MAGANIN CHUTUKAN FATA :


TAMBAYA TA 2554
*******************
Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai :

- Man Jirjir,
- Man kwakwa.
- Man Ghelo.
- Man Kadanya.
- Man Alayyadi.
- Man Zaitun.
- Man Aloe Vera.

Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje guda. Misali :

1- Ki samu danyen reshen Aloe Vera (wani tsiro ne kore shar, ana yin flower dashi a makarantu da ofisoshi) ki dandakashi ki goga ruwansa akan fatarki daidai wajen da abun ya fito. Zaki barshi kamar tsawon minti 30 sannan ki wanke da ruwan dumi.

Bayan kin wanke sai ki kawo man alayyadi ko man kadanya ki shafa awajen. Haka zaki ci gaba dayi har sati biyu. Idan zaki kwanta barcin dare sai ki kwaba lalle (Henna leaves) ki shafa aduk wuraren da abin ya fito.

In shaAllah zaki ga waraka da izinin Allah. Koda Makero ne ko Tautau ko gargartu, ko Qazzuwa duk za'a iya jarraba wannan fa'idar kuma za'a dace In sha Allah.

Idan babu Aloe Vera awajejenku, sai ki nemi danyen ganyen lalle ki dakashi ki goga awajen. Idan babu man kadanya sai kuyi amfani da Man Alayyadi ko Man kwakwa.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU  (24/11/1439  06/08/2018)

ZAKU IYA TURO DA TAMBAYOYINKU TA ADIRESHINMU NA EMAIL : zaurenfiqhu@gmail.com ko ku ziyarci babban shafinmu na facebook :  www.facebook.com/zaurenfiqhu

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI