WASIYYAR LUQMAN ALHAKEEM (01)
Luqman (Allah shi Qara masa yarda) wani Salihin bawa ne baqar fata wanda Allah yayi masa arzikin harshe mai fasaha da hikimomi tare da samun hanyoyin warware mishkilolin al'ummah.
Koda acikin Alqur'ani akwai surah guda wacce Allah ya kawo labarin Luqman da irin hikimominsa, har ma ana kiran surar da "SURATU LUQMAN".
To yanzu in sha Allah zamu kawo wasu daga cikin irin hikimominsa kamar yadda suka zo a litattafan manyan Maluman Musulunci domin mu amfana da alkhairin dake cikinsu.
Watarana Luqman yace ma 'dansa "Ya Kai 'dana! Kada ka aiki Jahili anatsayin 'dan aikenka. Idan har baka samu mai hikima wanda zaka aika ba, to gara ka zamanto 'dan aiken kanka.
Ya kai 'Dana! ka nisanci yin Qarya. Domin hakika ita Qarya tana da zaqi abakin mutane kamar yadda naman tsuntsu yake, amma sai dai Ma'abocinta bai cika samun tsira daga gubarta ba.
Ya kai 'dana! Ka rika ziyartar wajen Janazah, amma kada ka yawaita ziyartar wajen bukunkuna. Domin kuwa kamar yadda zuwanka wajen janazah ke tunasar dakai lahirarka to hakanan ziyartar wajen bukunkuna ke Qara maka sha'awar zaman duniya..
Ya kai 'dana! Kada ka rika cin abinci bayan ka Qoshi akan Qoshi. Domin hakika ka jefa ma kare abinci yafi alkhairi fiye da sanyashi acikin cikinka bayan Qoshi.
Ya kai 'Dana kada ka kasance mai zaqi sai mutane su hadiyeka. Kuma kada ka zamanto mai 'daci sai su furzar dakai..".
"Ya kai 'dana!! Hakika ni na dauki duwatsu da Qarfe da duk wani abu mai nauyi amma ban dauki abu mafi nauyi kamar mummunan makobci ba.
Ya kai 'dana!! Hakika na dandana duk wani abu mai 'daci amma ban ta'ba dandanar abinda yafi talauci 'daci ba (Allah shi kiyayemu).
"Ya kai 'dana!! Hakika ita duniya tamkar wani kogi ne mai zurfi wanda ya hallakar da mutane masu yawa sosai. To lallai ka sanya Tsoron Allah ya zamto shine jirgin ruwanka acikinta. Imaninka da Allah kuma shine Kayan cikin jirgin. Dogaronka ga Allah kuma shine abun tukin jirgin. Watakil in kayi sa'a ka samu tsallakewa. Amma ban ga alamar zaka tsira ba".
Hakika wadannan wasiyyoyin na Luqman Alhakeem suna kunshe da abubuwa masu yawa wadanda ba kowa ke iya fahimtarsu kai tsaye ba. Amma idan munyi nazari sosai zamu iya fahimtar daidai gwargwado. Allah yasa mu dace da samun yardarsa ameen.
Anan zamu tsaya sai mun hadu acikin darasi na gaba in sha Allah. Da fatan Allah shi Qara mana ilimi da fahimta da ikhlasi ameen.
ANYI KARATUN NE A ZAUREN FIQHU WHATSAPP 4, RANAR 13/11/2018 (05/06/1440).
Comments
Post a Comment