KU DUBI WANNAN BAIWA
Sayyiduna Naufal bn Al-Harith bn Abdil-Muttalib (rta) ya nemi taimako awajen Manzon Allah (saww) alokacin da zai yi aure. (Mahaifinsa yayan Mahaifin Manzon Allah ne).
Sai Annabi (saww) ya aura masa wata Mace. Bayan nan sai ya zamanto babu abinda zai ci. Don haka sai Manzon Allah (saww) ya aiki su Abu Rafi'in da Abu Ayyub Al-Ansariy (rta) suka jinginar da wasu kayan Yakinsa awajen wani Bayahude. Suka karbo masa Mudu Talatin na sha'eer.
Naufal (rta) yace "Bayan Manzon Allah (saww) ya bani wannan Mudu Talatin na sha'eer din, mun ci gaba da cinsa har tsawon rabin shekara (6 months) sannan da muka aunashi sai muka ganshi kamar yadda yake. (Wato yana nan daidai kamar ba'a ta'ba ci daga gareshi ba).
Da naje na gaya ma Manzon Allah (saww) sai yace mun "DA ACHE BAKA AUNASHI BA, DA SAI YA ISHEKA MUTUKAR KANA RAYE" (Wato da zai isheka kaci har karshen rayuwarka).
Imamul Hakim ne ya ruwaito wannan Mu'ujizar acikin MUSTADRAK juzu'i na biyu shafi na 246. Baihaqiy ma ya ruwaitoshi acikin Dala'ilun Nubuwwah juzu'i na 6 shafi na 114.
Ibnu Katheer ma ya kawo wannan acikin ALBIDAYAH WAN NIHAYAH juzu'i na shida shafi na 119.
Salatin Allah da aminci su tabbata bisa mafi kyawun Halaye da kyawun daidaiton halitta, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa Tsarkaka.
DAGA ZAUREN FIQHU 19-07-2016 (14-10-1437).
Comments
Post a Comment