Posts

DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA QUNSA (003)

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP B ISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salati da amincin Allah su tabbata ga Annabin da aka aikoshi zuwa ga dukkan Halittu baki daya, Shugabanmu Muhammad tare da iyalan gidansa Masu albarka da Sahabbansa yardaddu. Idan daliban Wannan Zauren basu manta ba, acikin wancan karatun namu mun warware wasu mas'aloli dangane da sha'anin duniyar aljanu. Munyi bayani akan wuraren zamansu da kamanninsu da kuma abincinsu kamar yadda Ayoyin Alqur'ani Mai Girma da kuma Sahihan hadisai suka tabbatar. Yanzu kuma zamu dora daga inda muka tsaya in sha Allahu. S H AITAN YANA DA QAHO *************************** Tabbas lallai shaitan yana da Qaho akansa. Kamar yadda wasu da dama daga cikin Shaitanun Aljanu su ma suna dashi. Akwai hadisi wanda yake tabbatar da hakan. An ruwaitoshi daga Sayyiduna 'Amru bn 'Anbusata (rta) yace Manzon Allah (saww) yace : " HA KIKA ITA RANA TANA FITOWA NE TA TSAKANIN QAHOHUNA BIYU NA WANI SHAITANI, KUMA TANA FA'DUWA NE...

HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW)

HAKKOKIN IYALAN GIDAN ANNABI (SAWW). ********************************************** Da sunan Allah buwayi Gagara-Misali. Wanda yake zabar wanda yaso ya fifitashi da falalarsa, ya kebanceshi da fifikonsa. Dukkan Tsira da aminci da yarda da albarkoki da ni'imomi da rahama su tabbata ga Mabudin dukkan alkhairai, Shugaban Mutanen farko da na karshe, kuma Makullin Zurin Annabta da Manzanci, Masoyinmu, Abincin zukatanmu, Annabi Muhammadu, Tare da iyalan gidansa tsarkaka masu albarka, da dukkan Sahabbansa Shiryayyu. Mun shirya wadannan lakchochi ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP domin warware wasu muhimman batutuwan da suka shafi Iyalan gidan Manzon Allah (saww) tare da yin bayani akansu da falalarsu da kuma hakkokinsu wadanda suka rataya bisa wuyan dukkan Muminai. Sannan in sha Allahu zamu kawo misalai na irin Zurfafawar da wasu suke yi da sunan wai suna son Ahlul baiti (amma basu bin tafarkinsu). Allah ya san ina Qaunar Ahlul Baiti fiye da yadda nake son kaina da iyayena.. Amma ba kom...

ANNABINA RAYAYYE NE ACIKIN QABARINSA

Wadansu mutane sun dauka cewar Manzon Allah (saww) ya riga ya rasu, ya tafi kenan, babu sauran wani hakkinsa akan su. Shi yasa basu damu da Girmamashi ko yawaita salati agareshi ba.. Malam Mai ZAUREN FIQHU ko zaka iya banu Hujjoji gamsassu akan cewa Ma'aiki (saww) yana nan raye acikin Qabarinsa? AMSA ******* Ba haka abin yake ba. Domin kuwa Manzon Allah (saww) yana ji, yana gani, har ma yana ibada acikin Qabarinsa. Kamar yadda Hujjoji zasu bayyana mana akan gaba. 1. Acikin Alqur'ani mai girma Allah ya gaya mana cewa Shaidai (wadanda suka mutu awajen Jihadi) ba mutuwa sukayi ba. suna nan rayayyu acikin Qabarinsu. Alkah yace: "KAR KUYI ZATON CEWA WADANNAN DA AKA KASHESU BISA TAFARKIN ALLAH, SU MATATTU NE. A'A SU RAYAYYU NE ANA CIYAR DASU AWAJEN UBANGIJINSU". Alqadhy Shawkaniy yace: "Acikin Alqur'ani ance mana Shaheedai rayayyu nd har ma ana ciyar dssu awajen Ubangijinsu. to gashi kuma Annabawa da Salihai suna sama dasu awajen daraja. To su yaya matsa...

