HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (106)

2DAUKAR HAJJI DAGA MASALLACIN QUDUS
*********************************************
hadisi daga Yahya bn Abi Sufyan Al-Akhnasiy, daga Kakarsa Hakeematu daga Ummu Salamah matar Manzon Allah (saww) tace taji Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa :

"Duk wanda ya dauko niyyar aikin hajji ko umrah daga Masallaci mafi nisa (wato masallacin Kudus) zuwa ga Masallaci mai alfarma (Masallacin Ka'abah) to Allah zai gafarta masa abinda ya gabata da kuma abinda ya jinkirta daga zunubansa, ko kuma Aljannah ta wajabta gareshi. (daya daga cikin mazajen hadisin ne yayi kokwanton ainahin kalmar da aka fa'da).

Abu Dawud ne ya ruwaito hadisin acikin Sunanu nasa, Juzu'i na 2 shafi na 143. Kuma yace "Allah ya jiqan Malam Wakee'u (Malamin su Imam Shafi'iy) yayi harramar hajji daga Masallacin Qudus zuwa Makkah.

QARIN BAYANI
***************
Wannan falala ce ta musamman wacce ta kebanci mazaunan birnin Qudus da sauran biranen dake kewaye dashi, sai kuma masu ziyarah wadanda ke zuwa chan sannan su dauko haramar Hajji ko Umrah.

Wannan masallacin na Qudus shine masallaci mai daraja ta uku a addinin Musulunci. Kuma  Annabi (saww) yayi umurnin ziyartarsa da yin sallah acikinsa.

Acikin daren Isra'i da Mi'iraji Allah ya tafiyar da babban bawansa wato Annabinmu Muhammadu (saww) daga Masallacin harami zuwa ga masallai mafi nisa (Qudus) kuma yanzu haka akewayen masallacin akwai wajen da Manzo (saww) ya 'daure akalar buraqarsa, da kuma gurbin wajen da ya tsaya yayi wa Annabawa limancin Sallah (saww).

Yanzu haka madafan ikon birnin suna Karkashin hannun Yahudawan Isra'eela wadanda kafircinsu da muguntarsu ga Musulunci da Musulmai ba boyayyen abu bane.

Fatanmu shine Allah ya Qarfafi musulunci da Musulmai yadda zamu samu damar 'yantar da wannan masallacin. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (29/08/2018 18/12/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI