GA SADAQAH JARIYAH GARWMU BAKI DAYA

Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU zan bada ita amatsayin SADAQATUN JARIYATUN.

Addu'a ce daga Manzon Allah (saww) wacce anfaninta ba zai Qirgu ba.

Duk wanda yake son Allah ya kiyayeshi daga sharrin Munafurci, ko kallon haramun, ko Zina, ko dangogin zinar, ko Sata, ko kuma duk wani mummunan hali, idan yana yin wannan addu'ar tare da ikhlasi In sha Allahu  Ubangiji zai kiyayeshu ba zai aikata ba..

Hakanan duk wanda shaitan ya rinjayeshi yana aikata haka, to idan yana yin wannan addu'ar tare da Ikhlasi Allah zai yaye masa, zai shiryar dashi hanya Madaidaiciya.

Gata nan zan rubuto da larabci, sannan in rubuto da boko, sannan in rubuto fassararta in sha Allah.

اللهم إني أعوذ بك من شر سمعي, ومن شر
بصري, ومن شر لساني, ومن شر قلبي, ومن شر منيي.

"Allahumma innee a'uzu bika min sharri Sam'ee,  Wa min sharri Basaree, Wa min sharri Lisaanee, Wa min sharri Qalbee, Wa min sharri Maniyyee"

"YA ALLAH INA NEMAN TSARINKA DAGA SHARRIN JI NA, DA SHARRIN GANI NA, DA SHARRIN HARSHENA, DA SHARRIN ZUCIYATA, DA KUMA SHARRIN MANIYYI NA".

- Abu Dawud ne ya ruwaito wannan addu'ar acikin hadisi mai lamba 1,551.
- Imam Tirmiziy ma ya ruwaito akan lambar hadisi na 3,492.
- Imam Nisa'iy kuma akan lambar hadisi na 5,470.
Kuma hadisi ne Sahihi. (Ingantacce).

Wannan addu'ar zatayi mutukar amfani ga matasanmu wadanda suke yawaita Qarya, gulma, hassada, jin kade-kade, kalle kallen batsa, Istimna'i, da sauransu.

ZAUREN FIQHU yayi izini duk wanda ya samu ya tura ma 'yan uwa Musulmi ba tare da chanza komai acikin wannan rubutun ba.

Idan kayi amfani da addu'ar ka samu lada. Idan kuma ka tura ma wani kayi SADAQAH JARIYAH.

BISSALAM DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (4).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI