HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (009)

MUTUWA TARE DA IMANI
****************************

Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-aas (ra) yace Manzon Allah (saww) yace :

"DUK WANDA YAKE SO ATSALLAKAR DASHI DAGA SHIGA WUTA KUMA A SHIGAR DASHI ALJANNAH, TO YAYI KOKARI MUTUWARSA TA RISKESHI ALHALI YANA MAI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA YAZO MA MUTANE DA IRIN ABINDA SHIMA YAKE SO AZO MASA DASHI (WATO YASO MA MUTANE IRIN ABINDA YAKE SO MA KANSA).

ADUBA:

# TAFSEERIN IBNU KATHEER JUZU'I NA 1 SHAFI NA 389.

# MUSNADU AHMAD JUZU'I NA 2 SHAFI NA 191.

DARASI
********
Wannan hadisin yana kunshe da bishara ne sannan kuma da gargadi. Gargadin shine wato lallai ne ya zama tilas garemu muyi kokari mu kiyaye imaninmu. Domin bamu da abinda ya kaishi ballantana yafi shi.

Mu kiyayi duk abinda yake janyo ma mutane zubewar imaninsu kamar :

1. Haramta halal, ko Halalta haram.
2. Shirka, tsafi, Bori, bokanci, etc.

3. Chutar da Manzon Allah (saww) afili Qarara ko aboye, ko ta hanyar chutar da wani wanda idan an tabashi kamar ab ta'ba Annabin ne. (saww).

3. Chutar da Sahabbai da Ahlul baiti. Duk mai wulakantasu ba zai cika da imani ba.

4. Kafirta Musulmi bisa dalilin bambancin ra'ayin Mazhabi ko Fahimta. Ko kuma akan wani dalilin da ya shafi harkokin duniya kamar siyasa etc.

Bayan haka kumahadisin yana nuna mana cewa mu kiyaye hakkin 'Yan uwanmu Musulmai. Muyi musu irin Mu'amalar nan mafi kyawu wacce muke so muma ayi mana.

Wato Kamar irin su :

TAWADHU'U, GASKIYA, RIKON AMANA, RANGWAME, HAKURI, KYAUTATAWA, MUTUNTAWA, GIRMAMAWA, KUNYA, JURIYA, YAFEWA, ETC.

Mu kula da kanmu ta hanyar tsaftace dattin dake cikin zukatanmu kamar irin su Hassada, Qarya, girman kai, rowa, etc.

Mu dena hangen laifukan Mutane alhali mu kanmu masu laifi ne.

Allah shi taimakemu Aaameeen.

ZAUREN FIQHU (20-01-2016)

www.facebook.com/zaurenfiqhu1

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI