HASKEN ZIKIRIN ALLAH

HASKEN ZIKIRIN ALLAH (SWT)
******************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Hakika dukkan Malamai Masanan Allah sun tabbatar da cewa babu wani abu guda daya wanda yake bude Zuciyar 'dan Adam fiye da Zikirin Allah.

Kuma babu aiki mafi sauki kuma mai kawowa mutum lada masu yawa acikin Qankanin lokaci kamar Zikirin Allah.

Kuma babu aiki mafi daraja awajen Allah fiye da Zikiri. Shi yasa ma Madaukakin Sarkin yace : "KU AMBACENI NIMA ZAN AMBACEKU".

Kuma yace "KU AMBACI ALLAH, AMBATO MAI YAWA, KUMA KU TSARKAKE SUNANSA (TASBEEHI) SAFIYA DA MARAICE".

Kuma babu wata katanga mafi Qarfi wacce take tsare mutum sannan ta kubutar dashi daga Sharri da makircin Shaitan fiye da Zikirin Allah.

Hakika shi Zikirin Allah, wata Aljannah ce adoron Qasa wacce duk wanda bai shiga cikinta anan duniya ba, to ba zai shiga waccen Aljannar ta lahira ba.

Zikirin Allah shi kadai ne yake ceton zukata daga 'dimuwa da tsoro da firgici, Kuma shine hanya mafi sauki domin samun isuwa zuwa ga kowanne babban rabo da dacewa.

Leka cikin Alqur'ani mai girma kaga manyan manyan Fa'idodinsa. Idan kayi nazari za kaga cewa shine babban Sabulun dake wanke ma Zukata dattin Tsoro da bakin ciki da damuwa, Kuma shi ke samar da rayuwa ga zukata.

Idan kayi nazari dole kayi mamakin yadda Gafalallu suke rayuwa ba tare da ambatonsa ba. "SU MATATTU NE BA RAYAYYU BA, KUMA BA ZASU SAN YAUSHE NE ZA'A TASHESU BA".

Gwargwadon yadda ka nitse cikin ambatonsa, gwargwadon haka hasken zuciyarka yake Qaruwa, tunaninka yak

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI