SHAUKIN SON MA'AIKI (SAWW) DAGA KUTUTTUREN DABINO

Acikin jerin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww) wadanda Zauren Fiqhu ke kawowa, in sha Allahu yau zamuyi magana akan Shahararriyar Mu'ujizar nan wacce duniya take labari. Wato Kukan da itacen dabino (Kututture) yayi saboda shauki, da kuma tashin hankalin da yaji yayin rabuwa da Ma'aiki (saww).

Hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace : Manzon Allah (saww) ya kasance ranar Juma'a yana tsayawa ajikin wata bishiya ko itacen dabino (Idan zai yi Khutbah).

Sai wata Mace ko Namiji daga cikin mutanen Madeenah tace "Ya Rasulallahi ko mu sanya maka Mimbari ne?".

Sai Manzon Allah (saww) yace: "IDAN KUN SO". Don haka sai suka sanya masa Minbari.

Yayin da ranar Juma'a tayi, Manzon Allah (saww) ya tafi zuwa ga Minbarin, Sai wannan itacen dabinon yayi kururuwa irin Kururuwar da Jariri ke yi.

Sai Manzon Allah (saww) ya sauko (daga kan Minbarin) yaje ya rungumeshi. Sai ya rika yi wani abu kamar yadda yaro Qarami keyi idan an rarrasheshi.

Sai Manzon Allah (saww) yace "Ta kasance tana kuka ne saboda (rabuwa da) abinda ta kasance tana ji na Zikiri awajenta".

(Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi).

Acikin riwayar kuma daga Jabir din (ra) yace:

"Masallacin (na Manzon Allah saww) ya kasance ne yana kafe akan kututturai na Itatuwan dabino.

Manzon Allah (saww) ya kasance yana tsayawa akan wani Kututture daga cikinsu. Amma bayan anyi masa Minbari watarana yana tsaye akan Minbarin sai muka rika jin nishi daga wannan kututturen tamkar irin nishin nan na rakuma mai naquda.

Har sai da Manzon Allah (saww) yazo ya dora hannunsa akansa, sannan yayi shuru".

(Imamul Bukhariy ne ya ruwaito).

Acikin wata riwayar wacce Imamu Ahmad da Ibnu Maajah suka karbo daga Sayyiduna Abdullahi 'dan Abbas (ra), Manzon Allah (saww) cewa yayi :

"WALAHI DA BAN RARRASHESHI BA, DA SAI YACI GABA DA KUKA HAR TASHIN ALQIYAMAH".

Acikin wata riwayar kuma Sai da Manzon Allah (saww) ya tambayeshi Shin kana so in dawo in cigaba damn yin Khutubah akanka, ko kuwa in saukaka acikin gidan Aljannah Muminai sure rika yin 'ya'yanka?".

Sai yace ya za'bi asanyashi agidan Aljannar.  Sai Annabi (saww) yace "TO NA SANYAKA".

ALLAHU AKBAR!!!

Al Imam Hasanul Basariy (rah) ya kasance duk lokacin da ya karanta wannan hadisin yakan yi kuka sannan yace:

"Ya ku taron Musulmai!  Ga Kututturen dabino yayi Kuka yayi kururuwa saboda Shauqin haduwa da Manzon Allah (saww).

Hakika ku kuka fi chanchanta kuyi irin wannan shauqin zuwa gareshi".

Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!

Ya kai 'Da uwana mai daraja! Sau nawa ka ta'ba yin kuka ka zubda hawaye, Kayi Kururuwa saboda Shauqin haduwa da Ma'aiki (saww)??

Wallahi in dai baka ta'ba yi ba, ya Kamata kayi ma kanka kukan rashin yin kukan..

In dai kasan zaka iya yin kuka saboda rabuwa da Mahaifinka ko Mahaifiyarka ko Miji ko Mata, ko dan uwa ko 'yar uwa, to mai yasa ba zakayi kuka saboda rashin haduwa da Manzon Allah (saww) ba?.

Shi yayi maka abinda Iyayenka da 'Yan uwanka ma ba zasu ta'ba yi maka ba. Kuma ya jure wahalhalu domin samun isowar sakon Allah zuwa gareka. Domin ya fidda kai daga hanyar Wuta zuwa ta Aljannah.

Salati da tasleemi da albarka su tabbata bisa Shugaban na farko da na karshe, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa adadin motsin dukkan halittun Allah. Ameen.

DAGA  ZAUREN FIQHU 07064213990 (02-02-2017  05-05-1438).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI