DALILAN DAKE JANYO MA MUTUM AZABAR QABARI

Kwanciyar Qabari tana daga cikin manyan Jarrabobin dake jiran kowanne mutum dake raye aduniyar nan. Kowa zai fara riskar yanayin sakamakon ayyukansa ne tun daga Qabarinsa.

Kamar yadda muka bayyanar acikin Lakchochinmu da dama wadanda muka gabatar anan Zauren Fiqhu, lallai Hadisai sun tabbata daga Manzon Rahama (saww) wanda ya tabbatar da cewa Shi Qabari shine Masauki na farko daga Masaukan Lahira. Idan yayi kyau, to abinda ke gabansa ya fishi kyawu. Idan kuma yayi Muni, to abinda ke gabansa ya fishi Muni. Kuma lallai duk inda kaga Qabari, to kodai ya zamanto dausayi ne daga dausayoyin Aljannah, ko kuma Kwazazzabo ne daga Kwazazzaban azabar wutar jahannama.

Kuma lallai babu bambanci cikin adadin dadewar da bayin Allah zasuyi acikin Qabarinsu. Da wanda ya mutu tun azamanin farko, da wanda ya mutum awannan zamanin da muke ciki, duk babu bambanci.

Hakanan babu bambanci tsakanin wanda ya mutu aka binneshi, da wanda ya mutu acikin ruwa gawarsa ta ru'be, da wanda wuta ta cinye namansa, da wanda kura ko zaki suka cinyeshi. Kowa sai Mala'ikun nan guda biyu (MUNKARUN WA NAKEER) Sunje masa. Kuma kowa sai ya riski dandanon sakamakon aikinsa.

SHIN WADANNE ABUBUWA NE SUKE JANYO MA MUTUM AZABAR QABARI?

Abubuwan dake janyo ma mutum azabar nan ta Qabari suna da yawa. To amma akwai wasu daga ciki sunzo acikin ingantattun hadisai daga Sayyiduna Rasulullahi (saww).

Akwai hadisin da Imamul Bukhariy da Imamu Muslim suka ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) cewa watarana Manzon Allah (saww) ya wuce ta kusa da wasu Qaburbura guda biyu, sai yace:

"HAKIKA SU WADANNAN (NA CIKIN QABURBURAN) ANA AZABTAR DASU NE. KUMA BA WAI AKAN WANI BABBAN ABU AKE YI MUSU AZABA BA (SU AGANINSU).

- AMMA 'DAGA DAGA CIKINSU, SHI YA KASANCE BA YA TSARKAKE KANSA DAGA FITSARI NE.

- 'DAYAN KUMA YA KASANCE YANA YAWON GULMA NE (WATO ANNAMIMANCI).

Sannan sai Annabi (saww) ya dauki Tankar dabino (wato ganyen) ya tsagashi biyu, sannan ya kafa guda akan wannan Qabarin, guda kuma akan 'daya Qabarin.

Sai Sahabbai suka ce "Mai yasa ka aikata haka Ya Rasulallah?". Sai yace "WATAKIL SU ZA'A SAUKAKA MUSU AZABAR MUTUKAR DAI BAI BUSHE BA".

An ruwaito wannan hadisin daga Manzon Allah (saww) ta hanyoyi masu yawa. Misali akwai ruwayar Ibnu Maajah daga Sayyiduna Abu Bakrata (ra) wanda acikinsa Manzon Allah (saww) yace "AMMA 'DAYAN CIKINSU, ANA YI MASA AZABA NE SABODA GHEEBAH (WATO CIN NAMAN MUTANE)".

Acikin ruwayar Khalal daga Sayyiduna Abu Hurairah kuma, yace "AMMA DAYAN CIKINSU, TO YA KASANCE YANA GULMAR MUTANE NE DA HARSHENSA SANNAN YANA YAWO DA ANNAMIMANCI ATSAKANINSU".

Akwai kuma ruwayar Tabaraniy daga Nana A'ishah (ra) da Anas bn Malik da Abdullahi bn Umar (ra). Sannan akwai ruwayar Abu Ya'ala daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra).

Amma acikin ruwayar  Athram daga Abu Umamah Al-Bahiliy (ra) Sahabbai sun tambayi Manzon Allah (saww) cewa "Ya Rasulallahi har zuwa yaushe za'a ci gaba da yin azaba agaresu?" .

Sai yace "WANNAN GHAIBU NE. BABU WANDA YA SANI SAI ALLAH. AMMA BA DON GUDANUWAR ZUCIYARKU DA KUMA YAWAN ZANTUKANKU BA, DA KUNJI ABINDA NAKE JI".

Imamun Nisa'iy ya ruwaito wani hadisi daga Nana A'isha (ra) tace "Wata Mata Bayahudiya ta shigo wajenmu sai tace "Azabar Qabari ana yinta ne saboda Fitsari".

Sai nace mata "Qarya kikeyi". Sai tace "Ai shi (fitsari) ana kankareshi ne daga fatar jiki da kuma tufafi".

"Sai Manzon Allah (saww) ya fito zuwa sallarsa alhali muryoyinmu sunyi sama!. Sai yace "MENENE HAKA?" Sai na bashi labarin abinda ta fa'da, sai yace "TAYI GASKIYA".

To kunga duk wadannan hadisan sun Tabbatar mana da abu guda ne. Wato lallai ana yiwa mutum azaba a Qabarinsa ta dalilin rashin yin cikakken tsarkin fitsari da kuma gulma, sannan Annamimanci. (Allah ya tsaremu).

Imamu Ahmad da Abu Dawud da Nisa'iy da Ibnu Maajah sun fitar da hadisi daga Sayyiduna Abdurrahman bn 'Auf (ra) cewa yaji Manzon Allah (saww) yana cewa "SHIN BAKU SAN ABINDA YA SAMU MUTUMIN NAN NA BANU ISRA'EEL BANE?.

SUN KASANCE IDAN FITSARI YA TA'BA JIKINSU, SUNA YANKEWA WAJEN DA YA TA'BA DIN NE. SAI SHI (WANNAN MUTUMIN) YA HANASU YIN HAKA. DON HAKA AKE YI MASA AZABA ACIKIN QABARINSA".

Acikin wani hadisin ma wanda Imamu Ahmad da Ibnu Maajah suka ruwaito daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa "MAFI YAWAN AZABAR QABARI ANA YINTA NE SABODA FITSARI".

Anan nake so in ja hankalin 'Yan uwa Matasa. Musamman wadanda suke ganin kamar kansu ya waye. Basu damu da yin tsarki da ruwa sosai yayin fitsarinsu ba.

Wasu ma atsaye suke yin fitsarin. Kuma basu bari su kammala sosai. Daga sun mike tsaye sai sauran fitsarin ya zubo acikin wandonsu. Wannan ba Qaramin bala'i bane suke janyo ma kansu. Domin tabbas ibadarsu bata yiwuwa yadda Allah yake so.

Hakanan masu aikin Khaki, suma akwai mafiya yawansu idan sun fita daji basu damu da yin tsarkin fitsari da ruwa ba.. Ya kamata agyara.

Sannan masu yawon baza jita-jita atsakanin Mutane, da masu rubutun gulmace-Gulmace a Social Media duk idan basu tuba ba, zasu afka cikin Azabar Qabari. (Allah shi kiyayemu).

Zauren Fiqhu jan kunne shine namu. Wanda ya karanta ya kiyaye to yayi ma kansa. Hakanan wanda ya karanta ya wuce bai chuchemu da komai ba. GYARA KAYANKA....

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (18-04-2016).

Comments

  1. Na yi imani da wanda ya mallaki 100% na zuciyarka ya cancanci yaƙin. Haka ne, ina alfahari saboda ban taɓa bin shawara mai kyau daga iyayena ba lokacin da nake son yin aure. Akwai yakin tsakanin iyalinmu biyu sannan mijina ya kasance jaririn uwarsa, 'yan uwansa sunyi amfani da shi da yawa wanda ya yanke hukunci ba tare da tuntube su ba. Abinda ya mamaye ni shine lokacin da dan shekaru 36 ya nemi iyayensa da wasu dangi su yarda kafin su gana da kowa da kowa, mafi munin abin da ya faru lokacin da aka umurce shi ya kawo ni zuwa ƙasarsu a Rampart, New Orleans, yana da haɗari don karɓar wannan gayyatar.Gamar tsakanin iyalanmu ya fara lokacin da ya karshe (wannan kimanin shekaru 4 da suka wuce), iyalinsa sun ba da wasu ka'idoji idan yana da matata (muna zama tare da su), na yi fushi lokacin da miji yarda da farin ciki da yanayin su (don haka mahaukaci). Iyalanmu sun yi tawaye kuma sun bukaci ya kamata in rabu da shi nan da nan.Na yanke shawarar ba shi harbin karshe kamar mutum wanda ya riga ya dauki 100% na zuciyata, na dauki haɗari na tafiya ta ruhaniya tare da su ta hanyar tuntuɓar Doctor Sharaja ta sharajasid @ Gmail.com, Ban sani ba amma mahaifin ruhaniya ya rigaya ya san zan shawarce shi. Da farko dai ya gaya mani hatsarin da nake ciki da kuma yadda miji ya zama bautar tun lokacin da aka haife ni, yadda suke ci gaba da kwakwalwa ta wanke shi don yin abin da suke so. Kamar yadda abin da mutum yake gani a hankali kawai, na gane cewa babu wanda ya ga abin da na gani a cikin mijina kuma wancan ne dalilin da ya sa na yi amfani da taimako na SHARAJA SHIRYA don cire shi daga cikin wahala. Idanunsa inda aka bude ta SHARAJA SID a karo na farko, iyalinsa sun ƙaunace ni kuma sun ba da duk bukatunmu, iyalanmu sun san zaman lafiya tun bayan ƙaunar da aka yi. Yana da shekaru 2 bayan ƙauna da mijina ya ci gaba da inganta kowace rana ba tare da tsangwama daga iyalinsa ba. Na jira tsayi sosai don raba wannan yanki mai ban mamaki. Na gode da lokacinka da kuma SHARAJA SID. Na san shi ta hanyar karatun wasu shaidun ban mamaki game da blogs .. rubutu firist sharajasid ++ (234) 9066-376197

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI