SHI BA MUTUM NE KAMAR KOWA BA

Lallai Annabi Muhammadu (saww) mutum ne 'dan Adam a jinsinsa.. Amma acikin zatinsa ba kamar kowa yake ba.

Acikin Alqur'aninsa wanda Allah ya saukar masa, yace : "KACE (MUSU) NI MUTUM NE IRINKU, AMMA ANA YIN WAHAYI ZUWA GARENI".

Bari dai shi Annabi ne, kuma acikin Annabawan ma ba kamar kowa yake ba.. Shi Manzo ne, amma acikin Manzannin ma ba kamar kowa yake ba.

Kasancewarsa mutum irinka a jinsi, ba ya nufin cewa kamar kai yake... A'a ba haka bane. Bambancin dake tsakaninsa da sauran Mutane baki daya, kamar bambancin dake tsakanin DIAMOND 💎 (LU'U-LU'U) ne da sauran duwatsu.

Babban abinda ya hana kafiran Makkah su sallama masa su Musulunta, shine Suna ganin cewa "Wai shi mutum ne irin su". Wasu kuma suna ganin cewa "Ai marayan nan ne na gidan Abu Talib".

Har ma Allah ya bada labarin irin wannan tunanin nasu acikin Alqur'aninsa inda yake cewa "KUMA SUN CE MAI YA SAMU WANNAN MANZON NE, YANA CIN ABINCI (KAMAR YADDA SUMA SUKE CI) KUMA YANA YAWO ACIKIN KASUWANNI (DON YIN KASUWANCI KAMAR KOWA).

MAI YASA BA'A SAUKAR MASA DA MALA'IKA WANDA ZAI KASANCE MAI YIN GARGADI TARE DASHI BA?. KO KUMA A SAUKAR MASA DA TASKA (WATO YA ZAMA MAI KUDI, BA SAI YA NEMA BA) KO KUMA YA KASANCE YANA DA WATA GONA WACCE ZAI RIKA CIN ABINCI DAGA CIKINTA".

(FURQAN ayah ta 7).

Awani wajen Kuma Allah yana bada labarin kafiran da suka gabata, sai yace "SAI SUKA CE : "KU FA BA KOMAI BANE ILLA MUTANE KAMAR MU, KUNA SO NE KU JUYAR DAMU DAGA KAN ABINDA IYAYENMU SUKA ZAMANTO SUNA BAUTA MA".

To jama'a idan kukayi nazarin wadannan maganganun duk zaku ga akwai tsantsar jahilci da rainin wayo, da kuma rashin hankali da toshewar basira.

Hakanan su ma Munafukan garin Madeenah, irin wannan rainin wayon ne a zukatansu, Sai hassada ta shiga cikin zukatansu, Shi yasa basu ganin girma da kuma alfarmar Manzon Allah (saww).. Dalilin kenan da yasa Allah ya la'ancesu ya tsine musu. Duk da cewa bakinsu ya furta kalmar Shahada, Kuma suna yin sallah, suna sadaqah in sun ga dama, Amma rashin ganin Alfarmar Annabin ta sa suka zama kafirai. Hasali ma sai sunfi kafiran shan azaba a lahira.

Ya kai 'dan uwa wallahi babu wani abinda zaka samu a lahira sai dai in kaje da "IMANI". Shi kuma Imani ba ya tabbata sai da SON MANZON ALLAH (SAWW) DA YIN BIYAYYA GARESHI. Soyayyar da biyayyar basu tabbata sai kana ganin girmansa da martabarsa..

Acikin rubuce-rubucen da mukeyi a Zauren Fiqhu, sau da yawa idan mun kawo wata maganar da take nuna girman darajar Ma'aiki (saww) sai kaga wani ya shigo yana challenging din Maganar.. kamar wai shi bai yarda ba.. Duk da cewa mukan kawo ingantattun Hadisai ne, da littafin da aka ciro hadisin da lambarsa, da kuma darajar isnadinsa.

Don Allah jama'a ya kamata muyi taka-tsantsan da Harshenmu. Fagen Manzon Allah (saww) ba wajen wasa bane. Allah yana kishinsa. Idan ka kuskura ka munana ladabi gareshi nan take ka kafirta. Kuma shari'a ba zatayi maka uzuri ba. Awajen Allah ma ba zaka samu rangwame ba.

"KACE MUSU SHIN DA ALLAH DA AYOYINSA DA MANZONSA KUKA KASANCE KUNA YIN IZGILI??

"KAR KUYI WANI UZURI! KUN RIGA KUN KAFIRCE, BAYAN IMANINKU...".

Nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP -1. 07064213990 08021141312

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI