SAYYIDUNA ABUBAKRIN (RTA) -3
KHALIFAN MANZON ALLAH (saww)
Azamanin Khalifancinsa, bayan wafatin Manzon Allah (saww) Farkon annobar data fara kunnowa kai ita ce: RIDDA da yawancin larabawan Qauyuka suka rika yi.
Mafiya yawansu daga jin cewar Manzon Allah (saww) yayi wafati shikenan sai sukayi ridda suka fice daga Musuluncin.
Wasu kuma basu bayyana cewar sun fita daga Musuluncin ba, sai dai sun Qi bayar da zakkah.
Wasu kuma bayan riddar ma, har sun fara da'awar Annabta. Irinsu Musaylamah Alkazzab.
Har sai da ya zama iya garuruwa 3 ne kadai ake yin Musulunci aduniya. Wato Makkah, Madeenah, da Ta'if.
Amma matakin farko da ya fara yi shine zartar da abubuwan da Manzon Allah (saww) ya riga ya fara su. Misali kamar tashin rundumar Usamah bn Zaid bn Harithah zuwa yakin Rum.
Da yawa daga cikin Sahabbai sunyi niyyar hanashi tura wannan rundunar. Saboda ganin halin da ake ciki.
Yayin da Sayyiduna Umar (ra) ya tareshi ya gaya masa cewar bai kamata atura wannan rundunar ba.
Sai ya bada amsa cewar:
"Wallahi ni bazan kunce duk wani abinda Manzon Allah (saww) ya Qulla ba. Koda tsuntsaye da Zakokin gefen Madina zasu rika kawo mana hari suna cinyemu daya bayan daya"
Ya Qara da cewar: "Wallahi koda zakoki zasu cinye Ummuhatul Mu'umineena, wallahi sai na tashi rundunar Usamah"
Da sauran Manyan Sahabbai suka ga babu makawa awajen Sayyiduna Abubakrin, sai suka sake bashi wata shawarar. Suka ce masa: "to me zai hana ka chanza Komandan rundunar? Ka cire Usamah ka sanya wani wanda yafi shi yawan shekaru?" (Saboda shi Usama yaro ne matashi asannan)
Daga jin wannan shawarar tasu sai ransa ya baci. Yake ce musu: "Ta yaya za'a chanza hukuncin da Manzon Allah (saww) ya riga ya zartar?"
Saboda haka ya tura wannan rundunar Qarkashin jagorancin Sayyiduna Usamatu bn Zaid. Suka fita suka tafi suka yaki rundunar Rumawa. Suka samo gagarumar nasara. Suka zauna Kwana 70 ko 40 awata ruwayar. Sannan suka dawo gida.
Wannan fitar tasu da dawowarsu ya tsorata Larabawan Qauyuka wadanda sukayi ridda.
Don haka da dawowarsu sai Sayyiduna Abubakrin (Khalifan Manzon Allah saww) ya tura su yaki da 'yan ridda da kuma masu hana zakkah.
Nan zan tsaya. Amma insha Allah in an jima ko kuma gobe zan ci gaba daga nan.
Da fatan Allah ya Qara tsira da aminci abisa Fiyayyen Manzanni (saww) tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbai da magoya bayansa.
ZAUREN FIQHU (2014).
Comments
Post a Comment