Posts

Showing posts from April, 2016

SAYYIDUNA ABUBAKRIN (RTA) -3

KHALIFAN MANZON ALLAH (saww) Azamanin Khalifancinsa, bayan wafatin Manzon Allah (saww) Farkon annobar data fara kunnowa kai ita ce: RIDDA da yawancin larabawan Qauyuka suka rika yi. Mafiya yawansu daga jin cewar Manzon Allah (saww) yayi wafati shikenan sai sukayi ridda suka fice daga Musuluncin. Wasu kuma basu bayyana cewar sun fita daga Musuluncin ba, sai dai sun Qi bayar da zakkah. Wasu kuma bayan riddar ma, har sun fara da'awar Annabta. Irinsu Musaylamah Alkazzab. Har sai da ya zama iya garuruwa 3 ne kadai ake yin Musulunci aduniya. Wato Makkah, Madeenah, da Ta'if. Amma matakin farko da ya fara yi shine zartar da abubuwan da Manzon Allah (saww) ya riga ya fara su. Misali kamar tashin rundumar Usamah bn Zaid bn Harithah zuwa yakin Rum. Da yawa daga cikin Sahabbai sunyi niyyar hanashi tura wannan rundunar. Saboda ganin halin da ake ciki. Yayin da Sayyiduna Umar (ra) ya tareshi ya gaya masa cewar bai kamata atura wannan rundunar ba. Sai ya bada amsa cewar: "Walla

FALALAR NEMAN ILIMI

Mafiya yawan mutanenmu awannan zamanin basu dauki neman ilimin addini amatsayin da ya kamata su daukeshi ba. Sun daukeshi ne amatsayin wani abu na wucin-gadi. (Wato kamar bai zama lallai akansu ba). Manzon Allah (saww) yace "NEMAN ILIMI FARILLA NE AKAN KOWANNE MUSULMI DA MUSULMA". Ilimi yana sama da dukkanin wata baiwa wacce Allah yake yiwa 'Dan Adam. Shi yasa ma Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya rika yin addu'ar neman Qarin ilimi yana cewa : "KACE YA UBANGIJI KA QARA MIN ILIMI". Sannan tun farko wannan jinsin namu ya samu daukaka ne saboda albarkar ilimi. Allah ya Umurci Mala'iku sunyi Sujjadah ga Annabi Aadam (as) ne saboda fifikon ilimin da yayi musu. Ilimin addini abu ne wanda ya zama Wajibi ka nemeshi tun daga zanin goyo, har zuwa Qabarinka. Babu ranar denashi. Domin kuwa idan kaje ma Allah amatsayinka na jahili, to fa baka da sauran wani uzuri awajensa (SWT). "Ban sani ba" ko kuma "Ban samu lokaci ba" Ba zasu zama Uz

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************************** Anan ZAUREN FIQHU Muna yawan samun tambayoyi akan wannan Mas'alar daga bangarorin Maza da mata. Amma in sha Allahu yanzu zanyi bayani daidai gwargwadon iko. Bismillahir Rahmanir Raheem. Ina fatan zaku gafarceni. Zanyi bayani dalla dalla (duk da cewar akwai nauyi sosai) to amma abu ne wanda ya shafi addini. Kuma bangaren tsarki ne wanda sai dashi ibadah zata yiwu. Maniyyi da Maziyyi suna da bambanci ta bangarori guda uku kamar haka: 1. Bambanci a yanayin Siffarsu. 2. Bambanci ayanayin da ake ji bayan fitarsu. 3. Bambanci a bangaren hukuncinsu. 1. SIFFOFINSU ***************** Manzon Allah (saww) shi da kansa yayi bayanin yadda siffarsu take yayin da yake bada amsa bisa tambayar da Sayyidah Ummu Sulaym tayi masa. Yace : "SHI DAI MANIYYIN NAMIJI, FARI NE KUMA YANA DA KAURI. SHI KUMA MANIYYIN MACE, FATSI FATSI NE, KUMA TSINKAKKE NE (BASHI DA KAURI). (Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi). Akan wannan n

DALILAN DAKE JANYO MA MUTUM AZABAR QABARI

Kwanciyar Qabari tana daga cikin manyan Jarrabobin dake jiran kowanne mutum dake raye aduniyar nan. Kowa zai fara riskar yanayin sakamakon ayyukansa ne tun daga Qabarinsa. Kamar yadda muka bayyanar acikin Lakchochinmu da dama wadanda muka gabatar anan Zauren Fiqhu, lallai Hadisai sun tabbata daga Manzon Rahama (saww) wanda ya tabbatar da cewa Shi Qabari shine Masauki na farko daga Masaukan Lahira. Idan yayi kyau, to abinda ke gabansa ya fishi kyawu. Idan kuma yayi Muni, to abinda ke gabansa ya fishi Muni. Kuma lallai duk inda kaga Qabari, to kodai ya zamanto dausayi ne daga dausayoyin Aljannah, ko kuma Kwazazzabo ne daga Kwazazzaban azabar wutar jahannama. Kuma lallai babu bambanci cikin adadin dadewar da bayin Allah zasuyi acikin Qabarinsu. Da wanda ya mutu tun azamanin farko, da wanda ya mutum awannan zamanin da muke ciki, duk babu bambanci. Hakanan babu bambanci tsakanin wanda ya mutu aka binneshi, da wanda ya mutu acikin ruwa gawarsa ta ru'be, da wanda wuta ta cinye namansa,

TWELVE POINTS AGENDA DAGA ZAUREN FIQHU

DUK WANDA YAKE SO 'YARSA KO MATARSA, KO QANWARSA TAYI KARATUN BOKO MAI ZURFI (Higher Institutions) YA ZAMA WAJIBI YA KULA DA WADANNAN ABUBUWAN GUDA GOMA SHA-BIYU: 1.Wajibi ne ya zama tana da ilimi akan addininta tare da fahimtar abubuwan da suka haramta agareta. Gwargwadon yadda zata iya kiyaye dokokin shari'ar Allah, kuma ta kauce ma haramtattun abubuwa. 2. Wajibi ne shi karatun zamanin ya zama ya cancanta mace ta karance shi a shari'ah, Kamar misali KARATUN HARKAR LAFIYA, KARBAR HAIHUWA, ISLAMIC LAW, etc. 3. Wajibi ne ya zama tana da kwakwalwar da zata iya rike karatun: domin bai kamata ka sanyata amakarantar Alhalin kasan ba zata fahimci wannan fannin ba. Irin haka ne yake sa wasu yaran suke dadewa basu kammala ba. Saboda faduwar Jarabawa. 4. Wajibi ne ya zama akwai kudin da za'a dauki dawainiyar ta. Rashin wannan ne yake sanya wasu yaran DAUKAR NAUYIN KANSU, kuma amatsayinta na 'YA-MACE, zata iya aikata kowacce irin 'Barna domin ta samu kudin biyan Maka

ADDU'AR SAMUN BIYAN BUKATU

Image
ADDU'AR SAMUN BIYAN BUKATU : ************************************ Ku bude Kunnuwanku ku saurara. Addu'a ce ta Musamman wacce Annabi (saww) yayi ma 'Yarsa (Nana Fatimah) Wasiyyah da ita. Sayyiduna Anas bn Malik (rta) ya ruwaito cewa watarana Manzon Allah (saww) yace ma 'Yarsa Nana Fatimah (r.a.): "MAI ZAI HANAKI KI SAURARI ABINDA ZANYI MIKI WASIYYAH DASHI? KI RIKA FA'DA IDAN KIKA WAYI GARI, DA KUMA IDAN KIN YAMMANTA : "YA HAYYU YA QAYYOUM BI RAHMATIKA ASTAGHEETHU, ASLIHLEE SHA'ANEE KULLAHU WALA TAKILNEE ILA NAFSEE TARFATA 'AININ". MA'ANA : Ya Rayayyen Sarki, Ya Madawwami (Tsayayye akan lamarin bayinsa) da rahamarka ne nake neman Taimako. Ka kyautata min sha'anina baki dayansa. Kar ka dogarar dani zuwa ga kaina. #Imamun Nisa'iy ne da Bazzaar suka ruwaitoshi da Ingantaccen Isnadi. ZAUREN FIQHU : ***************** Wannan addu'a ce ta musamman wacce in sha Allahu Za'a samu biyan bukatu idan dai ana yinta da kyakyawar

HUKUNCIN AIKIN MALAMIN TSAFTA

HUKUNCIN AIKINSA A GWAMNATI TAMBAYA TA 1900 ********************* Assalamu alaikum  ALLAH YA SAKA MA MALAM DA MAFIFICIN ALHERI AMIN. BAYAN HAKA MAL INADA TAMBAYA KAMAR HAKA AKAN AIKI GWAMNATI A DAUKI AIKI  AKAN MALAMIN TSAFTA GARINMU  IN KULA DA  GARINMU NE  INA MAGANA AKAN SHARA MUSAMMAN MASU SANA'A TO AMMA WASU NAYI WASU BASAYI  IDAN NAYI MAGANA SUCE NA MATSA MASU  SHIN MALAN YAYA MATSAYIN ALBASHINA YAKE? KA HUTA LAFIYA AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko ina tayaka murnar samun aiki. Kuma ina yi maka nasiha tare da ni kaina, da jin tsoron Allah afili da boye tare da bin dokokinsa ba tare da tsoron zargin masu zargi ba. Wannan aikin naka na Malamin Tsafta, aiki ne mai Muhimmancin gaske. Domin kuwa tsafta tana da matsayi mai girma a addinin Musulunci. Manzon Allah (saww) yace "TSAFTA TANA CIKIN IMANI". Don haka amatsayinka na Malamin tsafta wajibi ne ka tsaya ka kula da aikin da Gwamnati ta daukeka kuma take biyanka akansa. K

HASKEN ZIKIRIN ALLAH

HASKEN ZIKIRIN ALLAH (SWT) ****************************** BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Hakika dukkan Malamai Masanan Allah sun tabbatar da cewa babu wani abu guda daya wanda yake bude Zuciyar 'dan Adam fiye da Zikirin Allah. Kuma babu aiki mafi sauki kuma mai kawowa mutum lada masu yawa acikin Qankanin lokaci kamar Zikirin Allah. Kuma babu aiki mafi daraja awajen Allah fiye da Zikiri. Shi yasa ma Madaukakin Sarkin yace : "KU AMBACENI NIMA ZAN AMBACEKU". Kuma yace "KU AMBACI ALLAH, AMBATO MAI YAWA, KUMA KU TSARKAKE SUNANSA (TASBEEHI) SAFIYA DA MARAICE". Kuma babu wata katanga mafi Qarfi wacce take tsare mutum sannan ta kubutar dashi daga Sharri da makircin Shaitan fiye da Zikirin Allah. Hakika shi Zikirin Allah, wata Aljannah ce adoron Qasa wacce duk wanda bai shiga cikinta anan duniya ba, to ba zai shiga waccen Aljannar ta lahira ba. Zikirin Allah shi kadai ne yake ceton zukata daga 'dimuwa da tsoro da firgici, Kuma shine hanya mafi sauki domin samun