ZUWA GA MASOYIN RAINA (SALLAL LAAHU ALAIHI WA AALIHI WA SALLAM)

Amincin Allah ya tabbata agareka gwargwadon matsayinka awajen Ubangijinka Ya Masoyin Allah.

Hakika Ni na shaida cewa Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma shi kadai ya chanchanta a bauta masa. Kuma na shaida Kai Bawansa ne kuma Manzonsa ne.

Ya aikoka alokacin da dukkan wani hasken shiriya ya riga ya dusashe. Gaskiya tayi Qas, sai Qarya take hankoro.

Kazo da haskenka ka kauda dukkan Qarya da ma'abotanta. Ka isar da aiken Allah, Ka karya Gumaka ka tsarkake Bautar Allah. Ka fidda bayi daga Kafirci zuwa ga Imani, daga jahilci zuwa ga Ilimi, daga Zalunci zuwa ga adalci.

Hakika na shaida cewa cikin dukkan bayin Allah babu tamkarka babu kamarka. Kai ne Shugaban dukkan bayin Allah. Kai ne Haskensu kuma da kai Allah ya haskakasu.

Kai ne Shugaba kuma jagoran dukkan Annabawa da Manzannin Allah. Kuma kai kadai ne wanda saboda kai Allah ya tara dukkan Annabawa da Manzanni sai da sukayi Imani dakai, Suka dauki alkawarin cewa su Mataimakanka ne, zasu taimakeka akan aikinka sannan ya karbi alkawarinsu ya basu Manzanci.

Kai ne wanda ka hau Buraqah acikin dare kayi tafiyar da tun farkon duniya har Qarshenta ba'a samu wanda yayi irinta ba.

Acikin dare guda kaje Baitul Maqdis ka jagoranci dukkan Annabawa kayi Musu sallah bisa addinin Kakanka (alaihis salam). Sannan ka mike kayi kirari agaban dukkan Annabawa da Manzanni. Jibreelu yayi chaffa dakai, hakanan dukkan wadanda suke wajen sai da sukayi maka chaffa.

Ka keta dukkan Sammai Jibreelu yana yi maka Zaggi, Mala'iku sukayi Sahu-sahu kayi musu sallah. Baka gushe kana ratsawa kana lulawa ba, tun daga Sama ta farko har sama ta bakwai, Har zuwa Magaryar Tikewa (Sidratul Muntaha). Har zuwa "QABA-QAUSAINI AI ADNA".

Kututturen dabino yayi nishi don shauqin rabuwa dakai na 'Yan kwanaki, to yaya mu zamuyi kenan. Mu da bamu ta'ba ganinka ba, bamu ta'ba jin Qamshin nan na jikinka ba, Bamu taba jin taushin nan na tafin hannunka ba!!

Mu muka fi dacewa da yin kuka da gigicewa don shaukin rashin ganinka Ya Ma'aikin Allah!

Salatin Allah da amincinsa su tabbata agareka da ahalin gidanka Gwargwadon adadin fitowar rana da faduwarta, da adadin dukkan abinda haskenta ke haskawa, da adadin Motsi da numfashin dukkan abinda Allah ya halitta, tun daga farkon faruwar halitta har Qarshenta.

Albarkacin hasken Salatin nan Ya Allah ka dawwamar damu bisa hasken shiriya, Ka Bamu Sirrin soyayyarsa mafi girma, mafi nauyi, Ka kusantamu dashi, Ka Qara mana karfin riko da Alqur'ani da sunnarsa (saww).

MAI ZAUREN FIQHU (07064213990) 24-07-2016 (19-10-1437).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI