GASKIYA SAHABBAI SUNJI DADINSU!

Hakika Sahabban Manzon Allah (saww) mutane ne wadanda babu irinsu. Sun fi dukkan Mutane daraja. Don banda Annabawa babu wanda yafisu daraja awajen Allah daga cikin mutane.

Sun zauna da Annabi (saww) sunso shi, sun bishi, sun taimakeshi da dukiyoyinsu da rayukansu. Sun sayar ma Allah dukiyoyinsu da rayukansu. Shi kuwa ya saya ya biyasu da tukwuicin gidan Aljannah da kuma yardarsa ta har abada.

Sun samu lambobin girmamawa daga Allah da Manzonsa (saww).

# Shin yaya Sayyiduna Abubakrin yaji acikin zuciyarsa yayin da Manzon Allah (saww) yace masa : "DA ACHE ZAN RIKI BADA'DI ACIKIN MUTANE, TO DA NA RIKI ABUBAKAR AMATSAYIN BADA'DINA".

# Shin yaya Sayyiduna Umar Al-Faruk yaji acikin zuciyarsa, alokacin da ya nemi izinin shigowa wajen Manzon Allah (saww) sai yace "KACE MASA YA SHIGO, KUMA KAYI MASA ALBISHIR DA SAMUN ALJANNAH".

Kuma yace "ALLAH YA SANYA GASKIYA AKAN HARSHEN UMARU DA ZUCIYARSA".

# Shin yaya Uthman Dhun Nurayni yaji azuciyarsa, bayan ya dauki nauyin rundunar yaqin Tabuka, Kuma Manzon Allah (saww) yace "DAGA YAU DUK ABINDA UTHMANU YA AIKATA BA ZAI CHUCHESHI BA (BABU BABU ABINDA ZAI HANASHI SHIGA ALJANNAH)".

# Shin yaya Sayyiduna Aliyyu bn Abi Talib (rta) yaji azuciyarsa, lokacin da za'a tafi Yaqin Khaybara Manzon Allah (saww) yasa akayi masa wata Tuta ta musamman sannan yace "HAKIKA GOBE ZAN BAYAR DA WANNAN TUTAR GA WANI MUTUM WANDA YAKE SON ALLAH DA MANZONSA, KUMA ALLAH DA MANZONSA MA SUKE SONSA"

Sahabbai da dama sun nuna kwadayinsu ga wannan tutar amma ba'a basu ba.. Sai aka bama Imamu Aliy bn Abi Talib (Allah shi yarda dasu baki daya).

#Shin yaya yaji azuciyarsa lokacin da Manzon Allah (saww) yake addu'a agareshi yana cewa:

"YA ALLAH NI INA SON ALIY. YA ALLAH KASO DUK MAI SONSHI. KUMA KAQI DUK MAI QINSA"

# Shin yaya Sayyiduna Mu'azu bn Jabal yaji azuciyarsa lokacin da Manzon Allah (saww) yace masa "WALLAHI NI INA SONKA YA MU'ADH!!".

# Shin yaya Sayyiduna Abdullahi bn Abbas yaji azuciyarsa yayin da Manzon Allah (saww) ya dora hannunsa mai albarka akansa, sannan yayi masa addu'a yana cewa : "YA ALLAH KA SANAR DASHI FASSARA, KUMA KA FAHIMTAR DASHI ACIKIN ADDINI".

# Shin yaya Sayyiduna Sa'adu bn Abi Waqqaas (ra) yaji azuciyarsa aranar Yaqin Uhudu, yayin da ya dauki Kibiya yana harbin kafirai, agefensa kuma ga Shugaban Halitta (saww) yana ce masa "HARBESU YA SA'ADU!! MAHAIFINA DA MAHAIFIYATA FANSA NE AGAREKA!".

# Shin yaya Hassanu bn Thabit (ra) yaji azuciyarsa lokacin da ya mike tsaye zai rama irin Waqar zagin da kafirai sukayi ma Musulunci, sai Shugaba (saww) yace masa "CI GABA YA HASSAANU, WALLAHI NA RANTSE DA ALLAH, WAQAR NAN TAKA TAFI ZAFI AKANSU FIYE DA SAUKAR KIBIYA. KUMA ALLAH YANA KARFAFARKA DA RUHU MAI TSARKI".

# Shin yaya Sayyiduna Ka'abu bn Zuhayr (ra) yaji alokacin yazo yana yabon Ma'aiki (saww) sai Ma'aikin (saww) ya cire bargonsa mai albarka ya Mika masa!!

# Shin yaya Sayyiduna 'Ubayyu bn Ka'ab (ra) yaji alokacin da Ma'aiki (saww) yace masa "HAKIKA ALLAH YA UMURCENI CEWA IN ZO IN KARANTA MAKA WANNAN SURAR (Suratul Bayyinah) "

# Shin yaya Sayyiduna Saa'ibu bn Yazeed (ra) yaji acikin zuciyarsa yayin da Manzon Allah (saww) ya dora hannunsa mai daraja akansa, Sai da yayi shekaru masu yawa bai mutu ba. Kuma dukkan gashin kansa sunyi furfura amma banda wajen da Tafin Hannun Ma'aiki (saww) ya shafa.

# Shin yaya Sayyiduna Julaybeeb (ra) yaji azuciyarsa lokacin da Manzon Allah (saww) yace masa "KAI DAGA GARENI KAKE, NIMA DAGA KAI NAKE!!".

# Shin yaya Nana Fatima (amincin Allah gareta da Mahaifinta) taji azuciyarta yayin da Mahaifinta ya gaya mata cewa : "ALLAH YA TURO WANI MALA'IKA YAYI MUN ALBISHIR CEWA KE CE SHUGABAR MATAYEN HALITTU BAKI DAYA".

#Shin yaya Iyalan Manzon Allah (saww) suka ji, yayin da ya lullubesu da bargonsa mai daraja, yana cewa : "YA ALLAH WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA, TO KA TAFIYAR DA DAU'DA DAGA GARESU KUMA KA TSARKAKESU MUTUKAR TSARKAKEWA".

# Shin yaya Mutanen Madeena (AL-ANSAAR) suka ji Azukatansu yayin da Ma'aiki (saww) yake cewa "ALAMAR IMANI SHINE SON MUTANEN MADINA.. KUMA ALAMAR MUNAFURCI SHINE QIN MUTANEN MADINA".

# Shin yaya Sahabbai dukkaninsu sukaji, yayin da suka rayu tare da Ma'aiki (saww).. Suna kallonsa yana kallonsu kullum kullum, safiya da maraice...

# Shin yaya suka ji yayin da suka saurari Karatunsa??

# Shin yaya sukeji idan sun saurari Muryarsa alokacin da yake musu Khutuba!?

# Shin yaya sukeji idan ya kallesu da murmushin nan nasa!!?

# Shin yaya sukeji idan sun gaisa dashi, ya gaisa dasu!!?

# Shin yaya suka ji ARANAR DA YA BAR DUNIYAR NAN!!!??? 󾌺󾌺󾌺

LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULULLAH!!!!

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Nakanji Zuciyata kamar zata fashe idan na tuna cewa banyi zamani dashi ba, Ban ganshi azahiri ba... Banji muryarsa afili ba..

Mai yasa Zamani ya dakatar dani ban riskeshi ba!!

Amma duk da haka na gode ma Allah da bai sanyani cikin makiyansa ba...

Ya Allah kayi salati da tasleemi da albarka da rahama da ni'ima agareshi da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa, albarkacin wannan Salatin ka Qara mana soyayyarsa da Qarfin riko da Sahihiyar Sunnarsa da Koyi da halayensa.

An gudanar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (5) ranar Juma'a 18-12-2015.

Don Girman Allah masu kwafa suna chanzawa su dena.

https://mobile.facebook.com/zaurenfiqhu/?refid=52&_ft_=top_level_post_id.1685806454771769%3Atl_objid.1685806454771769%3Apage_id.261230340562728%3Athid.261230340562728&__tn__=C-R

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI