Posts

Showing posts from July, 2016

GASKIYA SAHABBAI SUNJI DADINSU!

Hakika Sahabban Manzon Allah (saww) mutane ne wadanda babu irinsu. Sun fi dukkan Mutane daraja. Don banda Annabawa babu wanda yafisu daraja awajen Allah daga cikin mutane. Sun zauna da Annabi (saww) sunso shi, sun bishi, sun taimakeshi da dukiyoyinsu da rayukansu. Sun sayar ma Allah dukiyoyinsu da rayukansu. Shi kuwa ya saya ya biyasu da tukwuicin gidan Aljannah da kuma yardarsa ta har abada. Sun samu lambobin girmamawa daga Allah da Manzonsa (saww). # Shin yaya Sayyiduna Abubakrin yaji acikin zuciyarsa yayin da Manzon Allah (saww) yace masa : "DA ACHE ZAN RIKI BADA'DI ACIKIN MUTANE, TO DA NA RIKI ABUBAKAR AMATSAYIN BADA'DINA". # Shin yaya Sayyiduna Umar Al-Faruk yaji acikin zuciyarsa, alokacin da ya nemi izinin shigowa wajen Manzon Allah (saww) sai yace "KACE MASA YA SHIGO, KUMA KAYI MASA ALBISHIR DA SAMUN ALJANNAH". Kuma yace "ALLAH YA SANYA GASKIYA AKAN HARSHEN UMARU DA ZUCIYARSA". # Shin yaya Uthman Dhun Nurayni yaji azuciyarsa, bayan ya

KU DUBI IRIN WANNAN SOYAYYAR

Bayan an dawo daga Yakin Uhudu, kasancewar shine Yaqi na farko wanda Musulmai da yawa sukayi shahadah, Sai garin Madeena ya cika da kururuwar Mata da Qananan yara. Yayin da Manzon Allah (saww) yaji wasu mata daga dangin Banu Abdil-Ash'hal suna ta rusa kuka saboda mamatansu, Sai hankalinsa ya tashi. Ya tuna da Baffansa wato Sayyiduna Hamzah bn Abdil Muttalib (rta). Sai yace: "SAI DAI KUMA SHI HAMZA BASHI DA MASU YI MASA KUKA". Daga jin wannan Qaulin sai gaba daya Matayen mutanen Madeenah suka taho suka zauna suka fara rusa kuka domjn su taya Manzon Allah (saww) bakin cikin rabuwa da Baffansa. Suna ta kuka cikin dare har Manzon Allah (saww) yayi barci. Yayin da ya farka yaji har yanzu suna tayi, sai yace: "Ya Kaitonsu, har yanzu suna zaune anan? Ku umurcesu su koma (gidajensu) Kuma bayan wannan ranar kar su sake yin kuka bisa wani Mamaci". ADUBA : - ÃLUL BAITI HAULAR RASOOL (shafi na 101). - SUNANU IBNI MAAJAH (hadisi na 1591). Zauren Fiqhu, wannan yana n

ZUWA GA MASOYIN RAINA (SALLAL LAAHU ALAIHI WA AALIHI WA SALLAM)

Amincin Allah ya tabbata agareka gwargwadon matsayinka awajen Ubangijinka Ya Masoyin Allah. Hakika Ni na shaida cewa Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma shi kadai ya chanchanta a bauta masa. Kuma na shaida Kai Bawansa ne kuma Manzonsa ne. Ya aikoka alokacin da dukkan wani hasken shiriya ya riga ya dusashe. Gaskiya tayi Qas, sai Qarya take hankoro. Kazo da haskenka ka kauda dukkan Qarya da ma'abotanta. Ka isar da aiken Allah, Ka karya Gumaka ka tsarkake Bautar Allah. Ka fidda bayi daga Kafirci zuwa ga Imani, daga jahilci zuwa ga Ilimi, daga Zalunci zuwa ga adalci. Hakika na shaida cewa cikin dukkan bayin Allah babu tamkarka babu kamarka. Kai ne Shugaban dukkan bayin Allah. Kai ne Haskensu kuma da kai Allah ya haskakasu. Kai ne Shugaba kuma jagoran dukkan Annabawa da Manzannin Allah. Kuma kai kadai ne wanda saboda kai Allah ya tara dukkan Annabawa da Manzanni sai da sukayi Imani dakai, Suka dauki alkawarin cewa su Mataimakanka ne, zasu taimakeka akan aikinka sanna

KU DUBI WANNAN BAIWA

Image
Sayyiduna Naufal bn Al-Harith bn Abdil-Muttalib (rta)  ya nemi taimako awajen Manzon Allah (saww) alokacin da zai yi aure. (Mahaifinsa yayan Mahaifin Manzon Allah ne). Sai Annabi (saww) ya aura masa wata Mace. Bayan nan sai ya zamanto babu abinda zai ci. Don haka sai Manzon Allah (saww) ya aiki su Abu Rafi'in da Abu Ayyub Al-Ansariy (rta) suka jinginar da wasu kayan Yakinsa awajen wani Bayahude. Suka karbo masa Mudu Talatin na sha'eer. Naufal (rta) yace "Bayan Manzon Allah (saww) ya bani wannan Mudu Talatin na sha'eer din, mun ci gaba da cinsa har tsawon rabin shekara (6 months) sannan da muka aunashi sai muka ganshi kamar yadda yake.  (Wato yana nan daidai kamar ba'a ta'ba ci daga gareshi ba). Da naje na gaya ma Manzon Allah (saww) sai yace mun "DA ACHE BAKA AUNASHI BA, DA SAI YA ISHEKA MUTUKAR KANA RAYE" (Wato da zai isheka kaci har karshen rayuwarka). Imamul Hakim ne ya ruwaito wannan Mu'ujizar acikin MUSTADRAK juzu'i na biyu shafi na 2

ANNABINA SHUGABANA MACECINA (SAWW)

Image
ANNABINA, MASOYINA (SAWW) SHINE : ***************************************** DHU QUWWATIN : Ma'abocin Qarfin jiki da Qarfin Hujjah. Annabin da shi kadai yaci nasarar da sauran Annabawan Allah vasu samu ba. Ya kori shirka,  ya karya gumaka, ya tsarkake Ka'abah. DHU HURMATIN : Ma'abocin alfarma aduniya da lahira. Annabin da saboda shi Allah yake dauke Bala'i, kuma yake saukr da niimah.  Shine wanda saboda alfarmarsa al'ummarsa ta samu daukaka da darajoji. DHU MAKANATIN : Ma'abocin Qurewar Matsayi afadar Allah. Shine wanda Allah ya tara dukkan Annabawa sukayi imani dashi, sukayi masa chaffa, Suka dauki alkawarin taimakonsa wajen isar da sako. DHU 'IZZIN : Ma'abocin Buwaya aduniya da lahira. Shine wanda ya chusa tsoro da razana azukatan Sarakunan duniya tun afarkon lokacin bayyanarsa. DHU FADHLIN : Ma'abocin Falala da fifiko a saman dukkab halittu. Shine wanda ambaton sunansa yake yaye damuwa ga Masoyansa. Kallon fuskarsa yakan Gigita hankali,  Tun

LIKITAN LIKITOCI (SAWW)

Hadisi daga Sayyiduna Hubaibu bn Fuwaik (rta) yace: "Hakika Mahaifina ya tafi wajen Manzon Allah (saww) alhali alokacin nan idanuwansa sunyi fari fat baya ganin komai dasu. (Wato ya riga ya makance). Da Manzon Allah (saww) ya tambayeshi "MENENE YA SAMEKA?". Sai yace "Na kasance ina horar da Rakumina, Sai Qafata ta taka wani Qwai, Sai (ruwansa) ya zuba a idanuwan". Nan take da Annabi (saww) yayi masa tofi acikin idanuwansa sai ya fara gani (Wato ya warke tarwal). Ni na ganshi (shi Mahaifina) yana iya shigar da zare cikin allura, alhali alokacin nan yana ɗan shekaru Tamanin (80) aduniya, Kuma idanuwan nasa suna nan fari fat ɗin". ADUBA : DALA'ILUN NUBUWWAH na Baihaqiy, juzu'i na 6 shafi na 173. Wannan yana nuna mana tsantsar Mu'ujizah irin ta Ma'aikin Allah (saww). Da kuma tausayawarsa ga Sahabbansa (rta). Masu ilimin kiwon lafiyar jikin 'Dan Adam sun tabbatar da cewa dole sai da wannan ɗigon baƙin na cikin idanu sannan mutum zai i

ZAKKAR FIDDA KAI (PART ONE)

Image
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Tsira da aminci su Qara tabbata abisa fiyayyen halittu, Annabi Muhammadu da Iyalan gidansa da dukkan sahabbansa. Kamar yadda muka alkawarta, -INSHA ALLAHU zamu fara ne da kawowa hadisai wadanda suka yi magana akanta, tare da sharhi, sannan kuma daga baya mu leka wajen maluman fiqhu domin muji hukunce-hukuncen da suka fitar daga cikin wadannan hadisan: ★ HADISI NA FARKO: daga IBNU UMAR (rta) yace: "Manzon Allah (saww) ya farlanta zakkar fidda kai, Sa'i daya na dabino, ko Sa'i daya na sha'eer. Abisa kowanne bawa, ko 'da, da namiji ko mace, Qarami da babba daga cikin musulmi. Kuma yayi umurni abayar da ita kafin tafiya sallar (eedi)" (Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi) Wannan hadisin dalili ne akan wajibcin zakkar fidda kai, saboda cewar sa "YA FARLANTA". Domin hakan yana nufin ya lazimta, ya wajibta, Kuma ana fitarwa ne akan yaro da babba, Mace da namiji. Dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan