Posts

MU SAN ANNABINMU (26)

Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Acikin wannan darasin na Zauren Fiqhu zamu dora daga inda muka tsaya acikin tarihin Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). YAQIN HAMRA'UL ASAD : Washegarin dawowa daga yaqin uhudu sai Manzon Allah (saww) yayi tunanin watakil mushrikan Quraishawa su sake kawo hari garin madeenah don haka yayi nufin fita domin sake tararsu a sake wani sabon gumurzu don a nuna musu cewa har yanzu fa musulunci yana nan da Qarfinsa. Ashe kuwa shi Abu Sufyan shugaban dakarun Quraishawa ya daura niyyar dawowa din don Qara kawowa hari akan Musulmai, akan hanyarsa sai ya hadu da wani mutum mai suna Ma'abadu 'dan Ubayyu Alkhuza'iy. Sai Abu Sufyan din ya tambayeshi "Meye labarin abinda ke bayanka?". Sai yace masa "Ya kai Abu Sufyan, yi sauri ka guje daga garesu domin hakika sun tanadi makama...

LABARIN CIKIN QABARI

Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Hammadu bn Salamah, shi kuma ya karbo daga Hisham bn 'Urwah, shi kuma daga Babansa yana cewa : "Watarana wani mahayin doki yana tafiya atsakanin garin Makkah da Madeenah sai gashi kusa da wata Maqabarta,  sai yaga wani mutum ya fito daga cikin Qabarinsa yana ci da Wuta!!. Ga kuma Qarafuna an daddaureshi dasu. Sai yace "Ya kai bawan Allah! Hure min wutar nan! Hure min wutar nan!". Nan take sai ga wani ya sake fitowa ta cikin wannan Qabarin, yabi wancan din yana cewa "Ya kai bawan Allah kada ka bushe masa (wutar nan)!" Nan take shi wannan mahayin dokin ya suma akan dokin nasa. Kuma dokin yaci gaba da tafiya dashi ahaka har sai da ya kaishi wajen wata rijiya. Yayin da ya farka sai yaga duk gashin dake kansa ya juye ya zama furfura fari fat tamkar auduga! Yaje ya bama Sayyiduna Uthman bn Affan (ra) labarin abinda ya faru (Zamanin Khalifancinsa ne). Sai shi Sayyiduna Uthman din ya hana mutum ya rika yin tafiya shi ka...

MU SAN ANNABINMU (25)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa shiryayyu. YAQIN BANU QAINUQA'A : Banu Qainuqa'a sunan wata Qabila ne daga cikin Qabilun yahudawan madeenah wadanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya qulla alkawarin zan lafiya dasu tun farkon zuwansa garin. Nasarar da Manzon Allah (saww) ya samu a yaqin badar ta basu haushi, don haka sai suka fito fili suna bayyana qiyayyarsu ga Musulmai da kuma soyayyarsu ga mushrikan Quraishawa. Kuma sun kasance suna gadara da Qarfin tattalin arziki kasancewarsu masu sana'ar zinare ne. Suna cin mutuncin jama'ar musulmai, suna yi musu izgili har dai watarana suka yiwa wata mace musulma tsirara a kasuwarsu, ta nemi taimako awajen wani musulmi ya taimaka mata ya kashe bayahuden da ya zalunceta. Sai sauran yahudawan suka taru akansa (shi Musulmin) suka kasheshi. Wannan shine tushen yaqin. Kuma Manzon Allah (sa...

RANAR RABON TAKARDU!!!

Ranar da za'ayi rabon takardu, rana ce wacce hankula ke tashi.. Idanuwa suna kuka amma babu zubar hawaye...! Mutane zasu kasance kaso uku ne awannan lokacin : # Akwai wadanda ba za'a basu littafi ba. Wato ba za'a yi musu hisabi ba. Kamar Annabawa kenan (as) da manyan Salihan bayin Allah da Siddiqai da Shahidai. # Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun dama. Sune wadanda za'ayi musu hisabi sassauka. Wato ba za'a duba laifukansu ba. Farkon wanda zai karbi Littafinsa da hannun dama shine Sayyiduna Umar bn Khattab (rta). Kamar yadda hadisi ya fada. # Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun haggu. Acikin wata ayar ma Allah yace zasu karba ne ta baya. Wato Mala'iku zasu sanya hannunsu na hagu su fasa musu Qirjinsu dashi, sannan su zaroshi ta baya, Sannan a miko musu littafin nasu. Za'a ce ma kowanne daga cikinsu " KARANTA LITTAFINKA DA KANKA .... " A sannan ne Dan Adam zai tuno da dukkan abinda ya aikata a rayuwarsa ta duniya.. Wat...

LABARIN DAMO YANKAKKE

DAGA ZAUREN FIQHU : Wani Balaraben Qauye ya farauto Damo (alligator) ya shigo gari sai yaga Manzon Allah (saww) tare da wasu Jama'a yana yi musu wa'azi. Da yaga haka sai ya tambayi mutane "Wannan mutumin fa? wanene?". Sai akace masa "AI ANNABI NE". Saboda haka sai Balaraben Qauyen nan ya rika keta tsakanin jama'a, har sai da yazo ya tsaya agaban Manzon Allah (saww). Sannan yace: "Na rantse da lata da uzza (sunayen gumakansa ne) babu mutumin da na tsaneshi fiye da kai, Ba don kar mutanena su washeni ba, da sai na kasheka". Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) zai zare takobi ya kasheshi sai Manzon Allah (saww) ya hanashi. Balaraben Qauyen nan ya fito da damonsa (yankakke) daga cikin jakarsa, ya jefar agaban Manzon Allah (saww) sannan yace: "Na rantse da lata da uzza ba zan bada gaskiya gareka ba, har sai wannan yankakken damon yayi Imani dakai". Sai Manzon Allah (saww) yace "YA KAI DAMO!!". Sai Damon ya amsa acikin harshe...

MAGANIN TSAGEWAR FATAR TAFIN HANNU DA SAURAN CIWUKAN DAJI :

TAMBAYA TA 2621 ******************* Assalamu Alaikum, Malam barka da rana ya iyali? Allah saka maku da aljanar firdaus akan taimakon dakukeyi amin. Malam yarona ne  yake  fama da kuraje a tafukan hannun shi   kurajan suna fitowane kamar bororon Wuta, wani lokaci kuma sai sufito kanana ko kuma haka kawai sai hannuwan su rinka tsagewa kamar ya yanke kuma suna Mashi kaikai Dan wani lokaci kaikain yakan hanashi bacci sosai idan kuma ya Sosa sai su rinka fitar da jini.Malam dan  Allah ataimaka mana, daga  dalibarku. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullah. Irin wadannan chutukan fata ne kuma basu rasa alaqah da ciwon daji irin na fata. Amma ga wasu abubuwa nan ki jarrabah. 1. Ki samu lalle (irin wanda kuke yin Qunshi dashi) ki kwaba da ruwa amma ki sanya man zaitun kamar cokali guda aciki. Sai kiyi masa Qunshi a hannayen nasa. Lalle yana maganin mafiya yawan ciwukan fata. Kici gaba da yi masa Qunshin duk bayan sati biyu. In shaAllah cikin Qankanin l...

MADUBIN DUBAWA (70)

Yau madubin namu zai waiga baya ne ya dauko mana wani abu daga rayuwar magabatanmu wato tabi'ai da tabi'ut tabi'un. Daga cikin magabata akwai wadanda tsoron wutar lahira da kuma tunaninta yasa suka haramta wa kansu yin dariya anan gidan duniya. Isma'eel As-Suddiy (rah) yace "Lokacin da Hajjaju bn Yusuf (wani azzalumin gwamna ne) yasa aka kamo masa babban Malamin tabi'ai din nan mai suna Sa'eed bn Jubair kafin ya kasheshi sai ya tambayeshi cewa "Labari ya sameni cewa wai kai baka ta'ba yin dariya ba tunda kake!". Sai Sa'eed bn Jubair (rah) yace masa "Ta yaya zan rika dariya alhali an riga an hura jahannama, Kuma Qukuman cikinta an riga an kakkafasu, Kuma Zabaniyawan cikinta an riga an tanadesu ? (Qukumi shine irin chain din da ake Qakaba musu a wuyansu lokacin da ake jibgarsu ana azabtar dasu. Zabaniyawa kuma sunan Mala'ikun nan ne Qarfafa guda goma sha tara wadanda Allah ya tanadar dasu domin azabtar da 'yan wuta). Bayan H...