SU WANENE MASU ARZIKI??


Ko kun san cewa masu tarin Nairori da Daloli ba sune masu arziki ba, Hakanan Qaton gida ko Babbar Mota duk ba sune alamomin arziki ba.

# Masu arziki sune mutanen da suka shagaltu da kallon laifukan kansu, basu damu da kallon laifukan mutane ba. Sai suka kwadaitu da gyaran zukatansu.. Da kuma mikar da karkatattun halayen Zukatansu, Kuma suka yi. a kansu Hisabi anan duniya tun kafin ayi musu hisabi aranar Alqiyamah.

# MASU ARZIKI sune mutanen da suka fahinci mecece rayuwar duniyar nan, Suka fahimci cewa ita duniya ba gidan zama bane. Gida ne mai shudewa. Don Haka suka ribaci lokutan rayuwarsu cikin aikata abinda Allah yake so.

# MASU ARZIKI Sune masu ambaton Allah atsaye, da kuma azaune ko a kwance akan hakarkarinsu.. Kuma suke yawaita neman gafarar Allah bisa laifukansu, da kuma Takitawarsu acikin lamarin Ubangiji (SWT).

# MASU ARZIKI sune wadanda Hassada ko Kyashi basu samu hanyar shiga cikin zukatansu ba. Idan wani abu mai kama da haka ya bijiro musu, sukan yi kokarin gusar dsshi ds kwantar dashi.

# MASU ARZIKI : Sune wadanda basu sauraro ko furta wata kalma sai ta alkhairi kuma mafi kyau mafi tsarki. Kuma sukan tsaftace kalma kafin su furta.. Kamar yadda ake za'bar Mafiy kyawu acikin 'Ya'yan itace.

# MASU ARZIKI : Sune wadanda suke tafiyar da rayuwarsu bisa tsari irin na Manzon Allah (saww). Kuma suke bin sunnarsa abakinsu kuma a aikace.

# MASU ARZIKI : Sune wadanda suka hakurtar da Zukatansu bisa kyakkyawan tunanin cewa duk abinda ya samesu ba zai taba kubce musu ba, Kuma duk abinda ya kubce musu ba zai taba samunsu ba.

# MASU ARZIKI : Sune wadanda zuciyarsu ta samu nutsuwa da Zikirin Allah, Kuma Ruhinsu yake debe kewa da kusancin Ubangiji.. Shi yasa zaka samesu ko yaushe acikin fsrin ciki koda suna cikin Quncin rayuwa.

Ina rokon Allah ya sanyani daku da dukkan Daliban wannan Zauren Fiqhu mai albarka da iyayenmu da iyalanmu acikin wadannan masu arzikin aduniya da lahira.
Kuma ya azurtamu da samun gidan farin ciki aranar Alqiyamah, Kuma ya bamu yardarsa Matabbaciya. Aaameeen..

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Muna Qara jan hankalin masu kwafar rubutun suna chanzawa cewa DON GIRMAN ALLAH su dena.. Zaka iya latsa "SHARE" ajikin post din ko kuma ka kwafa ka lika awani wajen. Mutukar dai ba zaka cire sunan Zauren Fiqhu (inda ka kwafo Original din).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI