LIKITAN LIKITOCI (SAWW)

Hadisi daga Sayyiduna Hubaibu bn Fuwaik (rta) yace:

"Hakika Mahaifina ya tafi wajen Manzon Allah (saww) alhali alokacin nan idanuwansa sunyi fari fat baya ganin komai dasu. (Wato ya riga ya makance).

Da Manzon Allah (saww) ya tambayeshi "MENENE YA SAMEKA?". Sai yace "Na kasance ina horar da Rakumina, Sai Qafata ta taka wani Qwai, Sai (ruwansa) ya zuba a idanuwan".

Nan take da Annabi (saww) yayi masa tofi acikin idanuwansa sai ya fara gani (Wato ya warke tarwal).

Ni na ganshi (shi Mahaifina) yana iya shigar da zare cikin allura, alhali alokacin nan yana ɗan shekaru Tamanin (80) aduniya, Kuma idanuwan nasa suna nan fari fat ɗin".

ADUBA : DALA'ILUN NUBUWWAH na Baihaqiy, juzu'i na 6 shafi na 173.

Wannan yana nuna mana tsantsar Mu'ujizah irin ta Ma'aikin Allah (saww). Da kuma tausayawarsa ga Sahabbansa (rta).

Masu ilimin kiwon lafiyar jikin 'Dan Adam sun tabbatar da cewa dole sai da wannan ɗigon baƙin na cikin idanu sannan mutum zai iya ganin abu.

Amma ga Likitan Likitoci (saww) yayi tofi acikin farin idanu, kuma ana gani dashi Tarwal ba tare da kwayar bakin ba!.

Ya Allahu yi salati da amincinka gareshi da iyalan gidansa da Sahabbansa gwargwadon Matsayinsa awajenka.

'Yan uwa barkanmu da Safiya, Daga Zauren Fiqhu Whatsapp -1. 06-10-1437  (11- July 2016)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI