Posts

Showing posts from 2017

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (02).

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Ya Allah yi salati da aminci mafi wanzuwa bisa Babban Masoyin nan naka wanda babu kamarsa. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa amintattu, da Sahabbansa masu daraja. Daliban Zauren Fiqhu, wannan shine darasi na biyu acikin Maudhu'in da muke bayani akan Halaye ko kuma dabi'un magabata na kwarai dangane da yadda tsoron azabar Allah ako yaushe. Duk da cewar su din mutane ne masu mutukar Son Allah da Manzonsa da kuma tsayawa akan ibadah dare da rana. Kuma muna fadin halayensu ne domin muji muyi amfani dashi, mu kwaikwayesu gwargwadon ikonmu. Yazeed bn Hushib (rah) yace: "Ban taba ganin mutane masu tsananin tsoron Allah kamar Hasanul Basariy da kuma Umar bn Abdil-Azeez ba. Saboda tsananin tsoron azabar Allah, kai kace dominsu kadai aka halicci Wutar!". Shi dai Umar bn Abdil-Azeez yana daga cikin Banu Umayyah. Kuma tun daga ranar da ya karbi Khalifancin daular Musulunci bai taba kwanciya yayi barcin dare akan katifarsa ba. Ya

RANAR DA YABAR DUNIYA (2)

RANAR DA YA BAR DUNIYA (2) ******************************* Sayyiduna Anas bn Malik (ra) ya ruwaito cewa "Yayin da Annabi (saww) jinyarsa tayi nauyi, ya kasance Zafin ciwo yakan lullubeshi. Sai Nana Fatimah (as) tace "WAYYO WAHALAR BABANA!!". Sai Annabi (saww) yace mata "BAYAN YAU DIN NAN BABU SAURAN WATA WAHALA AKAN BABANKI". Yayin da Annabi (saww) ya rasu, sai Nana Fatimah tace "Wayyo Mahaifina! Ya amsa kiran Ubangijin da ya kirashi!... Wayyo Mahaifina! Aljannar Firdausi ce Masaukinsa. Wayyo Mahaifina, Zuwa ga Mala'ika Jibreelu muke mika Ta'aziyyarsa!". Yayin da aka binneshi kuma sai Nana Fatimah tace ma Sahabbai "Shin Zukatanku sunyi muku da'di yayin da kuka Watsa Qasa bisa Manzon Allah (saww) ?". Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi. Allahu Akbar!!! Nana Fatimah muna yi miki Ta'aziyyar Abbanki wanda babu Musibar da tafi rashinsa girma akan Mumini mai cikakken imani. Tunda ake rasuwa ba'a ta'ba yin irin tasa ba

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) - 1

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 1 ************************************* Yana daga cikin Khasa'isu na Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa Allah ya sanya soyayyarsa azukatan halittu masu motsi har ma marassa motsi. Mun kawo muku Qissar duwatsun dake yin gaisuwa gareshi tun tasowarsa agarin Makkah. Kuma mun gaya muku labarin wani dutsen dake gaisheshi bayan an fara yi masa wahayi. Sannan mun gaya muku Qissar da aka ruwaito daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (rta) game da duwatsu da bishiyoyin dake yin gaisuwa ga Manzon Allah (saww). Daga cikin duwatsun duniya wadanda soyayyarsu ga Manzon Allah (saww) ta bayyana Qarara afili, dutsen Uhudu yana kan gaba.. Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya hau kan Dutsen Uhudu tare da Abubakar da Umar da Uthman (Radhiyallahu anhum). Sai dutsen yayi girgiza dasu (Saboda Shauqin jin tafin Qafar Manzon Allah akansa). Sai Manzon Allah (saww) ya bugeshi da Qafarsa mai

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 2

DUWATSUN DAKE SONSHI (SAWW) 2 ************************************* Babban Malamin Hadisin nan a Mazhabin Malikiyyah, wato Alqadhiy 'Iyadh ya ruwaito acikin ASH-SHIFA cewa : Manzon Allah (saww) ya hau kan dutsen Thabeer Lokacin da Kafirai suke nemansa zasu kasheshi. Sai dutsen yayi magana dashi yace masa "Sauka Ya Rasulallahi. Domin ni ina tsoron kada su kasheka akan bayana, Kuma Allah yayi mun azaba". Shi kuma Dutsen Hira'u yace "Taho gareni Ya Ma'aikin Allah". Dutsen Thabeer da Dutsen Hira'u makobtan juna ne. Suna daura da juna, amma akwai wani kwari atsakaninsu. ADUBA ANWARUL MUHAMMADIYYAH ta Shaikh Yusufun Nabhaniy (rah) akan shafi na 275. Kunji fa yadda duwatsu suke gasar nuna kishinsu da soyayyarsu gareshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kaima kayi hankali da zuciyarka kada ta rudeka ka rika jin Qaikayi azuciyarka idan kaji ambatonsa.. Domin hakika Imani ba ya tabbata sai da Tsantsar Soyayyar Annabi Muhammadu (sallal Lahu alai

ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017)

ZIKIRINMU NA YAU (25/10/2017) ********************************* Hadithi daga Ɗalqu bn Habeeb yace "Wani mutum yazo wajen Abud Darda'i (rta) yace masa "Ya kai Abud Darda'i! Hakika gidanka ya Qone!". Sai Abud Darda'i yace "A'a bai Qone ba! Allah ba zai ta'ba yin haka ba, saboda wasu kalmomi da najisu daga wajen Manzon Allah (saww). Duk wanda ya fa'desu a farkon wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya yammanta. Kuma duk wanda ya fa'desu a Qarshen wuni, babu wata musibar da zata sameshi har sai ya wayi gari : اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت ، عليك توكلت وأنت رب العرش العظيم.  ما شاء الله كان وما لم يشأ لم يكن ، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم، أعلم أن الله على كل شيء قدير و أن الله  قد أحاط بكل شيء علما ، اللهم إني أعوذ بك من شر نفسي و من شر كل دابة ربي آخذ بناصيتها، إن ربي على صراط مستقيم >> Allahumma anta Rabbee la ilaha illa anta, 'Alaika tawakkaltu wa anta rabbul 'arshil 'azeem. Ma sha Allah kana wa

SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW)

SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW). ************************************* SON ANNABI (saww) wani hali ne ko dabi'a wanda babu irinsa duk acikin halayen da 'Dan Adam zai iya siffantuwa dasu. Zuciyar da aka tarbiyyantar da ita bisa son Annabi (saww) takan Mance da duk wani abinda ba SHI ba. Kuma bata iya yin wani abu sai cikin koyi dashi. Zuciyar da ta riga ta gaurayu da SON ANNABI (saww) ta kan kasance batta ji, batta gani sai da SHI. Kuma bata yin kowacce Mu'amalar da zata nisantar da ita daga gareshi. Har ta kan kai matsayin yadda ba zata rayu ba, sai da Tunaninsa (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam). MISALI : daga cikin Sahabbai akwai THAWBAAN (rta) wanda ya kasance ba ya iya jin dadi arayuwarsa, har sai yazo ya kalli Manzon Allah (saww). Tsawon dare (Awa 12) yayi yawa agareshi. Ba zai iya daurewa har gari ya waye bai ga Annabi ba (saww). Thawbaanu yakan kasa yin barci cikin dare, har sai yazo ya kalli gidan da Manzon Allah (saww) yake ciki. * Sayyiduna KHALID BN WAL

BABBAN TASHIN HANKALI

BABBAN TASHIN HANKALI!!! ***************************** Hadisi ne zan karanta muku daga Zauren Fiqhu Amma ina neman alfarma guda 'daya awajenku kafin ku karanta hadisin nan... Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau. Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya. Yazeedur Raqqaashiy ya karbo hadisin daga Anas bn Malik (ra) yana cewa: Watarana Mala'ika Jibreelu (as) yazo wajen Manzon Allah (saww) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa ya chanza. Sai Manzon Allah (saww) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CHANJA HAKA?". Yace "Ya Muhammadu (saww) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta. Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Qabari gaskiya ce, ku

YA KAI MAI NEMAN KUSANCI

Idan kaga mutane sun nuna wadatuwarsu da duniya, kai kuma sai ka wadatu da Allah. Idan kuma kaga suna nuna farin cikinsu da duniya, To kai kuma kayi farin ciki da Allah. Idan kaga mutane suna debe kewarsu da duniya, kai kuma ka sanya debe kewarka (wato samun nutsuwarka) da Allah. Idan kaga mutane suna neman shiga wajen Sarakunansu da manyansu, suna neman kusanci dasu domin su samu Girma da daukaka, to kai kuma ka nemi kusanci da Allah da kuma Soyayyarsa ta wannan hanyar zaka samu Mutukar girma da daukaka. NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990) - (31-01-2017).