KU DUBI IRIN WANNAN SOYAYYAR

Bayan an dawo daga Yakin Uhudu, kasancewar shine Yaqi na farko wanda Musulmai da yawa sukayi shahadah, Sai garin Madeena ya cika da kururuwar Mata da Qananan yara.

Yayin da Manzon Allah (saww) yaji wasu mata daga dangin Banu Abdil-Ash'hal suna ta rusa kuka saboda mamatansu, Sai hankalinsa ya tashi. Ya tuna da Baffansa wato Sayyiduna Hamzah bn Abdil Muttalib (rta).

Sai yace: "SAI DAI KUMA SHI HAMZA BASHI DA MASU YI MASA KUKA".

Daga jin wannan Qaulin sai gaba daya Matayen mutanen Madeenah suka taho suka zauna suka fara rusa kuka domjn su taya Manzon Allah (saww) bakin cikin rabuwa da Baffansa.

Suna ta kuka cikin dare har Manzon Allah (saww) yayi barci. Yayin da ya farka yaji har yanzu suna tayi, sai yace:

"Ya Kaitonsu, har yanzu suna zaune anan? Ku umurcesu su koma (gidajensu) Kuma bayan wannan ranar kar su sake yin kuka bisa wani Mamaci".

ADUBA :

- ÃLUL BAITI HAULAR RASOOL (shafi na 101).

- SUNANU IBNI MAAJAH (hadisi na 1591).

Zauren Fiqhu, wannan yana nuna mana Khususiyyah ce ta Manzon Allah (saww) wanda Allah ya kebanceshi dashi akan baffansa.

Kuma Qissar tana karantar damu irin girman soyayyar da Mutanen Madeenah suke yiwa Manzon Allah (saww). Domin gashi sun manta da, nasu bakin cikin saboda abinda ya shafi bangaren baffan Manzon Allah (saww).

Ya Allah ka Qara salati da girma da aminci da aminci bisa Shugaban masu Jihadi, Jagoran Jagorori, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa Jaruman fama.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP -1 (27-07-2016) 22-10-1437.

Kaifa Asbahtum?

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI