MU SAN ANNABINMU (05)

RASUWAR MAHAIFIYARSA MAI GIRMA (SAWW) :

Bayan Mala'ikun nan sun kwantar dashi sun tsaga kirjinsa, sai Halimatus Sa'adiyyah ta dawo dashi wajen mahaifiyarsa saboda jin tsoron da takeyi bisa lafiyarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Bayan dawowarsa wajen Mahaifiyarsa da shekaru biyu wato lokacin yana da shekara shida kenan aduniya, sai tayi nufin ta ziyarci garin Yathrib (Madeenah) wajen kawunnanta Banun Najjar, da kuma Qabarin mijinta Abdullahi.

Ta tafi tare da Manzon Allah (saww) tayi wadannan ziyarori, amma akan hanyarta ta dawowa sai jinyar ajali ta kamata, kuma ta rasu adaidai wani waje da ake kira "ABWA'U" kuma anan aka binneta, Qabarinta yana nan har yanzun nan.

Shikenan Manzon Allah (saww) ya zamanto cikakken maraya ta bangaren mahaifansa baki daya. To alokacin nan akwai baiwar mahaifinsa wacce ake kiranta "Ummu Aymana - Barakatul Habashiyyah" ita ta kamo hannunsa suka dawo garin Makkah,  kuma shekarunsa shida awannan lokacin.

ALLAHU AKBAR! Ya Allah kayi salati bisa Annabinka Shugaban mutanen farko dana Qarshe. Ka sanya iyalan gidansa da dukkan zuriyarsa da Sahabbansa baki daya da dukkan Salihan bayinka tare damu baki daya. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (03/11/2018  26/02/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI