MU SAN ANNABINMU (06)

KOMAWARSA HANNUN KAKANSA MAI DARAJA (SAWW)  :

Daga nan sai ya koma hannun Kakansa wato mahaifin mahaifinsa, mai suna Abdul Muttalibi 'dan Hashim. Ya kasance mai nuna so da Qauna ga wannan jikan nasa mai daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Ya kasance duk inda zai je tare suke tafiya, ba ya yin barci sai tare dashi, hakanan wajen cin abinci ma. Kuma yasoshi fiye da sauran jikanunsa da 'ya'yansa.

Ya kasance yana girmama Annabi (saww) kuma yana gaya ma mutane cewa "Akwai wani babban lamari da zai faru ga jikan nan nawa".

Sai dai zamansu bai tsawaita ba, domin bayan shekaru biyu kachal sai shima ya rasu,  Kuma yabar wasiyyah ga 'daya daga cikin 'ya'yansa mai suna "Abu Talib" cewa shi zai ci gaba da kulawa da wannan jikan nasa, Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Salati da amincin Allah si tabbata bisa Annabin Rahma Ma'abocin tausayi da karamci, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da mabiyansa da dukkan mutanen kwarai.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (03/11/2048 26/02/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI