TWELVE POINTS AGENDA DAGA ZAUREN FIQHU


DUK WANDA YAKE SO 'YARSA KO MATARSA, KO QANWARSA TAYI KARATUN BOKO MAI ZURFI (Higher Institutions) YA ZAMA WAJIBI YA KULA DA WADANNAN ABUBUWAN GUDA GOMA SHA-BIYU:

1.Wajibi ne ya zama tana da ilimi akan addininta tare da fahimtar abubuwan da suka haramta agareta. Gwargwadon yadda zata iya kiyaye dokokin shari'ar Allah, kuma ta kauce ma haramtattun abubuwa.

2. Wajibi ne shi karatun zamanin ya zama ya cancanta mace ta karance shi a shari'ah, Kamar misali KARATUN HARKAR LAFIYA, KARBAR HAIHUWA, ISLAMIC LAW, etc.

3. Wajibi ne ya zama tana da kwakwalwar da zata iya rike karatun: domin bai kamata ka sanyata amakarantar Alhalin kasan ba zata fahimci wannan fannin ba. Irin haka ne yake sa wasu yaran suke dadewa basu kammala ba. Saboda faduwar Jarabawa.

4. Wajibi ne ya zama akwai kudin da za'a dauki dawainiyar ta. Rashin wannan ne yake sanya wasu yaran DAUKAR NAUYIN KANSU, kuma amatsayinta na 'YA-MACE, zata iya aikata kowacce irin 'Barna domin ta samu kudin biyan Makaranta.

5. Wajibine ya zama tanada ra'ayi ko kuma asamu amincewarta cikin ruwan sanyi. Idan tafi son aure gara abarta tayi auren. Idan kuma karatun take so, to sai a za'ba mata Course din da zai fi amfanar al'ummah.

Rashin Amincewarta zai iya janyowa rashin mayar da hankalinta akan Karatun, sai kaga ta shiga harka da Qawaye, ashararun Samari, etc.

6. WAJIBI NE ALURA DA YANAYIN WURAREN DA ZA'A TURATA KARATUN: bai kamata aturata Makarantar da babu Doka da Order ba, kuma bai kamata ta zauna agidan haya ita kadai, ko tare da wasu Qawaye ba. Domin komai na iya faruwa ako yaushe.
Awasu lokutan Hostels dinma yafi security.

Awasu lokutan kuma gara ta zauna agidan wata Auntinta, in yaso tana zuwa Makarantar tana dawowa.

7. WAJIBI NE TA RIKA SANYA CIKAKKIYAR SUTURA IRINTA ADDINI: Bai kamata 'Yar Musulmai balagaggiya ta rika sanya T-SHIRT & JEANS tana zuwa makaranta ba.

8.WAJIBI NE AKULA DA SHIGE DA FICHENTA AKODA YAUSHE: asanya ido akan irin Qawayenta da take mu'amala dasu, Sannan kuma kar abarta ta Qulla abokantaka da Maza.
Koda kuwa akwai dangantakar jini. In dai ba Muharraminta bane.

9. WAJIBI NE IDAN TACE TA FASA KARATUN TO AKYALETA: Domin ba'a san abinda ta gani ba. Zata yuwu tana fuskantar Kalubale ne daga wajen Miyagun Lakcharori, ko Miyagun Qawaye 'yan madigo. (Ita kuma ba zata iya yi muku bayani ba).

10. WAJIBI NE DA ZARAR TA SAMU MIJIN AURE AYI MATA AURE, IN YASO TA QARASA KARATUN DAGA BAYA; Wani lokacin zaka ga yarinya ta isa aure, kuma ta samu Masoyi tsayayye mai kaunarta tsakani da Allah, ya turo manyansa, amma sai iyayen Yarinyar suce wai sai ta gama karatu. Irin wannan yana jefa su 'yan matan acikin garari. Wasu sun lalace, wasu kuma suna yiwa iyayensu "ALLAH YA ISA" Saboda hakin da suka afka ciki.

Ya kamata iyaye su san cewa 'Ya mace takan kamu da tsananin sha'awar Namiji tun kafin ta shekara 15 aduniya. Wasu ma tun Kafin haka. Wasu kuma sama da haka (Ya danganta da yanayin al'ummar da take rayuwa acikinsu).

11. YA ZAMA WAJIBI IYAYE SU SANYA WANI WANDA ZAI RIKA SA-IDO AKAN YARINYAR BA TARE DA SANINTA BA; da zarar yaga wani abinda bai kamata ba, sai yayi ma Iyayenta waya.

12. YA ZAMA WAJIBI IYAYE SU RIQA KAIWA 'YA'YANSU ZIYARAR BA-ZATA; Kuma in za'a je, atafi tare da mahaifiyar yarinyar ko yayarta ko Qanwarta mai wayo domin su ne zasu iya shiga har cikin 'Dakin da yarinyar take Kwana.

Duk da wannan taka tsantsan da kokarin son dacewa da shari'a din, to kuma sai ayi kokari kwarai wurin Kyautata niyyah da yin istikhara (addu'ar neman zabin Allah) kafin yin komai, Kuma ataimaka ma yara da addu'a domin addu'ar iyaye ga 'ya'yansu karbabbiya ce.

Kuma arika neman shawarwari nagari domin samun yardar Allah da cin nasara.

Wadannan shawarwarin sunzo  ne daga Zauren Fiqhu acikin rubutunmu na ranar 07-01-2015.

© ZAUREN FIQHU (07064213990 08163621213).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI