, KUMA (NINE) GIDAN TSUTSOTSI!!!" MENENE YA RU'DAR DAKAI ALHALI KA KASANCE KANA WUCEWA TA KUSA DANI ALOKUTA DA YAWA". To idan mutumin kirki ne (Mamacin) Sai wani amsawa (Wato Mala'ika) daga cikin Qabarin yace ma Qabarin "Shin yaya kake gani idan ya kasance yana Umurni da aikin alkhairi, kuma yana hani daga Mummuna?". Sai Qabarin yace "TO IN DAI HAKA NE, TO LALLAI NI ZAN ZAMANTO DAUSAYI NE GARESHI.. KUMA JIKINSA ZAI KOMA HASKE, KUMA RUHINSA ZAI TAFI ZUWA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI". # Ibnu Abid Dunya ne ya ruwaito hadisin daga Abul Hajjaj Ath-Thumaliy (ra) daga Manzon Allah (saww). # Ibnul Munkadir shima ya ruwaito irin wannan daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra). # Mu'awiyatu bn Salih ma ya ruwaito

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (009)

MUTUWA TARE DA IMANI **************************** Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-aas (ra) yace Manzon Allah (saww) yace : "DUK WANDA YAKE SO ATSALLAKAR DASHI DAGA SHIGA WUTA KUMA A SHIGAR DASHI ALJANNAH, TO YAYI KOKARI MUTUWARSA TA RISKESHI ALHALI YANA MAI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA YAZO MA MUTANE DA IRIN ABINDA SHIMA YAKE SO AZO MASA DASHI (WATO YASO MA MUTANE IRIN ABINDA YAKE SO MA KANSA). ADUBA: # TAFSEERIN IBNU KATHEER JUZU'I NA 1 SHAFI NA 389. # MUSNADU AHMAD JUZU'I NA 2 SHAFI NA 191. DARASI ******** Wannan hadisin yana kunshe da bishara ne sannan kuma da gargadi. Gargadin shine wato lallai ne ya zama tilas garemu muyi kokari mu kiyaye imaninmu. Domin bamu da abinda ya kaishi ballantana yafi shi. Mu kiyayi duk abinda yake janyo ma mutane zubewar imaninsu kamar : 1. Haramta halal, ko Halalta haram. 2. Shirka, tsafi, Bori, bokanci, etc. 3. Chutar da Manzon Allah (saww) afili Qarara ko aboye, ko ta hanyar chutar da wani wanda idan a

LABARIN WASU MUTANE GUDA BIYU

Image
Wani mutum daga cikin Banu Isra'eela yaje wajen wani daga cikinsu ya tambayeshi ranchen kudi DINARE DUBU. (1,000 Dinars). Sai mutumin yace "Ina so ka kawo min shaidu wadanda zan kafasu amatsayin Masu bada shaida". Sai shi mai neman ranchen yace "Allah shine Shaida". Yace to kawo min wanda zai maka lamuni. Sai yace "Ai Allah ya isar mana amatsayin Mai lamuni". Sai shi mai kudin yace "Lallai kayi gaskiya". Ya kawo kudin ya bashi, sukayi alkawari zuwa wani lokaci. Sai shi Wanda yayi ranchen ya fita ya hau jirgin ruwa yayi tafiyarsa. Yaje ya biya bukatarsa da kudin. Da lokacin biyan bashin yayi, sai yazo bakin ruwa (tashar jiragen ruwa) don neman jirgin ruwan da zai daukeshi zuwa wancan garin domin cika alkawarin da ya dauka. Ya jira amma bai samu abin hawa ba. Don haka sai ya nemi wani itace ya tsagashi gida biyu, ya sanya kudin acikinsa, Sannan ya rubuta wasika ya sanya aciki, sannan ya mayar ya rufe. Ya dauko yazo dashi bakin kogin. Sa

SHI BA MUTUM NE KAMAR KOWA BA

Image
Lallai Annabi Muhammadu (saww) mutum ne 'dan Adam a jinsinsa.. Amma acikin zatinsa ba kamar kowa yake ba. Acikin Alqur'aninsa wanda Allah ya saukar masa, yace : "KACE (MUSU) NI MUTUM NE IRINKU, AMMA ANA YIN WAHAYI ZUWA GARENI". Bari dai shi Annabi ne, kuma acikin Annabawan ma ba kamar kowa yake ba.. Shi Manzo ne, amma acikin Manzannin ma ba kamar kowa yake ba. Kasancewarsa mutum irinka a jinsi, ba ya nufin cewa kamar kai yake... A'a ba haka bane. Bambancin dake tsakaninsa da sauran Mutane baki daya, kamar bambancin dake tsakanin DIAMOND 💎 (LU'U-LU'U) ne da sauran duwatsu. Babban abinda ya hana kafiran Makkah su sallama masa su Musulunta, shine Suna ganin cewa "Wai shi mutum ne irin su". Wasu kuma suna ganin cewa "Ai marayan nan ne na gidan Abu Talib". Har ma Allah ya bada labarin irin wannan tunanin nasu acikin Alqur'aninsa inda yake cewa "KUMA SUN CE MAI YA SAMU WANNAN MANZON NE, YANA CIN ABINCI (KAMAR YADDA SUMA SUKE CI

LABARIN UMMU MALIK (RTA)

Akwai Wata Mata mai suna Ummu Malik ta kasance tana hidimta ma Manzon Allah (saww). Watarana ta zuba Man girki acikin Salka sannan ta tafi dashi ta kai masa (saww). To rannan ta wayi gari batta da Man gyadan ya Qare. Kuma gashi 'Ya'yanta suna bukatarsa zasu ci abinci. Da taje ta dauko Salkar sai ta tarar da ita acike Fal da man gyada. Ta dauko ta bama yaranta suka ci abinci dashi.. Ta kasance duk lokacin da take bukatar Mai agidanta, da ta dauko salkar sai ta tarar da ita acike Gal da mai. Rannan kawai sai ta juye man, ta tatse Salkar gaba daya... Tun daga ranar sai ta deba ganin Komai acikin salkar. Don haka taje ta sanar da Manzon Allah (saww). Sai yace mata : "DA ACHE BAKI TATSESHI BA, DA SAI YA ISHEKI HAR TSAWON RAYUWARKI". Acikin wata ruwayar kuma ance da ta koma gida sai taga Salkar man gyadar kamar ba'a juye ba.  Don haka sai hankalinta ya tashi. Ta dawo wajen  Manzon Allah (saww) Tace masa "Ya Rasulallahi ko an saukar da wata ayah. e game dani?

GARABASA GA MA'ABOTA KIYAMUL LAYLI

Image

MAGANIN CIWON KAI

TAMBAYA TA 1829 ******************** Assalamu Alaikum, Malam da fatan kana cikin koshin lafiya da kai da iyalinka Allãh ya karawa Malam daraja da kuma lafiya. Malam ni dai na kasance ina fama ne dawani ciwon kayi mai tsananin zafin gaske wanda yakan iya tashina ko ina bacci ne kuma Malam idan ya fara yakan rike gefen hagun kai na ne, shine nake rokon taimako. Nagode, Bissalam. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ciwon kai yana daga cikin chutukan da ake fama dasu yau da kullum. Kuma yana da dalilai ko Musabbabai da yawa. Amma ga wasu fa'idodi masu albarka ka jarraba. In sha Allahu zaka dace : 1. SURATUL FATIHA : Malaman Musulunci sun ce lallai fatiha tana maganin kowacce irin chuta ajikin 'Dan Adam. Yadda zakayi amfani da ita domin magance matsalar ciwon kai shine: Kayi Basmalah ka sanya hannunka na dama ka rike goshinka ko kuma wajen da yafi ciwon. ka karanta Fatiha Qafa daya sannan ka saki kan naka. In sha Allahu zaka ji ya Dena. Idan bai d

SU WANENE MASU ARZIKI??

Ko kun san cewa masu tarin Nairori da Daloli ba sune masu arziki ba, Hakanan Qaton gida ko Babbar Mota duk ba sune alamomin arziki ba. # Masu arziki sune mutanen da suka shagaltu da kallon laifukan kansu, basu damu da kallon laifukan mutane ba. Sai suka kwadaitu da gyaran zukatansu.. Da kuma mikar da karkatattun halayen Zukatansu, Kuma suka yi. a kansu Hisabi anan duniya tun kafin ayi musu hisabi aranar Alqiyamah. # MASU ARZIKI sune mutanen da suka fahinci mecece rayuwar duniyar nan, Suka fahimci cewa ita duniya ba gidan zama bane. Gida ne mai shudewa. Don Haka suka ribaci lokutan rayuwarsu cikin aikata abinda Allah yake so. # MASU ARZIKI Sune masu ambaton Allah atsaye, da kuma azaune ko a kwance akan hakarkarinsu.. Kuma suke yawaita neman gafarar Allah bisa laifukansu, da kuma Takitawarsu acikin lamarin Ubangiji (SWT). # MASU ARZIKI sune wadanda Hassada ko Kyashi basu samu hanyar shiga cikin zukatansu ba. Idan wani abu mai kama da haka ya bijiro musu, sukan yi kokarin gusar dsshi