NAU'O'IN AZABAR QABARI (02)

Idan ba'a manta ba, tun kwanakin baya Anan Zauren Fiqhu mun kawo muku farkon wannan darasin kashi na daya zuwa na uku. Yanzu kuma ga na hudu :

Nau'in azabar Qabari na hudu shine MATSEWAR QABARI. Wato Qabarin zai matse wanda ke cikinsa, Matsewa mai tsanani wanda har sai Qasusuwan haqarkarinsa sun shige cikin junansu...!!

Ita wannan matsewar tana faruwa akan kowa. Musui ko kafiri. Kamar yadda Hadisai masu yawa suka bayyana.

Misali kamar hadisin da Khalal ya karbo da isnadinsa zuwa ga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa (game da kafiri) :

"QABARIN ZAI MATSESHI HAR SAI RUWAN KWAKWALWARSA YA RIKA FITA TA TSAKANIN FARATUNSA DA NAMAN JIKINSA".

Akwai hujjoji da yawa da suke tabbatar da cewa lallai wannan matsewar tana shafar Mumini da kafiri. Kamar yadda Malamai da yawa suka bayyanar. Misali kaae ibnu Battah da waninsa.

Ga kuma hadisin da Shu'ubah ya karbo daga Sa'adu 'dan Ibrahim daga Nafi'u daga Nana A'ishah (ra) ita kuma ta karbo daga Manzon Allah (saww) yana cewa :

"LALLAI AKWAI MATSA GA QABARI. DA ACHE AKWAI WANDA ZAI TSIRA DAGA WANNAN, LALLAI DA SA'ADU BN MU'AZ YA TSIRA".

Imamu Ahmad da Imam Sufyanuth Thawree ma duk sun ruwaito irinsa.

Hakanan Ibnu Luhai'ah ya karbo daga Aqeel da Sa'adu 'dan Ibraheem daga A'ishatu bintu Sa'ad daga Nana A'ishah (ra) tace Manzon Allah (saww) yace mata "KI NEMI TSARI DAGA AZABAR QABARI. DOMIN KUWA DA ACHE WANI ZAI TSIRA DAGA GARESHI, DA SA'ADU BN MU'AZ YA TSIRA. SAI DAI QABARIN BAI QARA KOMAI BA AKAN MATSESHI DA YAYI". (WATO IYAKAR ABINDA YAYI MASA KENAN).

Imam Tabaraniy ma ya ruwaitoshi.

Sayyiduna Sa'ad bn Mu'az (ra) shine Sahabin nan wanda aranar Mutuwarsa sai da Al'arshi tayi girgiza, Kuma akan bude masa Kofofin Sammai, Kuma Mala'iku dubu saba'in ne suka sauko domin halartar jana'izarsa.

Amma duk da haka shima sai da Qabarinsa ya matseshi, sannan kuma aka yaye masa aka ci gaba da ni'imtashi.

Imamu Ahmad da Tabaraniy da Nisa'iy sun karbo wani hadisi ta hanyar Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace :

Yayin binne Sa'adu bn Mu'az (ra) sai Manzon Allah (saww) yace : "SUBHANALLAH (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH) WANNAN FA SALIHIN BAWA NE WANDA AL'ARSHIN ALLAH MAI RAHAMA TAYI GIRGIZA SABODA SHI KUMA AN BUDE MASA KOFOFIN SAMMAI AMMA GASHI SAI DA AKA TSANANTA MASA (QABARIN) SANNAN AKA YAYE DAGA GARESHI".

Sai dai Malamai suna da maganganu da dama da kuma fassare fassare game da wannan Mas'alar. Misali Ibnu Abid Dunya ya karbo Ibnu Abdillah At-Tamimiy yace "Naji Abubakrin Attamimiy wani dattijo ne daga cikin Quraishawa yana cewa :

"Dalilin matsewar da Qasa take yiwa Ma'abotan Qabari shine ita Qasa ita ce Uwarsu domin daga gareta ne aka haliccesu, sai suka 'bace mata lokaci mai tsawo.

Yanzu kuma tunda an dawp mata da 'ya'yanta shine take matsesu, irin matsewar da uwa take yiwa 'danta wanda ta dade bata ganshi ba.

Idan mutum Salihi ne to zata matseshi ne da tausasawa. Amma idan kafiri ne ko mai aikata sa'bo da yawa, zata matseshi ne matsewa irin na azaba saboda fushi bisa abinda yake aikatawa.

Hannad bn Sirriy ya ruwaito cewa watarana an wuce da gawar wani Qaramin yaro sai Nana A'ishah tayi kuka tana cewa : "Ina yin kuka ne saboda wannan yaron saboda tausayin matsewar da Qabari zai yi masa".

Su dai Muminai bayan Qabari ya matsesu da farko, nan take kuma ake saukaka musu a buda musu Qabarinsu. Amma Kafirai da fajirai da Munafukai kuma, Qabarin nasu zai ci gaba da matsesu ne har zuwa Qarshen zamansu acikinsa, wato tashin Alqiyamah.

Kuma wani hadisi daga Al-Bara'u bn Aazib (ra) daga Manzon Allah (saww) yace "Za'a tufatar da Kafiri dai wasu tufafi guda biyu na gidan wuta.. Shine fassarar ayar da Allah yake cewa :

"SUNA DA WATA SHIMFIDA DAGA JAHANNAMA, KUMA AKWAI WANI RUFI (NA AZABA) DAGA SAMANSU".

Ya Allah ka kiyayemu daga azabar Qabari da duhun Qabari da Quncin Qabari. Ka sada mu da ni'imominsa da yalwarsa da haskensa don Soyayyar da muke yiwa Annabinka (saww).

Anan zamu tsaya sai kuma acikin darasi na gaba wanda zamu gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp 1-5 in sha Allah.

DAGA ZAUREN FIQHU (28-03-2017) 07064213990

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI