ZAKKAR FIDDA KAI (PART ONE)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Tsira da aminci su Qara tabbata abisa fiyayyen halittu, Annabi Muhammadu da Iyalan gidansa da dukkan sahabbansa.
Kamar yadda muka alkawarta, -INSHA ALLAHU zamu fara ne da kawowa hadisai wadanda suka yi magana akanta, tare da sharhi, sannan kuma daga baya mu leka wajen maluman fiqhu domin muji hukunce-hukuncen da suka fitar daga cikin wadannan hadisan:
★ HADISI NA FARKO: daga IBNU UMAR (rta) yace: "Manzon Allah (saww) ya farlanta zakkar fidda kai, Sa'i daya na dabino, ko Sa'i daya na sha'eer.
Abisa kowanne bawa, ko 'da, da namiji ko mace, Qarami da babba daga cikin musulmi.
Kuma yayi umurni abayar da ita kafin tafiya sallar (eedi)"
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi)
Wannan hadisin dalili ne akan wajibcin zakkar fidda kai, saboda cewar sa "YA FARLANTA". Domin hakan yana nufin ya lazimta, ya wajibta, Kuma ana fitarwa ne akan yaro da babba, Mace da namiji.
Dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan cewar. Zakkar fidda kai WAJIBA CE.
-Imamu Malik da Imamush-shafi'iy da kuma jam'huurin Fuqaha'u sunce FARILLA ce. domin su awajensu da wajibi da farilla duk abu guda ne.
IMAM ABU HANIFAH yace wajiba ce amma ba farilla, saboda shi awajensa farilla tafi wajibi Qarfi.
Kuma da wannan hadisin ne suka kafa hujjar cewar za'a fitarwa Qaramin yaro. da mahaukaci.
MIJI zai fitarwa matarsa da 'ya'yansa da bayinsa (idan yana dasu) da duk wadanda ciyarwarsu take karkashinsa.
Akwai wasu daga cikin SAHABBAI DA TABI'AI kamar Sayyiduna Aliyu bn Abi-Talib da Sa'eed bn Almusayyib, da Hasanul-Basary (Allah shi kara musu yarda) wadanda suke ganin cewar ana yin fidda kai ne kawai abisa wanda Sallah da Azumi suka hau kansu. Wato banda kananan yara da jarirai.
Suna kafa hujjah ne da hadisin nan wanda IBNU ABBAS ma ya ruwaito tamkarsa inda yake cewa:
"Manzon Allah (saww) ya farlanta mana zakkar fidda kai domin ta zama tsarkakewa ga mai azumi daga laifukan (da ya aikata acikin azuminsa kamar) lagawu (wasa) da kuma sha'awa.
Kuma domin ta zama ciyarwa ne ga miskinai.
Duk wanda ya fitar da ita kafin sallah, to hakika wannan zakkah ce karbabbiya. amma wanda bai fitar ba sai bayan sallah, to wannan ta zama kamar sadaqa ne daga sadaqoqi.
(Abu dawud da Ibnu Majah da Hakim ne suka ruwaito shi)
Kuma da wannan hadisan ne ake kafa hujjar lokacin da yafi dacewa afitar da ita wannan zakkar.
WALLAHU A'ALAM.
Sai mun hadu a kashi na biyu.
Comments
Post a Comment