Posts

ƊAUƘAR CIKIN MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA HAIHUWARSA.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salati Matabbaci da aminci wanzajje su tabbata ga Mafi tsarkin dukkan bayi, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa. Acikin wancan darasin namu na farko, wanda muja gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) munji Tarihin iyaye da kakannin Manzon Allah (saww) da yadda tsarkin nasabarsa take. Acikin wannan darasin kuma, in sha Allahu zamu ji abubuwan da suka faru tun daga daukar cikinsa har zuwa haihuwarsa (saww) da kuma abubuwan da mahaifiyarsa mai daraja ta gani na ayoyin Ubangiji da kuma girmamawa. Babban Malamin tarihin nan mai suna Ibnu Sa'ad (rah) ya ruwaito wani hadisi daga 'Yar uwar mahaifin Yazeed bn Abdillahi bn Wahab bn Zam'ah, tana cewa: "Lokacin da mahaifiyar Manzon Allah (saww) (Wato Aaminatu bintu Wahbin) ta dauki cikinsa, ta kasance tana cewa: "Ban san cewa ni ina dauke dashi ba. Kuma ban ji irin nauye-nauyen nan da Mata suke ji ba. Sai dai kawai ni ban ga al'adata ba. Kuma dama ta kas...

MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 12

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata ga Annabinmu tare da iylan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyan bayansu da kyutatawa. Wannan shine ci gaban darasinmu na Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke kawo muhimman lamura acikin tarihin Ma'aikinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). ZAMANSA A KOGON HIRA'U ***************************** Annabi (saww) ya kasance akowacce shekara yakan kebance kansa tsawon wata guda ya tafi kogon hira'u wanda ke kan Jabalun Nur ya zauna yana tunani cikin lamarin Ubangijinsa kuma yana ibadah (bautar Allah) bisa addinin Kakansa Annabi Ibrahim (alaihis salam). Wannan tun kafin ya cika shekaru arba'in aduniya kenan. Amma bayan ya cika 'dan shekara arba'in aduniya watarana yana zaune acikin kogon sai ya hangi siffar wata Halitta mai girman gaske ta cika dukkan sasanni. Ashe Shugaban Mala'iku ne wato Jibreelu (amincin Allah ya tabbata gareshi). Yazo ya rungumeshi zuwa jikinsa runguma mai tsanani sannan y...

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA

Da Sunan Allah Buwayi gagara-misali, Mai kula da lamarin bayinsa. Wanda gyangyadi bai ta'ba daukarsa ba, ballantana barci. Babu abinda ke buya gareshi daga ayyukan bayinsa acikin sarari ko duhun dare. Salati da aminci su tabbata ga Annabin da Allah ya aikoshi zuwa ga dukkan halittu amatsayin rahama garesu tare da gargadi da bushara, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mutanen kirki. Wannan ita ce fitowa ta goma sha bakwai acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke bayani dalla-dalla game da wasu al'amuran tashin alqiyamah wacce lamarinta ke kwankwasar zukata. Babban abinda ya kamata mao karatu yayi, shine ya rika kwatanta faruwar abun a zuciyarsa domin hakika ranar nan tana tafe, kuma zata afku ne babu zato balle tsammani. Hakika idan alqiyamah ta tsaya, awannan ranar akwai masifar zafi da Qunar rana saboda kusanto da ita da za'a yi. Mutane da Aljanu gaba dayansu zasu rika zubda gumi (wato zufa) wanda sai damshinsa ya kai zurfin zira'i saba'in a Qa...

ZUWA GA 'YAN UWA MATA

Aure shine mafi girman al'amari arayuwar 'Ya mace. Ta hanyarsa ne zata samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta samu damar kafa nata iyalin. Idan aure yayi jinkiri agareki, kar kiyi amfani da wannan damar wajen biyan bukatar sha'awarki ta hanyoyin da Ubangijinki ya haramta.. A'a kiyi hakuri ki kama kanki. Ki dage wajen ibadah da neman yardar Ubangijinki. Ki kyautata zato ga Ubangijinki. Shi mabuwayi ne mai hikima. Kuma duk abinda ya Qaddara miki, to kiyi fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi sannan ki nemi mafita awajensa, ba wajen bokaye da 'yan bori da 'Yan duba ba.. Zina da Ma'digo da kallon hotunan batsa, da yin chatting na batsa duk Kofofin samun tsinuwa ne da kuma fushin Ubangijinki.. Ki kyautata ma kanki kiji tsoron Ubangijin da ya halicceki kar ki kai kanki ga Hallaka. Ki kiyayi hulda da mayaudaran samari wadanda ke kanki kin san ba aure ne yake kawosu wajenki ba. Mafiya yawansu zasu bata miki lokaci ne kawai. Idan kuma lokac...

WASIYYAR LUQMAN ALHAKEEM (01)

Luqman (Allah shi Qara masa yarda) wani Salihin bawa ne baqar fata wanda Allah yayi masa arzikin harshe mai fasaha da hikimomi tare da samun hanyoyin warware mishkilolin al'ummah. Koda acikin Alqur'ani akwai surah guda wacce Allah ya kawo labarin Luqman da irin hikimominsa, har ma ana kiran surar da "SURATU LUQMAN". To yanzu in sha Allah zamu kawo wasu daga cikin irin hikimominsa kamar yadda suka zo a litattafan manyan Maluman Musulunci domin mu amfana da alkhairin dake cikinsu. Watarana Luqman yace ma 'dansa "Ya Kai 'dana! Kada ka aiki Jahili anatsayin 'dan aikenka. Idan har baka samu mai hikima wanda zaka aika ba, to gara ka zamanto 'dan aiken kanka. Ya kai 'Dana! ka nisanci yin Qarya. Domin hakika ita Qarya tana da zaqi abakin mutane kamar yadda naman tsuntsu yake, amma sai dai Ma'abocinta bai cika samun tsira daga gubarta ba. Ya kai 'dana! Ka rika ziyartar wajen Janazah, amma kada ka yawaita ziyartar wajen bukunkuna. Domin kuw...

MU SAN ANNABINMU (05)

RASUWAR MAHAIFIYARSA MAI GIRMA (SAWW) : Bayan Mala'ikun nan sun kwantar dashi sun tsaga kirjinsa, sai Halimatus Sa'adiyyah ta dawo dashi wajen mahaifiyarsa saboda jin tsoron da takeyi bisa lafiyarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Bayan dawowarsa wajen Mahaifiyarsa da shekaru biyu wato lokacin yana da shekara shida kenan aduniya, sai tayi nufin ta ziyarci garin Yathrib (Madeenah) wajen kawunnanta Banun Najjar, da kuma Qabarin mijinta Abdullahi. Ta tafi tare da Manzon Allah (saww) tayi wadannan ziyarori, amma akan hanyarta ta dawowa sai jinyar ajali ta kamata, kuma ta rasu adaidai wani waje da ake kira "ABWA'U" kuma anan aka binneta, Qabarinta yana nan har yanzun nan. Shikenan Manzon Allah (saww) ya zamanto cikakken maraya ta bangaren mahaifansa baki daya. To alokacin nan akwai baiwar mahaifinsa wacce ake kiranta "Ummu Aymana - Barakatul Habashiyyah" ita ta kamo hannunsa suka dawo garin Makkah,  kuma shekarunsa shida awannan lokacin. ALLAHU...

MU SAN ANNABINMU (06)

KOMAWARSA HANNUN KAKANSA MAI DARAJA (SAWW)  : Daga nan sai ya koma hannun Kakansa wato mahaifin mahaifinsa, mai suna Abdul Muttalibi 'dan Hashim. Ya kasance mai nuna so da Qauna ga wannan jikan nasa mai daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Ya kasance duk inda zai je tare suke tafiya, ba ya yin barci sai tare dashi, hakanan wajen cin abinci ma. Kuma yasoshi fiye da sauran jikanunsa da 'ya'yansa. Ya kasance yana girmama Annabi (saww) kuma yana gaya ma mutane cewa "Akwai wani babban lamari da zai faru ga jikan nan nawa". Sai dai zamansu bai tsawaita ba, domin bayan shekaru biyu kachal sai shima ya rasu,  Kuma yabar wasiyyah ga 'daya daga cikin 'ya'yansa mai suna "Abu Talib" cewa shi zai ci gaba da kulawa da wannan jikan nasa, Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Salati da amincin Allah si tabbata bisa Annabin Rahma Ma'abocin tausayi da karamci, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da mabiyansa ...