Posts

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (106)

2 DAUKAR HAJJI DAGA MASALLACIN QUDUS ********************************************* hadisi daga Yahya bn Abi Sufyan Al-Akhnasiy, daga Kakarsa Hakeematu daga Ummu Salamah matar Manzon Allah (saww) tace taji Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa : "Duk wanda ya dauko niyyar aikin hajji ko umrah daga Masallaci mafi nisa (wato masallacin Kudus) zuwa ga Masallaci mai alfarma (Masallacin Ka'abah) to Allah zai gafarta masa abinda ya gabata da kuma abinda ya jinkirta daga zunubansa, ko kuma Aljannah ta wajabta gareshi. (daya daga cikin mazajen hadisin ne yayi kokwanton ainahin kalmar da aka fa'da). Abu Dawud ne ya ruwaito hadisin acikin Sunanu nasa, Juzu'i na 2 shafi na 143. Kuma yace "Allah ya jiqan Malam Wakee'u (Malamin su Imam Shafi'iy) yayi harramar hajji daga Masallacin Qudus zuwa Makkah. QARIN BAYANI *************** Wannan falala ce ta musamman wacce ta kebanci mazaunan birnin Qudus da sauran biranen dake kewaye dashi, sai ku...

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud...

SHAUKIN SON MA'AIKI (SAWW) DAGA KUTUTTUREN DABINO

Image
Acikin jerin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww) wadanda Zauren Fiqhu ke kawowa, in sha Allahu yau zamuyi magana akan Shahararriyar Mu'ujizar nan wacce duniya take labari. Wato Kukan da itacen dabino (Kututture) yayi saboda shauki, da kuma tashin hankalin da yaji yayin rabuwa da Ma'aiki (saww). Hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace : Manzon Allah (saww) ya kasance ranar Juma'a yana tsayawa ajikin wata bishiya ko itacen dabino (Idan zai yi Khutbah). Sai wata Mace ko Namiji daga cikin mutanen Madeenah tace "Ya Rasulallahi ko mu sanya maka Mimbari ne?". Sai Manzon Allah (saww) yace: "IDAN KUN SO". Don haka sai suka sanya masa Minbari. Yayin da ranar Juma'a tayi, Manzon Allah (saww) ya tafi zuwa ga Minbarin, Sai wannan itacen dabinon yayi kururuwa irin Kururuwar da Jariri ke yi. Sai Manzon Allah (saww) ya sauko (daga kan Minbarin) yaje ya rungumeshi. Sai ya rika yi wani abu kamar yadda yaro Qarami keyi idan an rarrasheshi. Sai...

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud...

SHIN WANENE ANNAMIMI? 02

Assalamu alaikum Jama'a, wannan shine kashi na biyu acikin wani darasin da yazo muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp, mai irin wannan sunan. Gashi nan zamu ci gaba daga inda muka tsaya kamar haka : Malamai suka ce bayyanar da sirrukan jama'a awajen da bai kamata a bayyanar dashi ba, shima yana daga cikin annamimanci kuma haramun ne. 'Yan uwa ku sani cewa kowanne Musulmi mumini yana da wata alfarma ta musamman awajen wacce bai halatta aketa masa ita ba, sai ko akan wani hakki na shari'ah. Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) yace "Naga Manzon Allah (saww) yana dawafi adakin ka'abah yana cewa "MAMAKIN TSARKINKI!  DA TSARKIN QAMSHINKI!. MAMAKIN GIRMANKI, DA GIRMAN ALFARMARKI!. AMMA INA RANTSUWA DA WANDA RAN ANNABI MUHAMMADU (SAWW) KE KARKASHIN IKONSA, WALLAHI ALFARMAR MUMINI TAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DAKE. DUKIYARSA (SHI MUMININ) DA JININSA, KUMA KADA AYI MASA WANI ZATO SAI NA ALLHAIRI". (Ibnu Maajah ne ya ruwaitoshi). Kowanne Musulmi yana da alfarma ta...

NAU'O'IN AZABAR QABARI (02)

Idan ba'a manta ba, tun kwanakin baya Anan Zauren Fiqhu mun kawo muku farkon wannan darasin kashi na daya zuwa na uku. Yanzu kuma ga na hudu : Nau'in azabar Qabari na hudu shine MATSEWAR QABARI. Wato Qabarin zai matse wanda ke cikinsa, Matsewa mai tsanani wanda har sai Qasusuwan haqarkarinsa sun shige cikin junansu...!! Ita wannan matsewar tana faruwa akan kowa. Musui ko kafiri. Kamar yadda Hadisai masu yawa suka bayyana. Misali kamar hadisin da Khalal ya karbo da isnadinsa zuwa ga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa (game da kafiri) : "QABARIN ZAI MATSESHI HAR SAI RUWAN KWAKWALWARSA YA RIKA FITA TA TSAKANIN FARATUNSA DA NAMAN JIKINSA". Akwai hujjoji da yawa da suke tabbatar da cewa lallai wannan matsewar tana shafar Mumini da kafiri. Kamar yadda Malamai da yawa suka bayyanar. Misali kaae ibnu Battah da waninsa. Ga kuma hadisin da Shu'ubah ya karbo daga Sa'adu 'dan Ibrahim daga Nafi'u daga Nana A'ishah (ra) ita k...

NAU'O'IN AZABAR QABARI (01)

Da sunan Allah Mabuwayin Sarki Gagara-Misali. Wanda ya halicci 'Yan Adam daga Qasa, Kuma ya sanyata ta zama Makwancinsu bayan rasuwarsu, sannan kuma daga cikinta zai tashesu aranar babban taro. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da Allah ya zabeshi ya fifita Halittar jikinsa da halayensa da nasabarsa fiye da na sauran halittunsa baki daya, tare da iyalan gidansa da Sahabbansa Taurarin Shiriya. Bayan haka, kamar yadda daliban Zauren Fiqhu suka sani, mun sha kawowa ayoyi, hadisai da hikayoyi wadanda suke tabbatar da cewa azabar Qabari gaskiya ce. Harma mun kawo zancen da Qabari ke yi yayin da za'a sanya Ma'abocinsa cikinsa. Yau kuma in sha Allah zamuyi magana ce akan kala-kalar azabobin Qabari da kuma yadda suke gudana. Kamar yadda muka sha gaya muku acikin darussan Zauren Fiqhu da suka gabata, ita dai azabar Qabari tana gudana ne akan jiki da ruhin Bil Adam. Ga nau'o'inta nan kamar haka : 1. DUKA DA GUDUMAR BAQIN QARFE : Akwai ruwayoyi daban-daban ta hanyo...