Posts

ANNABI BAHRUN NADA (SAWW)

ANNABI BAHRUN NADA (SAWW) ********************************* Qaisu bn Nu'uman (ra) yace : Lokacin da Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yake tafiya da Sayyiduna Abubakrin domin yin hijirah, sun wuce ta kusa da wani Bawa yana kiwon dabbobi. Sai suka tambayeshi ki zasu samu Nono su sha?. Sai yace "Babu wata akuya awajena wacce za'a iya tatsa daga gareta, Sai dai ga wata Raquma nan wacce ta dauki ciki tun afarkon hunturu, Kuma riga ta fita. Babu sauran nono gareta". Sai Annabi (saww) yace masa "KIRAWOTA". (Bayan zuwanta) sai Annabi (saww) ya sanya mata dabaibayi, ya shafi hantsarta yayi addu'a har sai da Nonon yazo. Sayyiduna Abubakrin (ra) ya kawo mazubi, Annabi (saww) ya tatsa ya shayar da Abubakrin din. Ya sake tatsa ya shayar da Makiyayin, Sannan ya tatsa yasha. Sai wannan makiyayin yace masa "Don Allah wanene kai? Domin wallahi ban ta'ba ganin tamkarka ba tunda nake". Sai Manzon Allah (saww) yace "SHIN KANA ...

GUZURIN SAFIYA (01)

Ya Ubangiji hakika mun wayi gari muna masu imani da kadaitakarka, da kuma Manzancin Annabinka Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam). Muna cikin masu mika godiya da kirari gareka bisa dukkan ni'imominka na fili da boye.. Hakika bamu isa mu gode maka da irin godiyar da ta chanchanta gareka ba. Muna cikin masu dogaro dakai da kuma neman taimakonka.. Hakika Kaine Fiyayyen Majibinci, Fiyayyen Mataimaki, Kuma fiyayyen abin dogaro. Hakika Kaine Mai yin baiwa ga bayinka ba don sun chanchanta da ita ba, sai dai don falalarka da rahamarka garesu. To Ya Allah muna Kamun Qafa da fiyayyen Masoyinka, da dukkan abinda yafi soyuwa gareka, Ka cika ni'imominka akanmu, Ka bamu lafiyar fili da boye, Ka suturcemu da bargon suturarka, Kayi mana arzikin duniya da lahira. Ameen. Salatinka mafi girma da amincinka mafi cika su tabbata ga Fiyayyen Bayi,  Annabi Muhammadu kenan tare da iyalan gidansa hasken al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Salihan bayinka har zuwa...

FATIMAH BINTU ASADIN ALHASHIMIYYAH

FATIMAH BINTU ASAD (RTA) ***************************** FATIMAH BINTU ASAD BN HASHIM BN ABDI MANAAF, ALQURASHIYYAH ALHASHIMIYYAH... (Allah shi Qara yarda da ita). Mahaifiyar Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib dashi da 'Yan uwansa Ja'afar bn Abi Talib da 'Aqeel bn Abi Talib (rta). Ita ce wacce ta rike Manzon Allah (saww) kuma ta kula dashi alokacin da yake hannun baffansa Abu Talib. Ta hidimtawa Ma'aiki (saww) tsawon rayuwarsa. Ta musulunta tun afarkon lamari. Kuma tayi hijira zuwa Madeenah, kuma a Madeena dinma ta rasu. Imamuz Zuhriy yace ita ce farkon Bahashimiyar da ta haifi Bahashime kuma Mijinta ma Bahashimi. Kuma ita ce Farkon Bahashiyar da Haifi wanda ya zamto Khalifan Musulunci. Bayan ita sai Fatimah 'Yar Manzon Allah (saww) wacce ta haifi Sayyiduna Hasan (ra).sai kuma Zubaidah Matar Khalifah Harunar Rasheed wacce ta haifi Khalifah Al Ameen. Lokacin da Fatimah bintu Asad (ra) ta rasu,  Manzon Allah (saww) yayi mata likkafani ne da rigarsa mai albarka.. Kuma d...

ALLAH YAFI GABAN KWATANCE

Hakika Allah Madaukakin Sarki, Samamme ne tun gabannin samuwa. Kuma dawwamamme ne ba tare da farko ko Qarshe ba. Babu Jihar da take ritsashi, kuma babu wajen da ake rasashi. Shi Makadaici ne wanda Qirge ko lissafi basu riskarsa. Yafi gaban kwatance da zuciya ko tunanin masu tunani. Bai haifa ba, kuma ba'a haifeshi ba. Shine abin nufin dukkan halittu. Kuma babu wani kini agareshi. Bai yi kama da komai ba, kuma babu abinda yayi kama dashi. Shi Mawadaci ne ba ya bukatar komai awajen kowa, shine wanda kowa ke bukatar komai awajensa. Mai cikakken iko ne wanda ikonsa bai rataya da zamani ko makani ba. Kuma mai nufi ne ga dukkan abinda yaso. Babu mai tambayarsa akan abinda yayi, kuma babu mai tuhumarsa akan abinda bai so kasantuwarsa ba. Shi Masani ne tun gabannin komai. Shi yasan komai, kuma ya san kowa. Amma babu wanda ya sanshi sai shi kansa. Shi Rayayye ne tun gabannin dukkan rayayyu. Kuma shi rayayyen bayan macewar dukkan rayayyu. Rayuwarsa bata ratayu da komai ba. Kuma bata do...

MAI DA'DIN SUNAYE SAWW (06)

Amincin Allah ya tabbata agareku 'Yan uwana cikin So da girmamawa ga Annabin Rahama (saww). Wannan itace fitowa ta shida (6) cikin darasin Zauren Fiqhu mai taken "Mai da'din sunaye" . Wanda acikinsa suke yin sharhi tare da bayanai game da sunayen Manzon Allah (saww) kuma mafiya yawan bayanan muna cirosu ne daga cikin litattafan manyan Maluman wannan al'ummah. Musamman "Zadul Ma'ad" na Ibnu Qayyimil Jauziyyah. Mun tsaya kan suna na takwas, yanzu kuma in shaAllah zamu ci gaba daga nan : 9. NABIYYUL MULHIMAH : Wato "ANNABI SHA-GWAGWARMAYA". Ma'anarsa shine Annabin da Allah ya aikoshi da Yaqi da Maqiyan Allah. Domin hakika babu wani Annabin da yayi yaqi tare da magoya bayansa daga al'ummarsa kamar irin yadda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kuma irin Yaqe-yaqen da suka afku tsakanin al'ummarsa da kuma kafirai, Yaqe-yaqe ne wadanda ba'a ta'ba ganin irinsu ba acikin tarihin duniya. Domin al'umma...

LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA!!!

Abdullahi bn Almubarak (rah) yana daga cikin magabata na kwarai, kuma mutum ne Salihi. Wata shekara bayan yayi niyyar tafiya aikin Hajji, sai ya fita domin yin ban-kwana da abokansa (Almajiransa) kafin tafiyarsa. Amma akan hanyar ne yaga wani abu wanda ya tada masa hankali ya firgitashi. Ya hangi wata baiwar Allah tana tone juji (bola) tana tonowa wani MUSHEN KAZA wacce aka jefar. Ta daukota ta sanya a Qasan hammatarta, ta juya ta tafi aboye acikin duhu. Sai yayi kiranta yace "Mai kikieyi ya ke baiwar Allah?!". Sai tace "Ya kai bawan Allah,  kyale halittu da mahaliccinsu. Domin Allah yana da sha'ani acikin lamarin halittunsa". Sai Ibnul Mubarak yace mata "Ina yi miki magiya don girman Allah ki gaya min labarinki". Sai matar tace masa "Amma wallahi ba don ka riga kayi mun magiya ba, da ban gaya maka halin da nake ciki ba". Kafin ta fara gaya masa har hawaye ya fara zuba daga idanunta. Sai tace "Hakika mu Allah ya halatta mana cin ...

BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (SAWW) - 5

BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (05) *********************************** Yana daga cikin Mu'ujizozin Annabinmu Muhammadu (saww) da kuma alamomin Manzancinsa cewa Allah ya hore masa dukkan halittu masu motsi da marassa motsi sunyi imani dashi, sun shaidar da Manzancinsa kuma suna yin biyayya gareshi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam). Wannan shine kashi na biyar cikin bayanin irin wadannan Mu'ujizozin : Hadeethi daga Sayyiduna Ya'ala bn Murrah Ath-Thaqafiy (rta) acikin wani dogon hadithi yace : "Sai muka ci gaba da tafiya tare da Manzon Allah (saww) har sai da muka sauka awani masauki sai Manzon Allah (saww) yayi barci. Sai ga wata bishiya ta taho tana Tsaga Qasa har sai da ta lullubeshi sannan ta koma wajen da take. Yayin da Manzon Allah (saww) ya farka na ambata masa abinda ya faru sai yace : "ITA DIN WATA BISHIYA CE WACCE TA NEMI IZININ UBANGIJINTA CEWA ZATA GAISHENI.. KUMA YAYI MATA IZINI". Imamul Bagawiy ne ya ruwaito hadisin acikin Sharhus Sun...