HIKIMOMI DAGA TASKAR MA'AIKI SAWW (1)

Kalmomi ne jerarru cike da hikimomi da wa'azozi, kumq sun fito daga bakin wanda ba ya fada son rai. Ba ya magana sai da wahayi daga Rabbul Izzati. Ga kadan daga ciki: 1. Manzon Allah (saww) yace: "MUTUM HUDU, HAKKI NE AKAN ALLAH CEWA BA ZAI SHIGAR DASU ALJANNAH BA, KUMA BA ZAI DANDANA MUSU NI'IMOMINTA BA : - MAI KWANKWADAR GIYA. - MAI CIN RIBAA (KUDIN RUWA - INTEREST). - MAI CIN DUKIYAR MARAYA BA TARE DA HAKKI BA. - MAI BIJIRE MA IYAYENSA. (Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin acikin Mustadrak). Wannan hadisin gargadi ne zuwa ga dukkan Musulmi. Idan an ce MAI KWANKWADAR GIYA, ana nufin har masu shan kwaya, da masu shan Weewi, da sauran kayan maye. Domin duk abinda ke bugarwa shima giya ne. MAI CIN RIBAA - Wannan gargadi ne ga masu hulda da bankuna, da masu hulda da kampanonin Inshaura (Insurance companies) da masu huldar kasuwanci da Ma'aikatan Gwamnati. Sai a kiyaye domin shi Allah ba ya mantuwa. kuma yana nan a madatsa zaka je ka iskeshi, Kuma zaka karbi sakam...

SHIN KA TABA ZUBDA HAWAYE SABODA TSORON ALLAH??

Zubar da hawaye saboda tsantsar tsoron Allah yana daga cikin halayen bayin ALLAH na kwarai. Musamman Annabawa, Sahabbai, da waliyyan Allah. Acikin Mutanen da zasu shiga Inuwar al'arshi aranar da babu wata inuwa sai ita, Manzon Allah (saww) ya Qirga har da mutumin da ya tuna Allah shi kadai aboye, har idanunsa suka zubda hawaye. Annabi Dawud (as) ya kasance mutum ne mai yawan zikirin Allah. Har ma Ubangiji ya hore masa duwatsu da Tsuntsaye suna yin Tasbeehi tare dashi. Manzon Allah (saww) yace: "MUTANE SUN KASANCE SUNA ZUWA SUNA GAISAR DA ANNABI DAWUD, SUNA ZATON KAMAR BASHI DA LAFIYA NE.. AMMA BABU KOMAI GARESHI IN BANDA TSORON ALLAH". Wato wannan ya faru ne saboda ramewa da kuma bayyanar alamomin jinya agareshi. amma ba jinya bace.. Tsoron Allah ne yayi ka-ka-gida azuciyarsa. Hamran bn A'ayun ya ruwaito cewa Manzon Allah (saww) ya karanta ayoyin nan na cikin Suratul Muzammil wato "Ø¥...

GA SADAQAH JARIYAH GARWMU BAKI DAYA

Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU zan bada ita amatsayin SADAQATUN JARIYATUN. Addu'a ce daga Manzon Allah (saww) wacce anfaninta ba zai Qirgu ba. Duk wanda yake son Allah ya kiyayeshi daga sharrin Munafurci, ko kallon haramun, ko Zina, ko dangogin zinar, ko Sata, ko kuma duk wani mummunan hali, idan yana yin wannan addu'ar tare da ikhlasi In sha Allahu  Ubangiji zai kiyayeshu ba zai aikata ba.. Hakanan duk wanda shaitan ya rinjayeshi yana aikata haka, to idan yana yin wannan addu'ar tare da Ikhlasi Allah zai yaye masa, zai shiryar dashi hanya Madaidaiciya. Gata nan zan rubuto da larabci, sannan in rubuto da boko, sannan in rubuto fassararta in sha Allah. اللهم إني أعوذ بك من شر سمعي, ومن شر بصري, ومن ...

ALBARKACIN MANZON ALLAH (SAWW

Annabi (saww) yana da albarka. Hasali ma shine yafi kowa albarka acikin dukkan halittun Allah. Duk na ani mai albarka daga wajensa ya samu. Abu Juhaifa (ra) yace: "Watarana Manzon Allah (saww) yazo wajenmu da rana sai aka kawo masa ruwa yayi Alwala. Bayan ya idar da alwalar sai Sahabbansa (ra) suka dauki sauran ragowar ruwan suna Shafawa ajikinsu. (Domin neman albarkarsa). Sai Manzon Allah (saww) ya mike yayi sallah raka'a biyu, sandansa yana kusa dashi (amatsayin Sutrah). Bayan ya idar sai yasa aka kawo masa ruwa awani Kofi, ya wanke fuskarsa da hannayensa aciki, sannan ya kurkure bakinsa ya zuba acikin Kofin. Sai ya kira Abu Musal Ash'ary da Kuma Bilal, ya basu wannan ruwan yace musu: "KU ZUBA WANNAN RUWAN AKAN FUSKARKU DA KUMA QIRJINKU" Aduba: * Sahihu Muslim juzu'I na 1 shafi na 360, hadisi na 503. * Sunanul Kubra na Imamun Nisa'iy juzu'I na 1 shafi n...