SHIN KA TABA ZUBDA HAWAYE SABODA TSORON ALLAH??

Zubar da hawaye saboda tsantsar tsoron Allah yana daga cikin halayen bayin ALLAH na kwarai. Musamman Annabawa, Sahabbai, da waliyyan Allah.

Acikin Mutanen da zasu shiga Inuwar al'arshi aranar da babu wata inuwa sai ita, Manzon Allah (saww) ya Qirga har da mutumin da ya tuna Allah shi kadai aboye, har idanunsa suka zubda hawaye.

Annabi Dawud (as) ya kasance mutum ne mai yawan zikirin Allah. Har ma Ubangiji ya hore masa duwatsu da Tsuntsaye suna yin Tasbeehi tare dashi.

Manzon Allah (saww) yace:

"MUTANE SUN KASANCE SUNA ZUWA SUNA GAISAR DA ANNABI DAWUD, SUNA ZATON KAMAR BASHI DA LAFIYA NE.. AMMA BABU KOMAI GARESHI IN BANDA TSORON ALLAH".

Wato wannan ya faru ne saboda ramewa da kuma bayyanar alamomin jinya agareshi. amma ba jinya bace.. Tsoron Allah ne yayi ka-ka-gida azuciyarsa.

Hamran bn A'ayun ya ruwaito cewa Manzon Allah (saww) ya karanta ayoyin nan na cikin Suratul Muzammil wato

"إن لدينا أنكالا وجحيما  وطعاما ذا غصة وعذابا أليما. 

Da ya karantasu nan yayi ta kuka, yana zubda hawayensa mai tsarki har sai da ya suma..

Abdul Azeez bn Abi Rawaad (ra) yace: "Yayin da Allah ya saukar ma Annabinsa ayar nan wacce take cewa: "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI KU TSERATAR DA KANKU DA KUMA IYALANKU DAGA AZABAR WATA IRIN WUTA WACCE MAKAMASHINTA MUTANE NE DA KUMA DUWATSU.

AKANTA (ITA WUTAR) AKWAI WASU MALA'IKU KAURARA MASU TSANANIN QARFI. BASU SA'BA MA ALLAH AKAN ABINDA YA UMURCESU, KUMA SUNA AIKATA ABDUK ABINDA AKA UMURCESU NE".

Manzon Allah (saww) yana cikin karanta ma Sahabbansa wannan ayar sai wani saurayi ya zube Qas ya suma!!! (SUBHANALLAH!!!).

Da Manzon Allah (saww) ya dora hannunsa akan zuciyar yaron sai yaji alamar ransa zai fita ne. Sai ya lakanta masa kalmar Shahada. nan take wannan saurayin ya rasu awajen, sannan aka wankeshi aka sallaceshi!!!

DALIBAN ZAUREN FIQHU kunji fa yadda halayrn magabatanmu yake idan an karanta musu ayah guda!!! Amma shin mu yaya halayenmu yake koda za'a sauke mana Alqur'anin baki dayansa????

Shin tunds kake zuwa wajen tafsiri da azumi sau nawa ka taba ganin wani yayi kururuwa yayi kuka, saboda tsoron Allah?? Sau nawa ka taba ganin Malamin ko mai jan baqin, ko kuma wani daga cikin masu sauraro ya Zube Qasa ya suma???

Shin mu mun samu wani tabbaci ne akan makomarmu ta lahira?? Ko kuwa muna da abinda yafi na magatanmu ne?? Ko mun manta cewar da MIZANI guda za'a auna ayyukanmu ne, damu dasu... kowa awannan mizanin za'a dora aikinsa agaban Zatin Ubangiji.

Ya Allah ka jikanmu ba don halinmu ba..

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI