Posts

MAI MATSAYIN QUREWA (SAWW).

Manzon Allah (saww) shine cikakken Malamin al'ummah. Malamin da bai koyi karatu awajen kowa ba, amma awajensa kowa yake kwankwadar ilimi. Acikin maganganunsa zaka samu Ilimai na zahiri da na 'boye. Zaka ji Ilimin Geography, Physiology, Astrology, Gynaecology, Botany, Economy, da sauran dubban ilimai wadanda babu wani 'Dan Adam da ya sansu. Allah ya fifita Annabi Aadamu akan Mala'iku ne tunda ya san ilimin Sunaye wanda su basu sani ba.. Don haka Allah yace suyi masa Sujadah su gaisheshi. Shi kuwa Annabi Yusufu (as) Allah ya fifitashi akan sauran 'Yan uwansa ne da ilimin sanin fassarar Mafarkai da kuma Mafita acikin al'amura boyayyu. Don haka Allah ya bashi Mulki da fifiko asamansu. Shi kuwa Khidru (as) Allah ya sanar dashi wani ilimi ne tsakaninsa dashi, ba tare da wani atsakani ba.. Ya sanar dashi Ilimin hangen nesa. Don haka ma ya bashi Manyan Annabawa suka zama Almajiransa. Wato irin su Annabi Musa da Yusha'u (alaihimus Salam). Annabi Dawud Allah ya s...

MU SAN ANNABINMU (31)

Da sunan Allah mamallakin dukkan komai, Salati da amincinsa su tabbata bisa Fiyayyen Annabawansa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka, da masu biye dasu da dukkan Salihan bayi har zuwa ranar sakamako. Sannan shine kashi na talatin da daya acikin darasin tarihin Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu Whatsapp. Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya. Idan baku manta ba, a darasinmu na 30 mun tsaya ne akarshen bayanin abubuwan da suka faru a yaqin gwalalo. Yanzu kuma zamu shiga cikin bayanin   yaqin da akayi da Yahudawan Banu Quraizah wadanda suka hada baki da kafirai don yaqar musulmai. YAQIN BANU QURAIZAH ************************* Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wayi gari sai ya koma cikin garin Madeenah tare da sauran jama'ar musulmai duk suka ajiye kayan yaqinsu (wato makamai). Shi kuwa Sayyiduna Sa'adu bn Mu'az (radhiyallahu anhu) saboda damuwa d...

MU SAN ANNABINMU (30)

Da sunan Allah Sarkin Sarakuna, Salatai marassa yankewa su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa da Sahabbansa tare da aminci gwargwadon girmansa. Wannan shine kashi na talatin acikin darasin tarihin Shugaban halittu (saww) wanda ke zuwa daga Zauren Fiqhu. Kuma zamu dora daga inda muka tsaya ne acikin bayanin yaqin gwalalo (Gazwatul Ahzab). Yayin da wannan sahabi (Sa'adu bn Mu'az) ya samu wannan mummunan rauni sai yai addu'a ga kafirai da yahudawan da sukayi yaudara, yace: "Ya Allah idan har akwai abinda ya saura daga yaqin Quraishawa, to ka wanzar dani (in halarci yaqin) domin babu wasu mutanen da nafi so in yaqesu fiye da wadannan da suka chutar da Annabinka kuma suka Qaryatashi. To Ya Allah idan kuma ka kawar da yaqi atsakaninmu dasu, to ka sanya (wannan raunin da akayi mun) ya zamto shahada gareni, kuma kada ka kasheni har sai ka faranta mun raina game da yahudawan banu quraizah". To dama su Banu Quraizah sun kasance abokan huldarsa ne kuma maji...

MADUBIN DUBAWA (75)

QARSHEN MAI CI DA ADDINI ***************************** Al Imam Ibnul Jauzee ya hakaito daga Uthman bn Abdillah cewa a zamanin Annabi Musa (amincin Allah ya tabbata gareshi da Annabinmu) akwai wani mutum wanda yake hidimta masa, kuma yana neman ilimi awajensa. Watarana sai wannan mutumin ya nemi izini awajen Annabi Musa (alaihis salam) cewa yana so zai je garinsu ya dawo. Sai Annabi Musa (alaihis salam) yayi masa izini ya tafi. Amma daga zuwansa sai ya mayar da kansa tamkar shine malamin garin. Yana tashi yana wa'azi atsakanin mutanen garin, motsi ka'dan sai yace musu "Musa kaleemul Lahi (alaihis salam) ya bani labari cewa kaza yayi kaza". Ko kuma "Annabi Musa mai ganawa da Allah ya bani labari cewa kaza yayi kaza... ". Su kuma mutanen garin suna jin dadi suna tara masa dukiya har dai ya tara kudi da dukiya mai yawan gaske. Kuma daga nan ya zauna agarinsu bai sake komawa wajen Annabi Musan ba. Shi kuwa Annabi Musa (alaihis salam) ya kasance yana yawan t...

MU SAN ANNABINMU (29)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, Salati da amincinsa su tabbata bisa zababben zababbunsa Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya. Har yanzu dai muna cikin bayanin abubuwan da suka faru ne a lokacin yaqin Ahzab (yaqin gwalalo) wanda mushrikan Quraishawa suka ha'da kai da sauran Qabilun larabawa da yahudawa da munafukan madeenah domin su murkushe musulunci amma Allah bai idda nufinsu ba. Dakarun Mushrikan Makkah sunyi sansani atsakanin tudun nan mai suna Juruf da Zugabah, su kuma Qabilar Gatfan sunyi sansani kusa da dutsen Uhudu, Shi kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya fito tare da Sahabbansa guda dubu uku sun yi nasu sansani kusa da dutsen Sal'u. Dama a baya na gaya muku cewa Yahudawan Madeena (wato Banu Quraizah) sun warware alkawarin dake tsakaninsu da Musulmai, don haka dole aka kwashe Qananan yara da Mata duk aka boyesu awani waje saboda tsoron sharrin Yahudawa. Ana cikin wannan tashin hankali...

MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari. 'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka : YAQIN BADAR NA KARSHE : Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar". Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wa...

MU SAN ANNABINMU (27)

Da sunan Allah Mabuwayi Gagara-Misali,  Salati da amincinsa madawwama su tabbata bisa cikakken bawansa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya. Da mabiyansu da magoya-bayansu har zuwa ranar cikar alkawari. 'Yan uwa wannan shine fitowa ta ashirin da bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu Whatsapp mai dauke da tarihin rayuwar Ma'aikin Allah (saww). Mai taken "MU SAN ANNABINMU". Kuma zamu dora ne daga inda muka tsaya a darasinmu wanda ya gabata kamar haka : YAQIN BADAR NA KARSHE : Idan baku manta ba, aranar yaqin uhudu lokacin da Abu Sufyan yaga alamar kamar sune da nasara (Aun shahadantar da mutum saba'in daga cikin musulmai) sai yace : "Uhudu ramuwar badar ce. Kuma shekara mai zuwa mu hadu a badar". Don haka da shekara ta zagayo, wato acikin shekara ta hudu kenan bayan hijirah, sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi shirin yaqi ya fita zuwa filin nan na badar (wajen da akayi wa...