IDAN AKA SANYA BAWA ACIKIN QABARINSA

Yayin da aka sanya bawa acikin Qabarinsa, sai Qabarin yace masa :

"KAICHONKA YA KAI 'DAN ADAM!! WAYE YA RUDEKA DAGA GARENI?

"SHIN BAKA SAN CEWA NINE GIDAN FITINA BA? KUMA (NINE) GIDAN DUHU, KUMA (NINE) GIDAN KADAITAKA, KUMA (NINE) GIDAN TSUTSOTSI!!!"

MENENE YA RU'DAR DAKAI ALHALI KA KASANCE KANA WUCEWA TA KUSA DANI ALOKUTA DA YAWA".

To idan mutumin kirki ne (Mamacin) Sai wani amsawa (Wato Mala'ika) daga cikin Qabarin yace ma Qabarin "Shin yaya kake gani idan ya kasance yana Umurni da aikin alkhairi, kuma yana hani daga Mummuna?".

Sai Qabarin yace "TO IN DAI HAKA NE, TO LALLAI NI ZAN ZAMANTO DAUSAYI NE GARESHI.. KUMA JIKINSA ZAI KOMA HASKE, KUMA RUHINSA ZAI TAFI ZUWA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI".

# Ibnu Abid Dunya ne ya ruwaito hadisin daga Abul Hajjaj Ath-Thumaliy (ra) daga Manzon Allah (saww).

# Ibnul Munkadir shima ya ruwaito irin wannan daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra).

# Mu'awiyatu bn Salih ma ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-Aas (ra).

Ya Allah kasa Qabarinmu ya zamanto Dausayi ne na aljannah..

Ya Allah kasa Alqur'anin da muka haddace ya zama Hujjah garemu ba Hujjah akanmu ba.

Ya Allah ka kiyaye dukkan daliban Zauren Fiqhu daga sharrin Mummunar cikawa, da mummunar makoma, da mummunan sakamako.

Ya Allah ka bamu kyakkyawan Qarshe. Mu mutu bisa Musulunci da Imani da Ihsani..

Ya Allah ka tashemu aranar Alqiyamah acikin Tawagar Annabawa da Siddiqai da Shaheedai da Waliyyanka Yardaddunka.

Aaameeen Ya Allah ka amsa don tsarkin Mulkinka, don Azaliyyar Ikonka, don wanzuwar Zatinka, don Yalwar Rahamarka.

Daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 (24-01-2016).

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI