HUKUNCIN AIKIN MALAMIN TSAFTA
HUKUNCIN AIKINSA A GWAMNATI
TAMBAYA TA 1900
*********************
Assalamu alaikum ALLAH YA SAKA MA MALAM DA MAFIFICIN ALHERI AMIN.
BAYAN HAKA MAL INADA TAMBAYA KAMAR HAKA AKAN AIKI GWAMNATI A DAUKI AIKI AKAN MALAMIN TSAFTA GARINMU IN KULA DA GARINMU NE INA MAGANA AKAN SHARA MUSAMMAN MASU SANA'A TO AMMA WASU NAYI WASU BASAYI IDAN NAYI MAGANA SUCE NA MATSA MASU SHIN MALAN YAYA MATSAYIN ALBASHINA YAKE? KA HUTA LAFIYA
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko ina tayaka murnar samun aiki. Kuma ina yi maka nasiha tare da ni kaina, da jin tsoron Allah afili da boye tare da bin dokokinsa ba tare da tsoron zargin masu zargi ba.
Wannan aikin naka na Malamin Tsafta, aiki ne mai Muhimmancin gaske. Domin kuwa tsafta tana da matsayi mai girma a addinin Musulunci. Manzon Allah (saww) yace "TSAFTA TANA CIKIN IMANI".
Don haka amatsayinka na Malamin tsafta wajibi ne ka tsaya ka kula da aikin da Gwamnati ta daukeka kuma take biyanka akansa. Kar ka rika tsallake wasu kana barin wasu. Idan kayi haka zaka zama mai cin amanar aikinsa kenan.
Koda zasu zargeka da cewa ka matsa musu, sai ka rika yi musu nasihar cewa wannan garinku ne dukkanku. Idan kun gyarashi kune zaku ji dadin zamanku acikinsa. Kuma tsafta tana da Muhimmanci a rayuwar al'ummah.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (02-04-2016).
Comments
Post a Comment