WASIYYAR LUQMAN ALHAKEEM (01)
Luqman (Allah shi Qara masa yarda) wani Salihin bawa ne baqar fata wanda Allah yayi masa arzikin harshe mai fasaha da hikimomi tare da samun hanyoyin warware mishkilolin al'ummah. Koda acikin Alqur'ani akwai surah guda wacce Allah ya kawo labarin Luqman da irin hikimominsa, har ma ana kiran surar da "SURATU LUQMAN". To yanzu in sha Allah zamu kawo wasu daga cikin irin hikimominsa kamar yadda suka zo a litattafan manyan Maluman Musulunci domin mu amfana da alkhairin dake cikinsu. Watarana Luqman yace ma 'dansa "Ya Kai 'dana! Kada ka aiki Jahili anatsayin 'dan aikenka. Idan har baka samu mai hikima wanda zaka aika ba, to gara ka zamanto 'dan aiken kanka. Ya kai 'Dana! ka nisanci yin Qarya. Domin hakika ita Qarya tana da zaqi abakin mutane kamar yadda naman tsuntsu yake, amma sai dai Ma'abocinta bai cika samun tsira daga gubarta ba. Ya kai 'dana! Ka rika ziyartar wajen Janazah, amma kada ka yawaita ziyartar wajen bukunkuna. Domin kuw