NAU'O'IN AZABAR QABARI (01)

Da sunan Allah Mabuwayin Sarki Gagara-Misali. Wanda ya halicci 'Yan Adam daga Qasa, Kuma ya sanyata ta zama Makwancinsu bayan rasuwarsu, sannan kuma daga cikinta zai tashesu aranar babban taro.

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da Allah ya zabeshi ya fifita Halittar jikinsa da halayensa da nasabarsa fiye da na sauran halittunsa baki daya, tare da iyalan gidansa da Sahabbansa Taurarin Shiriya.

Bayan haka, kamar yadda daliban Zauren Fiqhu suka sani, mun sha kawowa ayoyi, hadisai da hikayoyi wadanda suke tabbatar da cewa azabar Qabari gaskiya ce. Harma mun kawo zancen da Qabari ke yi yayin da za'a sanya Ma'abocinsa cikinsa.

Yau kuma in sha Allah zamuyi magana ce akan kala-kalar azabobin Qabari da kuma yadda suke gudana.

Kamar yadda muka sha gaya muku acikin darussan Zauren Fiqhu da suka gabata, ita dai azabar Qabari tana gudana ne akan jiki da ruhin Bil Adam. Ga nau'o'inta nan kamar haka :

1. DUKA DA GUDUMAR BAQIN QARFE : Akwai ruwayoyi daban-daban ta hanyoyi masu yawa akan wannan. Misali kamar hadisin da Ibnul Jawzee ya ruwaito ta hanyar Sayyiduna Abu Umamatal Bahiliy (ra) yana cewa :

"Manzon Allah (saww) yaje maqabartar baqee'a sai ya tsaya akan wasu Qaburbura guda biyu. Sai yace "SHIN ANAN WAJEN KUKA BINNE WANE DA WANE?.

Sai Sahabbai sukak ce "Kwarai kuwa". Sai yace : "To yanzu gashi nan an zaunar da wane, ana Jibgarsa".

Yaci gaba da cewa : "INA RANTSUWA DA WANDA NUMFASHINA KE HANNUNSA, YANZU HAKA ANYI MASA WANI DUKA GUDA 'DAYA WANDA BABU SAURAN WATA JIJIYA AJIKINSA FACHE SAI DA TA TSINTSINKE.

"KUMA GASHI NAN QABARINSA YANA TASHI DA WUTA. KUMA GASHI NAN WALLAHI YAYI WANI EEHU WANDA DUKKAN HALITTU SUNA JINSA IN BANDA MASU NAUYIN NAN GUDA BIYU,  WATO MUTANE DA ALJANU".

"BA DON KOKWANTON DAKE ZUKATANKU BA, DA KUMA QARI ACIKIN ZANCE, DA WALLAHI SAI KUNJI IRIN ABINDA NAKE JI.

"AMMA WANE, LAIFINSA SHINE YA KASANCE BA YA YIN TSARKI DAGA BAWALI. AMMA WANE KO WANCE, YA KASANCE YANA CIN NAMAN MUTANE NE".

lIbnu Jareer ya ruwaito hadisi acikin littafin tafeerinsa ta hanyar Asbaat daga Suddiy, yana cewa "Sayyiduna Al-Bara'u bn Aazib (ra) yace "Hakika shi kafiri bayan an sanyashi acikin Qabarinsa, sai wata dabba tazo masa wacce idanuwanta biyu tamkar Kaskon wutar dalma suke.

"Tare da ita akwai wata Qatuwar guduma ta baqin Qarfe wacce idan ya jibgeshi da ita atsakanin kafadunsa, sai zabga eehu. Babu wani wanda zai jiyo Eehunsa fache sai ya tsine masa. Kuma babu wata halittar da ba zata jiyoshi ba, sai dai nauyayan nan guda biyu (wato) Aljanu da mutane".

Hakanan akwai wata ruwayar shigen irin wannan daga Dhahhak (ra).

Imam Lalkaa'iy ya ruwaito da isnadinsa ta hanyar Muhammad ibnul Munkadir yace "Labari ya iskeni cewa Allah yana salla'da ma kafiri acikin Qabarinsa wata dabba wacce take Makauniya a hannunta akwai bulala ta Qarfe. Kayinta kamar girman rakumi. Zatayi ta jibgarsa har zuwa tashin Alqiyamah. Ba ta ganinsa, ba ta jin sautinsa ballantana ta tausaya masa".

2. MACIZAI DA KUNAMU : Nau'in bala'i na biyu wanda ake salla'da ma masu laifi acikin Qabarinsu shine Macizai da kunamu.

Isnadin Hadisi daga kan Ibnu Wahbin har zuwa kan Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah (saww) ya tambayi Sahabbai (ra) "Shin ko kun san akan menene aka saukar da ayar nan "فإن له معيشة ضنكا؟". (Lallai akwai rayuwa mai Qunci agareshi).

Shin ko kun san mecece rayuwa mai Qunchi?" sai suka ce "Allah da Manzonsa ne ya sani".

Sai Manzon Allah (saww) yace (Tana nufin) Azabar da za'ayi ma kafiri acikin Qabarinsa ne.

"INA RANTSUWA DA WANDA RAI NA YAKE HANNUNSA, HAKIKA ZA'A SALLA'DA MASA TINNEEN GUDA CHASA'IN DA TARA NE".

"SHIN KO KUN SAN MENENE TINNEENI?"

"MACIZAI NE GUDA CHASA'IN DA TARA. KOWACCE MACIJIYA TANA DA KAYUWA GUDA BAKWAI (ACIKIN WATA RUWAYAR KUMA AKA CE KAYUWA GUDA TARA).

"ZASU RIKA HURA (GUBA) ACIKIN JIKINSA, KUMA SUNA CIZONSA SUNA 'DAYE NAMAN JIKINSA HAR ZUWA RANAR ALKIYAMAH".

(Baqiyyu bn Mukhallad ne da Imamul Bazzar suka ruwaito shi).

Imamu Ahmad da Ibnu Hibban sun ruwaito wani Hadisin daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) yana cewa:

"Za'a sallada ma kafiri Macizai guda chasa'in da tara acikin Qabarinsa zasuyi ta cizonsa har Alqiyamah ta tashi.

Da ache daya daga cikin wadannan Macizan zai hura Qasa, da babu wani koren abu da zai sake tsirowa abayanta".

(Imamu Ahmad da Ibnu Hibban suka ruwaito shi).

Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) da Almajiransa suka tambayeshi akan abinda ake nufi da "MA'EESHATAN DHANKAN" (Wato rayuwa mai Qunchi), Sai yace "Ita ce rayuwar kafiri acikin Qabarinsa.

Qabarin nasa zai matseshi har sai Qasusuwan haqarkarinsa sun shige cikin junansu, har sai yayi burin gara ma ya fito daga Qabarin ya shiga wuta".

Wani hadisin kuma daga Nana A'isha (ra) tace Manzon Allah (saww) yace: "Za'a aika ma Kafiri wasu Jibga-jibgan Macizai guda biyu, 'daya ta wajen kansa, 'daya kuma ta wajen Qafafunsa Zasuyi ta cizonsa. Duk Sanda suka 'daye fatar jikinsa sai fatar ta dawo har zuwa tashin Alqiyamah".

Hakanan Ibnu Abid dunya ya ruwaito wani hadisin ta hanyar Masrouq yana cewa "Babu wani wanda zai mutu alhali yana zina ko shan giya ko kuma wani abun alfasha fache sai Allah ya sallada masa Manyan Macizai acikin Qabarinsa. Suna cizonsa suna cinye naman jikinsa har tashin Alqiyamah".

Ya Allah ka kiyayemu daga azabar Qabari. Ka gafarta mana zunubanmu, kayi mana afuwa busa laifukanmu don albarkar Annabinka (saww).

Anan zamu tsaya sai acikin kashi ba biyu zamu dora daga nan. In sha Allahu.

DAGA ZAUREN FIQHU (09-01-2017) 07064213990 Kuje kuyi "liking" din shafinmu na facebook

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI