MAGANIN CIWON KAI

TAMBAYA TA 1829
********************
Assalamu Alaikum, Malam da fatan kana cikin koshin lafiya da kai da iyalinka Allãh ya karawa Malam daraja da kuma lafiya.

Malam ni dai na kasance ina fama ne dawani ciwon kayi mai tsananin zafin gaske wanda yakan iya tashina ko ina bacci ne kuma Malam idan ya fara yakan rike gefen hagun kai na ne, shine nake rokon taimako. Nagode, Bissalam.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ciwon kai yana daga cikin chutukan da ake fama dasu yau da kullum. Kuma yana da dalilai ko Musabbabai da yawa. Amma ga wasu fa'idodi masu albarka ka jarraba. In sha Allahu zaka dace :

1. SURATUL FATIHA : Malaman Musulunci sun ce lallai fatiha tana maganin kowacce irin chuta ajikin 'Dan Adam. Yadda zakayi amfani da ita domin magance matsalar ciwon kai shine: Kayi Basmalah ka sanya hannunka na dama ka rike goshinka ko kuma wajen da yafi ciwon. ka karanta Fatiha Qafa daya sannan ka saki kan naka. In sha Allahu zaka ji ya Dena.

Idan bai dena ba, ka sake rikewa sannan ka karanta Fatiha din Qafa uku. Zaka ji ya dena. Idan kuma bai dena ba, ka karanta Qafa biyar. idan bai dena ba, ka karanta Qafs bakwai. In Allah ya yarda zakaji ka warke nan take.

2. HAYAKIN HABBATUS SAUDA : Ka samu kwayoyin Habbatus Sauda ka zuba acikin Garwashi sannan ka rika shekar hayakin. In sha Allahu zakaji babu ciwon kan.

3. MAN TAFARNUWA, MAN GELO : Kowannensu idan ka shafa zaka samu waraka daga ciwon kan.

Allah ya sawwake. Allah ya yaye maka.

WALLAHU A'ALAM.

ZAUREN FIQHU (04-01-2016).

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI