ALBARKACIN MANZON ALLAH (SAWW


Annabi (saww) yana da albarka. Hasali ma shine yafi kowa albarka acikin dukkan halittun Allah. Duk na ani mai albarka daga wajensa ya samu.

Abu Juhaifa (ra) yace:

"Watarana Manzon Allah (saww) yazo wajenmu da rana sai aka kawo masa ruwa yayi Alwala.

Bayan ya idar da alwalar sai Sahabbansa (ra) suka dauki sauran ragowar ruwan suna Shafawa ajikinsu. (Domin neman albarkarsa).

Sai Manzon Allah (saww) ya mike yayi sallah raka'a biyu, sandansa yana kusa dashi (amatsayin Sutrah).

Bayan ya idar sai yasa aka kawo masa ruwa awani Kofi, ya wanke fuskarsa da hannayensa aciki, sannan ya kurkure bakinsa ya zuba acikin Kofin.

Sai ya kira Abu Musal Ash'ary da Kuma Bilal, ya basu wannan ruwan yace musu:

"KU ZUBA WANNAN RUWAN AKAN FUSKARKU DA KUMA QIRJINKU"

Aduba:

* Sahihu Muslim juzu'I na 1 shafi na 360, hadisi na 503.

* Sunanul Kubra na Imamun Nisa'iy juzu'I na 1 shafi na 126 hadisi na 135.

Musnad na Ahmad bn Hanbal, juzu'I na 31 shafi na 41, hadisi na 18,744.

DARASI
********
Wannan hadisin Hujjah ce mai karfi wacce take tabbatar mana da cewa Manzon Allah (saww) yana da albarka, Sahabbansa ma sun tabbatar da haka. Tunda gashi suna neman albarkarsa.

DUK MALAMIN DA YACE WAI MANZON ALLAH (SAWW) BASHI DA ALBARKA, TO HAKIKA YAYI RIDDA, KUMA JININSA YA HALATTA.

Mu dai muna da hujjojinmu masu Qarfi. kuma gasu nan mun bayar.

- Saboda albarkar Manzon Allah, Ubangiji ya riki alkawari daga Annabawa da Manzanni tun kafin ya aikosu.

- Shine wanda Ubangiji ya aikoshi domin RAHAMA ga dukkan halittunsa. Harda Annabawan da Manzannin da Mala'iku baki daya.

Don Allah jama'a ayi hattara. Janibin Shugaban Halitta yafi gaban wasa. Idan ka tabashi Wallahi ba zaka gushe acikin fushin Allah ba. Kuma ba zakayi mutunci agunsa ba.

DAGA ZAUREN FIQHU.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI