FALALAR NEMAN ILIMI

Mafiya yawan mutanenmu awannan zamanin basu dauki neman ilimin addini amatsayin da ya kamata su daukeshi ba. Sun daukeshi ne amatsayin wani abu na wucin-gadi. (Wato kamar bai zama lallai akansu ba).

Manzon Allah (saww) yace "NEMAN ILIMI FARILLA NE AKAN KOWANNE MUSULMI DA MUSULMA".

Ilimi yana sama da dukkanin wata baiwa wacce Allah yake yiwa 'Dan Adam. Shi yasa ma Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya rika yin addu'ar neman Qarin ilimi yana cewa : "KACE YA UBANGIJI KA QARA MIN ILIMI".

Sannan tun farko wannan jinsin namu ya samu daukaka ne saboda albarkar ilimi. Allah ya Umurci Mala'iku sunyi Sujjadah ga Annabi Aadam (as) ne saboda fifikon ilimin da yayi musu.

Ilimin addini abu ne wanda ya zama Wajibi ka nemeshi tun daga zanin goyo, har zuwa Qabarinka. Babu ranar denashi. Domin kuwa idan kaje ma Allah amatsayinka na jahili, to fa baka da sauran wani uzuri awajensa (SWT).

"Ban sani ba" ko kuma "Ban samu lokaci ba" Ba zasu zama Uzuri agareka ba, aranar alkiyamah. Domin kuwa Ubangiji ya riga ya rayaka har zuwa shekarun balaga. Watakil ma har kayi aure ka haihu.

Hadisai ingantattu sunzo akan Maganar falalar Neman Ilimi. Misali kamar Hadisin nan na cikin Sahihul Bukhariy wanda Annabi (saww) yace "DUK WANDA YABI WATA HANYA WACCE YAKE NEMAN ILIMI ACIKINTA, TO ALLAH ZAI SAUKAKA MASA HANYAR ZUWA ALJANNAH".

Da kuma Hadithin da Manzon Allah (saww) yake cewa "DUNIYA TSINANNIYA CE, DUKKAN ABIN CIKINTA MA TSINANNE NE. IN BANDA MALAMI DA MAI NEMAN ILIMI, DA ZIKIRIN ALLAH DA ABINDA KE KEWAYE DASHI".

Sayyiduna Safwan bn 'Usaal Al-Muradiy (rta) yace : "Naje wajen Manzon Allah (saww) alhali shi yana kwance acikin Masallaci akan wani jan Mayafinsa.

Sai nace "Ya Ma'aikin Allah, Ni nazo neman Ilimi ne".

Sai yace "MARABA DA MAI NEMAN ILIMI. HAKIKA SHI MAI NEMAN ILIMI MALA'IKU SUKAN KEWAYESHI HAR SU RIKA YI MASA INUWA DA FUKAFUKANSU, SANNAN SU RIKA HAWA SAMAN JUNANSU HAR SAI SUN TA'BO SAMAN DUNIYA, SABODA MURNARSU AKAN ABINDA YAKE NEMA".

(Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi da isnadi mai inganci).

Kamar yadda Manzon Allah (saww) yace : Sallah ita ce farkon abinda za'a yiwa Mutum hisabi akansa aranar Alqiyamah.

Idan tayi kyau to za'a karbeta tare da sauran ayyukansa. Idan kuma tayi muni, to sai a mayar masa da ita tare da sauran ayyukansa".

To amma ita sallah bata kyautatuwa dole sai da ilimin sanin tsarki da alwala da Farillanta da sunnoninta.

Ashe kenan duk wanda bashi da Ilimin addini, Zai wahala sallarsa ta zama karbabbiya ba. Domin bai san Farillai da sunnoni ba, ballantana asamu Khushu'i da Hudhuuri acikin zuciyarsa.

Ta fuskar neman ilimin addini, Mafiya yawan Iyaye basu iya kashe ma 'Ya'yansu Rabin kudaden da suke kashe musu akan karatun boko.

Ubangiji yana cewa : "BARI DAI KU KUNA ZA'BAR RAYUWAR DUNIYA NE. GASHI KUMA LAHIRA ITA CE MAFI ALKHAIRI DA KUMA WANZUWA. HAKIKA WANNAN DIN NAN LALLAI YANA NAN ACIKIN LITATTAFAN FARKO. LITATTAFAN ANNABI IBRAHEEM DA ANNABI MUSA".

Gemu ba ya hana neman Ilimi. Don haka baka yi Girma ba. Ka rika zuwa wajen Malamin Unguwarku yana koyar dakai Akhdhari da Ishmawiy Ko Iziyyah da Risalah.

Koda ba zaka sanya littafi ba, to babu laifi ka yawaita tambayoyi awajen Malamai domin neman fahimtar addininka. In dai kana son ka samu shiga Aljannah, to ba'a shigarta sai da Ilimi.

Wannan Nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (24-04-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI