SHIN WANENE ANNAMIMI? 02

Assalamu alaikum Jama'a, wannan shine kashi na biyu acikin wani darasin da yazo muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp, mai irin wannan sunan.

Gashi nan zamu ci gaba daga inda muka tsaya kamar haka :

Malamai suka ce bayyanar da sirrukan jama'a awajen da bai kamata a bayyanar dashi ba, shima yana daga cikin annamimanci kuma haramun ne.

'Yan uwa ku sani cewa kowanne Musulmi mumini yana da wata alfarma ta musamman awajen wacce bai halatta aketa masa ita ba, sai ko akan wani hakki na shari'ah.

Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) yace "Naga Manzon Allah (saww) yana dawafi adakin ka'abah yana cewa "MAMAKIN TSARKINKI!  DA TSARKIN QAMSHINKI!. MAMAKIN GIRMANKI, DA GIRMAN ALFARMARKI!. AMMA INA RANTSUWA DA WANDA RAN ANNABI MUHAMMADU (SAWW) KE KARKASHIN IKONSA, WALLAHI ALFARMAR MUMINI TAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DAKE. DUKIYARSA (SHI MUMININ) DA JININSA, KUMA KADA AYI MASA WANI ZATO SAI NA ALLHAIRI".

(Ibnu Maajah ne ya ruwaitoshi).

Kowanne Musulmi yana da alfarma ta musamman wacce ta wajabta maka ka kiyaye masa mutuncinsa da dukiyarsa da jininsa. Kuma ta wajabta maka kada kayi masa mummunan zato, kada ka dauki sirrinsa ka gaya ma wani, kada ka rike binciken laifukansa don tozartarwa.

Manzon Allah (saww) yace "DUK WANDA YAKE SAURARAR ZANCEN MUTANE ALHALI BASU SO, TO ZA'A KWARARA MASA NARKAKKIYAR DALMA ACIKIN KUNNUWANSA ARANAR ALKIYAMAH".

(Bukhariy ne ya ruwaito hadisin akan lamba ta 7042).

Wannan ita ce irin azabar da ake yiwa magulmata masu saurarar hirar jama'a ba tare da izininsu ba. Suna daga mafiya shan tsananin azaba aranar alqiyamah. (Allah shi kiyayemu).

Manzon Allah (saww) yace "A daren da akayi mi'iraji dani, na wuce ta kusa da wasu mutane suna da faratun dalma, suna kwaye nama fuskokinsu da Qirazansu. Sai nace "Ya Jibreelu wadannan su wanene?".

Sai yace sune masu cin naman mutane kuma suna afkawa cikin mutuncinsu".

(Abu Dawud ne ya ruwaitoshi).

Imamu Ahmad ya ruwaito hadisi acikin Musnadu juzu'i na 4 shafi na 227 daga Abdullahi bn Ganam (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa :

"ZABABBUN BAYIN ALLAH SUNE WADANDA IDAN AN GANSU AKE TUNA ALLAH. KUMA MAFIYA SHARRIN BAYIN ALLAH SUNE MASU YAWO DA ANNAMIMANCI, MASU LIQA LAIFI GA WADANDA BASU DASHI, ALLAH ZAI TASHESU TARE DA KARNUKA (ARANAR ALQIYAMAH).

Duk wadannan hadisan suna karantar damu tare da yin gargadinmu akan girman laifin annamimanci ne. Har ma da hadisan da muka karanta abaya wanda Manzon Allah (saww) ya nuna cewa ana yiwa Annamimai azaba mai tsanani acikin Qabarinsu.

Hafizul Munziriy yace "Dukkan Maluman al'ummah sun yarda da cewa annamimanci haramun ne. Kuma yana daga cikin mafiya girman zunubai awajen Allah.

Imam San'aniy yace akwai yanayin da kuma annamimanci yakan zama wajibi. Misali idan kaji wani yana kokarin shirya yadda zai cuci wani ko wasu, to wajibi ne gareka kaje ka gargadi wancan din ba tare da ambaton sunan masu kokarin aikata laifin ba. Sai dai in ya zama dole sannan ka fadi sunan nasu.

Anan zamu tsaya da fatan Allah shi kiyayemu daga sharrin Annamimai da annamimanci. Ameen.

An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar 03/12/1439 14/08/2018.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI